
Shirin Mata 100 na BBC na 2022: Su waye a cikin jerin sunayen?

BBC ta fitar da jerin sunayen mata 100 da suka kasance fitattu da masu bai wa mutane ƙwarin gwiwa daga fadin duniya a 2022.
Daga cikin su akwai mawaƙiya Billie Elilish da matar shugaban Ukraine Olena Zelenska da ƴar fim ɗin Indiya Priyanka Chopra Jonas da Selma Blair da wata mawakiyar pop ta Rasha ta 'tsarina of Russian pop' Alla Pugacheva da mai wasan hawa tsaunuka ta Iran Elnaz Rekabi, ƴar tseren da ta kafa tarihi Yulimar Rojas da mawallafiyar littafi ƴar Ghana Nana Darkoa Sekyiamah.
Wannan ne karo na goma na Shirin Mata 100, kuma za mu yi amfani da wannan damar wajen fayyace irin ci gaban da aka samu a shekara goman da suka gabata. A yayin da aka samu gagarumin ci gaba a samun ƴancin mata - kama daga samun ƙarin mata a matakan shugabanci zuwa fafutukar MeTeooMovement - sai dai ga mata da dama a wasu lungunan a duniya, ba su ma san ana yi ba.
Jerin sunayen ya bayyana rawar da mata suka takawa a lokutan rikice-rikice a faɗin duniya a 2022 - daga jarumtar da mata suka nuna wajen kawo sauyi a Iran, da matan da suka nuna jajircewa a yakin Ukraine da Rasha. Sannan a karon farko, mun bukaci matan da suka taba shiga cikin Mata 100 a shekarun baya suk turo mana wadanda suka tunanin sun cancanci shiga na bana.
Siyasa da Ilimi

Roza Salih , Scotland
Yar siyasa kuma mai aikin jinyar sa kai
A Mayun 2022 ne Roza Salih ta zama 'yar gudun hijra ta farko da aka zaba a Karamar Hukumar Glasgow ganin ta shigo Scotland ne tana karama tare da iyayenta bayan yaki ya sa sun gudu daga kasarsu Iran. Yanzu kansila ce a Jam'iyyar SNP na mazabar Pollok. Salih tana fafutikar kwato hakkin 'yan gudun hijira tun tana karama, sannan ita da kawayenta sun taba haduwa domin zanga-zangar kama wata kawarsu.
Gangaminsu mai suna The Gasgow Girls ya ja hankalin mutanen kasar a kan halin da 'yan gudun hijira suke ciki. Salih ta hada hannu da wasu suka kirkiri Scottish Solidarity with Kurdistan, inda suka ziyartar yankin Kurdish a kasar Turkiyya domin kwato hakkin dan Adam.

Maeen Al-Obaidi, Yemen
Lauya
A lokacin da yakin kasar Yemen ya kazanta a bana, Lauya Maeen Al-Obaidi ta cigaba da neman wanzar da zaman lafiya a birnin Taiz. Ta zama mai shiga tsakani ne, inda takan shiga tsakani domin musayar fursunoni tsakanin kungiyoyin yaki. Duk da cewa ba ta cika samun nasarar dawo da mayakan zuwa gidajensu da rai ba, tana kokarin tabbatar da cewa ko da gawar mutum ce ta dawo gidansu.
Tana aikin sa kai a Kungiyar Matan Yemen, inda take kare matan kasar da aka tsare a fursuna. Ita ce lauya ta farko da ta kai matsayin babbar lauya wato Lawyers Syndicate Council, inda take lura da kare hakki da 'yantar da mutane.

Fatima Amiri, Afghanistan
Daliba
Matashiya Fatima Amiri tana cikin wadanda suka tsira daga harin kunar bakin wake a wata cibiyar Kabul, harin da ya ci sama da mutum 50, mafi yawansu dalibai mata. Ta ji raunuka da dama, ciki har da rasa ido da raunuka a habanta da kunne.
A lokacin da take warkewa, sai ta rubuta jarabawar shiga jami'a a watan Oktoba, inda ta samu maki sama da kashi 85. Burinta yanzu shi ne ta karanci kimiyyar kwamfuta a Jami'ar Kabul sannan ta ce rasa idonta a harin kara mata karfin gwiwa ya yi.

