An samu kusan juyin mulki 130 da suka yi nasara, a cikin ƙasashen Afrika 36, tun 1952 lokacin da Sarki Farouk na Masar ya zama shugaban wata ƙasa a Afirka na farko da aka hamɓarar.
Afirka ta fuskanci juyin mulki takwas da suka yi nasara cikin shekara uku da suka gabata. Yayin juyin mulki na baya-bayan nan da aka fuskanta na zuwa ne bayan da sojoji suka farfaɗo bayan shafe kusan shekara 20 rabonsu da yayin juyin mulkin, bayan yayinsa da suka yi a shekarun 1970.
Wasu jagororin da suka ƙwace iko, sun yi mulki na gomman shekaru, yayin da wasu kuma aka tumɓuke su cikin kwanaki bayan kwace mulkin.
Alal misali Shugaban ƙasar Equatorial Guinea, Obiang Nguema ya shafe shekara 44 yana mulki bayan ƙwace iko a shekarar 1979.
A yanzu shi ne shugaban ƙasa a Afirka da yafi jimawa a kan mulki.
Alal misali Shugaban ƙasar Equatorial Guinea, Obiang Nguema ya shafe shekara 44 yana mulki bayan ƙwace iko a shekarar 1979.
A yanzu shi ne shugaban ƙasa a Afirka da yafi jimawa a kan mulki.
Mafi yawan ƙasashen yankin Sahel sun fuskanci juyin mulkin soji. Juyin mulki na baya-bayan nan a yankin shi ne wanda aka yi a Jamhuriyar Nijar da Gabon a 2023
Shugabannin soji sun kuma ƙwace mulki a Mali a 2020 da 2021 da Chadi da Guinea da Sudan a 2021. Burkina Faso ta fuskanci juyin mulki har sau biyu a 2022, Duka waɗannan ƙasashe rainon Faransa ne, in ban da Sudan.
Tun 2000, kashi uku cikin huɗu na juyin mulkin da suka samu nasara a Afirka sun auku ne a ƙasashe rainon Faransa. Hakan ya sa wasu ke aza ayar tambaya cewa ko tasirin Faransa a Afirka ne ke haddasa hakan.
Yawan juyin mulki
0
2
4
6
8
Mafi yawan ƙasashen Yammacin Afirka da na Tsakiya sun fuskanci yawan juyin mulkin da ya yi nasara. Kusan rabin ƙasashen yankin 17 sun fuskanci aƙalla juyin mulki huɗu a Yammacin Afirka
Burkina Faso ce ta fi kowace ƙasa yawan juyin mulki a Afirka inda ta fuskanci takwas, daga nan sai Saliyo da Uganda masu bakwai kowannensu.
Kashi ɗaya cikin uku na ƙasashen Afirka, mafi yawancinsu daga Gabashi da Kudanci Afirka ne ba su taɓa fuskantar juyin mulkin da ya yi nasara ba
Mai shekara 34, a 2024, Ibrahim Traore ya kasance shugaban ƙasa mafi ƙanƙantar shekaru a duniya. Ya zama shugaban riƙon ƙwarya na Burkina Faso bayan da sojoji suka yi juyin mulki ranar 30 ga watan Satumban 2022, inda suka kifar da gwamnatin riƙon ƙwarya ta Paul-Henry Sandaogo Damiba.
Kusan kashi 90 na juyin mulkin da suka yi nasara a Afirka, sojoji ne suka yi, daga nan sai sojojin haya masu kashi huɗu. Sauran nau'ikan juyin mulki da ka yi a Afirka sun ha ɗa da boren fararen hula, mulkin mallaka, dakarun tawaye da juyin mulkin masarauta.
Mafi yawan shugabannin da suka karɓi mulki da ƙarfi, daga baya wasu ne ke hamɓarar da su, a wasu lokuta ma a kashe su
A 1972 Janar Ignatius Kutu Acheampong ya jagoranci juyin mulki da babu zubar da jini, wajen tumbuƙe zaɓaɓɓiyar gwamnatin Firaministan Ghana Dakta Kofi Busia. Shekara shida bayan haka aka tuɓuke shi a wani juyin mulkin masarauta sannan kuma aka kashe shi shekara guda bayan haka.
Thomas Sankara ya zama shugaban Burkina Faso a 1983, bayan wani juyin mulki da sojoji suka yi a madadinsa, a lokacin da yake ƙarƙashin ɗaurin talala. A ranar 15 ga watan Oktoban 1987 wata ƙungiyar masu ɗauke da makamai suka kashe Sankara a lokacin wani juyin mulki da Blaise Compaore ya jagoranta.
Gaafar Nimeiry ya tunɓuke shugaban Sudan Ismail al-Azhari a 1969, sannan ya karɓe iko, da farko a matsayin shugaban mulkin soji, sannan ya zama shugaban ƙasa, kafin a kifar da gwamnatinsa a 1985.
Jean-Baptiste Bagaza ya tumɓuke shugaban ƙasar Burundi Michel Micombero a 1976 sannan ya karɓe mulki. shekara 11 bayan hakan ne kuma aka hamɓarar da shi, lamarin da tilasta masa gudun hijira.
Omar al-Bashir ya zama shugaban ƙasar Sudan a 1989 a lokacin da yake muƙamin Burgediya Janar a rundunar sojin ƙasar, ya jagoranci sojoji wajen kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatim ƙasar. Daga nan ya ci gaba da zama shugaban Sudan har zuwa 2019 lokacin da wani juyin mulkin soji ya kifar da gwamnatinsa.
François Bozizé Yangouvonda ya ƙwace mulki a 2003. Inda ya zama shugaban ƙasar Jamhuriyar Tsakiyar Afirka. Shekara 10 bayan haka aka hamɓarar da shi.
Barinsa a cikin dangi
Ƙwace mulki al'ada ce ta dangi a wasu ƙasashen. Alal Misali a Equatorila Guinea, Teodoro Obiang Nguema Mbasogo - wanda ɗan ɗan'uwan shugaban ƙasar Francisco Macias Nguema - ne ya yi masa juyin muyin mulki a 1979. Zuwa shekarar 2024 Teodoro ne shugaban ƙasa - wanda ba na sarauta ba - na biyu mafi jimawa a karagar mulki.
Laurent Kabila ya hamɓarar da Shugaba Mobutu Sese Seko a 1997, sannan ya zama shugaban DR Kongo na uku. Daga baya kuma ɗansa mai shekara 29, Joseph Kabila ya gaje shi bayan da ɗaya daga cikin masu kare lafiyarsa ya kashe shi.
Bincike: Ruth Mulandi; Text and data analysis Dorothy Otieno; Design: Millicent Wachira; Development: David Ayoola and Boaz Ochieng; Editing: Damilola Ojetunde and Dorothy Otieno. Additional support: Olaniyi Adebimpe, George Wafula, Mayowa Alabi, Brian Otieno, Ashley Lime and Esther Ogola.
Getty Images da shafukan intanet na gwamnatocin Afirka