Nathalie Becquart, Vatican
Mai hidimar Coci
Nada ta mukamin karamar sakatariya da Fafaroma Francis ya yi na bangaren malaman Coci na Synod of Bishop ya sa ta zama mace ta farko da ta fara rike wannan matsayin. A wannan matsayin nata, ta kasance na gaba-gaba wajen ba Fafaroma shawara a kan muhimman abubuwa da suka shafi Cocin Katolika, sannan kuma ita kadai ce macen da ke da kuri'a a cocin. Sakatare Janar na Cocin ya fada a shekarar 2021 cewa nada ta wannan matsayin ya nuna cewa "An bude wa mata wata kofa."
A baya can, mai hidimar Cocin na Xavieres na kasar Faransa ta kasance mace ta farko da ta rike darakta a cibiyar wayar da kan matasa harkokin addinin Kirista da sana'o'i a kasar Faransa wato National Service for the Evangelism of Young People and Vocation.
Kamar yadda Fafaroma Francis ya bayyana, "Aiki ne na adalci a yi yaki da nuna bambancin kowane iri ne ga mata... Idan muka hada kai, muna bukatar karin karfin gwiwa domin samun karin mata a mukaman shugabanci a kowane mataki."
Nathalie Becquart

Taisia Bekbulatova, Rasha
'Yar jarida
Taisia Bekbulatova fitacciyar 'yar jarida ce a kasar Rasha da ta assasa gidan jaridar Holod a shekarar 2019. Gidan jaridar ya kawo labarai muhimmai game da yakin Ukraine tare da bayyana rashin adalci da aka yi wa mata. Gwamnatin Rasha ta rufe jaridar, wadda ta intanet ce a watan Afrilu a wani shirin gwamnati na yaki da gidajen jarida masu zaman kansu.
Duk da haka, Bekbulatova da ma'aikatanta sun cigaba da aiki, wanda hakan ya kara musu mabiya. Bekbulatova ta tsere daga Rasha a shekarar 2021 bayan an fara mata kallon 'wakiliyar kasashen waje', sannan ta je har kasar Ukraine da kanta domin dauko rahoton yadda yakin ke wakana.
"Ban yarda cewa akwai abin da ba zai yiwu ba. Cigaban zamani ya sa yanzu komai babu wahala a barnata shi, sannan hakkin mata ne na farkon barnatawa."
Taisia Bekbulatova

Kristina Berdynkykh, Ukraine
Yar jarida
A yakin Ukraine, fitacciyar 'yar jarida Kristina Berdynskykh ta yi tafiya zuwa kasarta domin dauko rahoton yankin da Rasha ke jefa bama-bamai. Wasu daga cikin ayyukanta sun fi mayar da hankali a kan yadda ake gudanar da rayuwa a biranen da ake yakin.
An haife ta ne a birnin Kherson, ta yi aikin kawo rahoton siyasa na sama da shekara 14 a birnin Kyiv, ciki har da Mujallar NV da wasu tashosin talabijin da gidajen radiyo. Ita ta kirkiri jaridr e-People a kafofin sadarwa inda take kawo rahoton Juyin juya halin Ukraine, sannan daga bisani ta mayar da mujallar ta zama littafi.

Maria Fernand Castro Maya, Mexico
Mai fafutikar kare hakkin nakasassu
Kasancewarta mace mai shan wahalar fahimtar karatu, Fernanda Castro tana fafutika ne domin 'yan uwanta masu irin wannan matsalar su samu shiga siyasa. Tana kuma cikin kungiyoyi kare hakkin masu nakasassu, wadanda suke samun goyon bayan Human Rights Watch, inda suke nema duk jam'iyyar siyasar kasar Mexico ta sanya su a cikin harkokinsu.
Aikinta sun kunshi samar da dama ga irinta domin su shiga a dama da su siyasa. Castro tana cikin tawagar Mexico da suka je taron Majalisar Dinkin Duniya, inda ta yi jawabi a kan hakkin nakasasu. Sannan wakiliya ce ga kungiyoyin neman a rika damawa da kowa ta duniya.

Chanel Contors, Austreliya
Mai fafutikar yaki da fyade
Ita ce ta assasa kungiyar 'Teach Us Consent' mai kokarin ilimantarwa game da jinsi, a shekarar 2021 ce Chanel Contos ta wallafa wani sako a shafinta na Instagram tana tambayar ko akwai wanda ya san wata da aka taba cin zarafinta a makaranta, inda a kasa awa 24, sama da mutum 200 suka amsa cewa akwai.
Wannan ya sa ta fara gangamin kira da gaggauta ilimantarwa game da saduwa a kasar Austreliya. Kokarin wayar da kan mutanen da ta yi ya sa za a mayar da wannan ilimin ya zama wajibi daga ajin wasa har zuwa shekara 10 daga shekarar 2023. Yanzu tana wayar da kan mutane kan yadda ake cire kororon roba ba tare da amincewar mace ba, tare da yin kira da a mayar da hakan laifi.

Eva Copa, Bolivia
Yar siyasa
Eva Copa tsohuwar shugabar dalibai ce daga yankin Aymara da a yanzu haka take girgiza siyasar kasar Bolivia. Bayan rashin sa'ar samu tikitin jam'iyyarta na tsayawa takarar Magajin Garin El Alto, wanda shi ne birni mafi girma na biyu a kasar, sai ta mara wa dan takarar jam'iyyarta baya, inda suka ci zabe da kashi 69 na kuri'u. Kwanan nan ta sanar da wasu tsare-tsare da suke yi domin mata a birnin, wanda zai karfafi mata da kare musu hakki.
Copa ba bakuwa ba ce a siyasa kasancewa ta taba zama sanata tsakanin shekarar 2015 zuwa 2020. Ficewarta daga jam'iyya mai mulki wani abu da ake ganin zai kawo sauyi a siyasar Bolivia.
"Muna bukatar karin shugabanni mata: Mata su kasance a tsaye, ba a tsugune ba."
Eva Copa

Joy Ngozi Ezeilo, Najeriya
Farfesar shara'a
A matsayinta na tsohuwar farfesa, kuma Shugabar Tsangayar Karatun Shara'a ta Jami'ar Najeriya wato University of Nigeria, kuma tsohuwar wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya a kan safarar mutane, Joy Ezeilo tana cikin mutane na gaba-gaba wajen kare hakkin dan Adam.
Ita ce daraktar farko ta kungiyar Women Aid Collective (WACOL), kungiyar da ta kwashe akalla shekara 25 da suka gabata wajen ba mata taimako wajen shara'a, sannan sun ba mata 60,000 marasa karfi muhallI a Najeriya. Ita ce kuma ta assasa Cibiyar kai korafin fyade ta Tamar Sexual Assault Referral Center domin taimakon wadanda aka ci zarafinsu.

Marubuci, Chimamanda Ngozi Adichie, wadda take cikin Matan 100 na BBC na 2021 ce ta bayar da sunanta.
"Farfesa Ezeilo ta taba rayuwar mutane da dama ta hanyar taimakon marasa karfi a kotu, musamman mata da 'yan mata da aka danne musu hakki."

Ibijoke Faborode, Najeriya
Wadda ta assasa ElectHER
Ta hanyar amfani da kungiyar ElectHER, Ibijoke Faborode tana girgiza yanayin siyasar mata a Najeriya. kungiyar ta shirya tarukan kara wa juna sani ga mata domin wayar da kansu kan shiga a dama da su a siyasa, sannan ta gana da mata sama da 2,000 game da harkokin siyasa a Afirka. a wani gangami da ta yi na #Agender35, kungiyarta tana daukar nauyin mata 35 da suke takara a matakin tarayya da jihohi a zaben 2023 ta hanyar karfafa musu da kudade da sauran tallafin.
Ita ce kan gaba wajen kirkirar manhajar African feminist wadda za ta tattara kuri'un zabe. Yanzu haka Faborode tana cikin jagororin Gidauniyar Democracy and Culture, wadda ke kokarin gano sababbin hanyoyin inganta dimokuradiyya.

Erika Hilton, Brazil
Yar siyasa
Erika Hilton ce maca baka wadda ta sauya jinsi ta farko da ta lashe zabe a Majalisar Brazil. Erika mai fafutikar yaki da nuna bambancin launin fata ce da kuma 'yancin masu madigo da luwadi.
Tana karama, an kore ta daga gida ta koma rayuwa a titi kafin ta fara jami'a. Kasancewar ta shiga harkokin siyasar makaranta, sai Hilton ta koma Sao Paulo ta shiga Jam'iyyar PSOL. A shekarar 2019, aka zabe ta a Majalisar Birnin garin, inda a nan ta samu damar jagorantar yin dokar Asusun Yaki da Yunwa a birnin wanda shi ne mafi girma a Brazil.
"Fafutikarmu ita ce a samu daidaito wajen damarmaki da albashi da kawo karshen nuna bambancin jinsi ko mutum baki ne ko fari ko talaka ko mai arziki ko wanda ya canja jinsinsa."
Erika Hilton

Park Ji-hyun, Koriya ta Kudu
Mai fafutikar gyara siyasa
Lokacin tana dalibar jami'a ce Park Ji-hyun ta bankado babban wajen hada zinace-zinace na intanet na kasar Koriya ta Kudu da ake kira da Nth rooms. A bana ne ta fito ta bayyana yadda lamarin ya auku, sannan ta shiga siyasa, inda take neman goyon bayan 'yan mata masu kada kuri'a.
Lokacin da Jam'iyyar Democratic Party ta fadi zaben Shugaban Kasa, sai aka bayyana ta a matsayin shugabar riko. Tana kuma cikin kwamitin mata, wanda ke kokarin hana laifukan da suke da alaka da saduwa. A watan Yuni, jam'iyyar ta kara rasa wasu kujeru, wanda hakan ya sa ta yi murabus. Duk da cewa ba ta wani mukami a yanzu, tana cigaba da fafutikar samar da daidaito a bangaren siyasa.
"A duniya, zinace-zinacen yanar gizo yana kawo tarnaki da hakkin mata, kuma akwai bukatar mu magance wannan matsalar a tare."
Park Ji-hyun

Zahra Joya, Afghanistan
Yar jarida
A shekara shida da suka yi a karkashin mulkin Taliban, Zahra Joya sai ta koma Mohammad kuma ake kiranta namiji domin ta samu zuwa makaranta. Lokacin da sojojin hadakar karkashin Amurka ta kifar da gwamnatin Taliban a shekarar 2001, sai ta koma amfani da sunanta na Zahra a makaranta. Ta fara aikin jarida ne a shekarar 2011, sannan a lokuta dama, ita ce kadai take kasancewa mace a dakin watsa labarai.
Ita ce ta bude Kamfanin Rukhshana Media, wanda shi kadai ne kamfanin watsa labarai mai kare hakkin mata, wanda aka sanya wa suna saboda wani dan shekara 19 da 'yan Taliban suka jefe. An dauke Joya daga kasar ta Afghanistan, inda a yanzu haka take gudanar da kamfanin daga Birtaniya, inda take samun mafakar siyasa. Ita ce ta lashe kyautar Gidauniyar Gates ta 2022 bisa sauyin da take kawowa.
"Ina da yakinin cewa alkalami ya fi takobi, kuma dole ne mu rika bayyana irin rashin adalcin da ake yi wa mata."
Zahra Joya

Ursula von der Leyen, Jamus
Shugaban European Commission
A matsayinta na mace ta farko Shugabar Europen Commission, Ursula von der Leyen 'yar siyasa ce a kasar Jamus da ta yi aiki tare da Shugabar Kasar, Angela Merkel, kuma ita ce mace ta farko da ta zama Ministar Tsaro a kasar.
An haife ta ne a garin Brussels, ta karanci tsimi da tanadi da likitanci ne kafin ta koma harkokin siyasa. Ta karbi shugabancin EU din ne a shekarar 2019, sannan ita ce ta jagoranci hukumar a duk fafutikar da aka yi na Brexit da annobar Covid-19 da kuma yakin Ukraine. Tana kan gaba wajen dokar samar da daidaito a kamfanoni a kasashen Turai da aka tabbatar a bana.

Firayi Ministan Finland Sanna Marin da ta kasance cikin Mata 100 na BBC na 2020 ce ta bayar da sunanta.
"Kasancewar yankin Turai na fama da rikice-rikice da dama, Ursula von der Leyen ta yi kokari matula wajen taimakon kasashen Turai wajen magance wadannan matsalolin. Kwarewarta wajen shugabanci abin yabo ne. An fuskanci matsaloli da dama a Turai, amma karfin gwiwarta wajen fuskantar matsalolin abin a yaba ne."

Naomi Long, Northern Ireland
Yar siyasa
Naomi Long tsohuwar Ministar Shara'a ce da ta kawo dokar yaki da laifuffukan cin zarafin mata a bana, kamar su cin zarafin mata a yanar gizo da saduwa da karfin tuwo da sauransu. Haka kuma kasancewar an taba mata barazana ita kanta ya sa take wayar da kan mutane kan barazanar da ake yi wa mata 'yan siyasa.
Asalinta injiniyar tsara gini ce, amma ta shiga Jam'iyyar Alliance Party a shekarar 1995. Bayan ta rike mukamin Magajiyar Garin Belfast, sai ta zama Ministar a Jam'iyyar Allian ta farko da ta wakilci Westmindter a shekarar 2010, inda ta doke tsohon Babban Minista Peter Robinson daga kujerar da ya rike tsawon shekara 30.
"Ya kamata mu yi yaki da al'adar nan ta mayar da cin zarafi kamar ba komai ba. Wannan na nufin dukanmu na hada hannu wajen yaki da nuna bambanci tsakanin maza da mata."
Naomi Long

Ayesha Malik, Pakistan
Mai shara'a
A bana aka nada ta a matsayin mace ta farko mai shara'a a Kotun Kolin kasar Pakistan. Mai shara'a Ayesha A. Malik ta yi wallafe-wallafe da hukunce-hukkunce a kan kare hakkin mata, ciki har da wanda ya fi fice na gwajin fyade ta hanyar sanya yatsa biyu a gaban macen. Kafin hukuncin da ta yanke a 2021, irin wannan gwajin ake yi domin budurtakar.
Hadi da matsayinta a Kotun Koli, Ayesha tana horar da alkalai a duniya, sannan ta shirya taruka domin mata alkalai a Pakistan, inda take karfafa musu gwiwa a bangaren shara'a.
"Dole mata su canja tunanin mutane-Ciki har da tunaninsu, su rika karawa junansu sani ta hanyar karfafa junansu."
Ayesha Malik

Zara Mohammadi, Iran
Malama
A matsayinta na daya daga cikin wadanda suka assasa kungiyar Nojin Socio-Cultural Association, Zara Mohammadi ta kwashe sama da shekara 10 tana koyar da harshen Kurdish a yankinta na Sanandaj.
Dokar Kasar Iran ta bayar da damar koyarwa a harshen yanki, amma lauyoyi da 'yan gwagwarmaya suna ganin hakan bai kamata ba, wanda hakan ya sa yara ba sa koyon harshen iyayensu a makaranta. Gwamnatin Iran ta zargi Mohammadi da "kirkirar kungiya da tara mutane domin tayar da zaune tsaye" wanda hakan ya sa aka yanke mata hukuncin daurin shekara biyar. Tana zaune a gidan yari tun Janairun 2022.

Mia Mottley, Barbados
Firaminista
A matsayinta na firaminista mace ta farko a Barbados, Mia Mottely ta yi nasarar sake cin zaɓe da gagarumin rinjaye a karo na biyu a watan Janairu. Ita ke jagorantari jam'iyyar Labour ta Barbados tun 2008. Ta ja ragamar ƙasar wajen yanke alaƙa da iyalan Masarautar Birtaniya, ta cire sarauniya a matsayin shugabar ƙasar, lamarin da ya sa ƙasar ta zama sabuwar jamhuriya a duniya.
Mottley ta yi fice wajen yin magana a kan sauyin yanayi. A wajen taron COP27 ta soki ƙasashe masu arziki da gaza magance matsalolin sauyin yanayi, tana gargadin cewa za a iya samun ƴan gudun hijira biliyan ɗaya nan da shekarar 2050 idan ba a ɗauki mataki ba.

Sepideh Qoliyan, Iran
Mai wayar da kan mutane kan siyasa
Sepideh Qoliyan dalibar bangaren shara'a ce da aka daure na shekara biyar saboda ta goyi bayan kwato hakkin ma'aikata a yankin Khuzestan, a Kudu maso Gabashin Iran. Yanzu haka ta yi kusan shekara hudu a gidan yari guda hudu daba-daban a kasar Iran, ciki har da Evin, wanda nan ne aka tsare 'yan siyasa da aka tura gidan yari.
Har daga gidan yari, ta cigaba da gudanar da ayyukanta, inda take aikowa da sakonnin murya, inda a ciki take bayyana halin kuncin da ta shiga. Ta kuma zama muryar matan da suke cikin fursuna, sannan ta rubuta littafi a lokacin da aka bayar da belinta a kan irin rashin adalcin da mata suke fuskanta a gidajen yarin Iran.

Simone Tebet, Brazil
Sanata
Ana mata kallon wadda za ta iya rage fargabar rabuwar kai da kasar fama da ita. Sanata Simone Tebet ce ta zo ta uku a zaben Shugabar Kasar ta bana. Ta taba zama wakiliyar jiharta a shekarar 2002, sannan ta zama Magajiyar Garin yankinta na Tres Lagoas a shekarar 2004 da 2008. A shekarar 2014 ce aka zabe ta a matsayin sanata, inda ta lashe sama da kashi 52 na kuri'un da aka kada.
Ita ce mace ta farko da ta shugabanci kwamitin Dokar Kasa da Shara'a na Majalisar Dattawar kasar, wanda shi ne babban kwamiti a majalisar. Farfesar shara'a ce kuma wadda ta kasance shugabar kwamitin yaki da cin zarafin mata.
"Ya kamata kowa ya gane cewa nan gaba duniyar za ta koma hannun mata, sannan mace za ta samu damar zama duk da abin da take da burin zama."
Simone Tebet

Kisanet Tedros, Eritrea
Malama
Beles Bubu wata tasha ce a YouTube da ake koyar da yaran kasar Eritrea harshensu da al'adunsu, wanda kuma Kisanet Tedros din ce ta bude. An haife ta ne a kasar Ethiopia, kuma a can ta girma. Tun tana karama ta fahimci bukatar da ake akwai na fahimtar harshen gida domin sanin asalin mutum.
Tare da ma'aikatanta suna hada hannu da wasu daga Eritea da Uganda da Democratic Republic of Congo domin koyarwa ta hanyar amfani da bidiyoyi da muryoyi da sauransu. Iyayen yankin Tigrinya da yaransu ne suke kallon bidiyoyinsu a kasar Eritrea da Habasha. Tedros ta kuma shirya kalankuwar yara ta Beeles Bubu Kids Festival domin yara 'yan gudun hijira a Kampala na kasar Uganda.

Cheng Yen, Taiwan
Mai hidimar addinin Buda
Ana kallon Cheng Yen a matsayin wata jigo wajen kawo cigaba a addinin Buda na kasar Taiwan. Ita ce ta assasa Gidauniyar Tzu Chi kuma a kan kira ta a wasu lokutan da 'The Mother Teresa of Asia'.
Ta assasa kungiyar a shekarar 1966 tare da matan aure 30, inda suke tara kudi domin taimakon mabukata. Yanzu kungiyar ta fadada, inda suke da miliyoyin mabiya a duniya, inda suke taimakon mabukata da kayayyakin jin kai irinsu magunguna sannan suna da makarantu da asibitoci. Yanzu ta kai shekara 80, amma mabiyanta na cigaba da ayyukan da take yi, kuma ba da dadewa ba ma sun kai agaji zuwa kasar Ukraine.

Nazanin Zaghari-Rafcliffe, Birtaniya/Iran
Ma'aikaciyar jin kai
"Ya kamata duniya ta hada kai domin tabbatar da cewa babu wanda aka tsare ko aka yi garkuwa da shi domin laifin da bai aikata ba," kalmomi ne na Nazanin Zaghari-Rafcliffe, wadda 'yar asalin kasar Iran ce da aka haife a Birtaniya bayan Gwamnatin Iran ta sake ta a watan Maris bayan dogon lokacin da mijinta Richard ya yi yana bukatar hakan daga Gwamnatin Birtaniya.
Zaghari-Rafcliffe ta shiga komar Gwamnatin Iran ce lokacin da ta je kasar hutu tare da 'yarta a shekarar 2016, inda Gwamnatin Iran ta yi amfani da ita wajen cim ma wata manufarta ta diflomasiyya. Ta yi shekara shida a tsare-inda da farko aka yanke mata hukuncin laifin kokarin kifar da Gwamnatin Iran. Da ta kammala daurin farko, sai aka sake yanke mata wani hukuncin a shekarar 2021, har sai da aka samu matsaya ta diflomasiyya. Zaghari-Rafcliffe ta musanta dukkan zargin da ake mata.

Olena Zelenska, Ukraine
Uwargidan Shugaban Kasa
Ta kasance fitacciyar 'yar jarida ce mai aiki a bayan fage. Sai dai fuskarta ta fito fili ne bayan mijinta Volodymyr Zelenskyy ya zama Shugaban Kasar Ukraine a shekarar 2019. A matsayinta na Uwargidan Shugaban Kasa, ta yi aiki matuka domin kare hakkin mata da dabbaka al'adun kasar Ukraine.
Bayan kasar Rasha ta fada wa Ukraine da yaki, ta rika amfani da shafukanta wajen nuna halin da mutanen Ukraine ke ciki, inda ta zama Uwargidan Shugaban Kasa ta farko da ta yi jawabi a gaban Majalisar Dokokin Amurka. Yanzu tana aiki ne domin gyara tunanin yara da iyalan da yakin ya jefa cikin damuwa.
"Yanzu mata sun karbi shugabanci da dama sama da lokacin da ake zaman lafiya... duk macen da ta ga yakin nan, ba za ta taba gajiyawa ba. Ina da tabbacin cewa karfin zuciyarmu zai karu."
Olena Zelenska
Al'ada da Wasanni

Dima Aktaa, Syria
Yar wasan tsere
A shekarar 2012 ce aka jefa bam a gidansu Dima Aktaa, wanda ya jawo mata asarar kafarta da take amfani da ita wajen tsere. Kimanin kashi 28 na 'yan Syria nakasassu ne, wanda ya kusa rubanya ka'ida kamar yadda kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna. Bayan shekara 10, Aktaa ta koma Birtaniya, inda yanzu haka take atisaye domin shiga gasar tseren nakasassu ta 2024.
Bayan ta jagoranci tara wa 'yan gudun hijira kudi a lokacin annobar covid-19, sai aka saka ta a cikin 'yan wasan kwallon nakasassu na Ingila, wato The Lionhearts. Labarinta ya fito kwanan nan a bidiyo mawakiya Anne-Marie mai suna Beutiful, kuma tana cigaba da wayar da kan mutane a kan karfafa gwiwar nakasassu.

Zar Amir-Ebrahimi, Iran
Jaruma
A bana, fitacciyar jaruma Zar Amir-Ebrahimi ta zama jarumar Iran ta farko da ta lashe Gwarzuwar Jaruma a birnin Cannes saboda rawar da ta taka a fim din Holy Spider, shirin da aka yi a kan wani kasurgumin dan bindiga da ya fi kai farmak kan karuwai.
Dole ta sa Amir-Ebrahimi ta tsere daga Iran domin gudun kamu bayan an yada bidiyon tsiraicinta ba tare da izininta ba, inda aka fara amfani da shi wajen farfaganda game da soyayyar da ta yi a baya. A shekarar 2008 ce ta koma Paris da zama, inda ta assasa kamfanin shirya fina-finanta, inda daga can ne take cigaba da harkokin fim dinta.

Selma Blair, Amurka
Jaruma
An santa ne a rawa da ta taka a fina-finan Cruel Intentions, Legally Blonde da The Hellboy franchise. Selma Blai jarumar fina-finai ce ta Amurka.
A shekarar 2018 ce aka gano tana fama da cutar yakunewar fata, wadda tun daga lokacin ta fara gangamin wayar da kan mutane a kan cutar, inda take amfani da kanta a matsayin misali. A bana ta fitar da littafin rayuwarta mai suna Mean Baby, sannan ta hada hannu da kamfanin kwalliya na ability-inclusive domin samar da kayan kwalliya masu sauki amfani ga masu lalurar.
"Nima mace ce da ta fuskanci kalubale da dama a baya da za iya fassarawa ta bangarori da dama, wadanda kuma sun kusa karya min gwiwa, amma na samu nasarar tsallakewa ne saboda taimakon wasu matan."
Selma Blair

Ona Carbonell, Spaniya
Ƴar ninƙaya
Ƴar ninƙaya ƴar ƙasar Soaniya Ona Carbonell ta yi ta fafutuka kan wayar da kan mutane su fahimci ba komai ba ne don uwa ta zama ƴar tsere. Matar wacce sau uku tana zuwa gasar Olymppic, ta ci lambobin yabo har fiye da 30, da suka haɗa da na azurfa da tagulla.
A shekarar 2020 ta haifi ɗanta na fari sannan ta fara atisaye don samun zuwa gasar Olympic ta Tokyo. Ta bayyana ɓacin ranta kan dokokin da suka ce ba za ta iya shayar da danta a wajen gasar ba. A bana ta sake haihuwar ɗanta na biyu. Ta bayar da labarin rayuwarta a wani shiri na talabijin inda ta ƙarfafa wa sauran mata ƴan wasannin tsere gwiwa da cewa za a iya hada wasanni da haihuwa da reno.

Sarah Chan, Sudan ta Kudu
Yar kwallon kwando
Sarah Chan tsohuwar 'yar kwallon kwando ce da a yanzu take horar da matasa harkokin wasanni a Kudancin Sudan da Kenya. Ita ce mace ta farko mai fita neman 'yan wasa a Afirka, da kuma kungiyar kwallon kwanda ta Toronta Raptors.
Sarah Chan tsohuwar 'yar kwallon kwando ce da a yanzu take horar da matasa harkokin wasanni a Kudancin Sudan da Kenya. Ita ce mace ta farko mai fita neman 'yan wasa a Afirka, da kuma kungiyar kwallon kwanda ta Toronta Raptors.
"Za ka zama abin da kake da burin zama idan ka yi imanin haka. Don haka ka yi amanna da cikar burukanka a nan gaba."
Sarah Chan

Priyanka Chopra Jona, Indiya
Jaruma kuma forodusa
Priyanka Chopra Jona ta fito a fina-finai sama da 600, wanda hakan ya sa ta kasance cikin manyan jaruman Masana'antar Bollywood ta Indiya. Bayan fim dinta na farko a shekarar 2002, tsohuwar Gwarzuwar Kyau ta Duniyar ta kafa tarihin shiga fina-finan Masana'antar Hollywood ta Amurka, inda ta kasance 'yar yankin Gabashin Asiya ta farko da ta jagoranci fim din Amurka a fim din Quantico mai dogon zango na 2015.
Fina-finanta na Amurka sun hada da Isn't It Romantic da The Matrix Resurrections. Tana da kamfanin shirya fina-finanta a Indiya. Chopra ambasada ce a asusun Unicef, inda take fafutika a kan hakkin yara da ilimin mata.
"Kungiyar MeToo da sauran kungiyoyin mata irinta masu hada kai domin kare mutuncin mata suna kokari-Lallai akwai muhimmanci a kasancewa tsintsiya madaurinki daya."
Priyanka Chopra Jona

Billie Eilish, Amurka
Mawaƙiya-mai rubuta waƙa
Billie Eilish wacce ta samu lambar yabo ta Grammy a tarihi, ta yi fice wajen yin sabbin abubuwa ta hanyar waƙoƙinta - daga waƙarta ta Your Power, inda ta yi wa masu cin zarafin yara mata tatas, zuwa waƙarta ta All The Good Girls Go To Hell, wacce ta yi maganar sauyin yanayi.
Ta kafa tarihi a bana wajen zama mafi ƙarancin shekaru da ta mamaye kanun labarai a bikin kalankuwa na Glastonbury, inda ta yi waƙarta a wajen mai nuna adawa da matakin Kotun Ƙolin Amurka na kawo ƙarshen damar da kundin tsarin mulki ya bayar na zubar da ciki. Ta yi magana ƙarara a kan halittar jiki, da lokutan da ta yi fama da matsananciyar damuwa da kuma cutar da ke da alaƙa da jijiyoyi ta Tourette.
Ina cikin matuƙar jin daɗin yanayin da muke ciki a yanzu. Mata su ne a sama. Akwai wani lokaci a rayuwata da na rasa madafa saboda ban ga ana ɗaukar ƴan mata irina da muhimmanci ba.
Billie Eilish

Ons Jabeur, Tunisa
Yar wasan tennis
Bayan kafa tarihin da ta yi na halartar Gasar Wimdledon ta 2022, 'yar wasan ta Tunisa ta kafa tarihin zama Balarabiya ta farko da ta kai wasan karshe. Sannan bayan wata daya ta sake kai wa wasan karshe a Gasar US Open.
Yar shekara 28 ce da ta fara wasan tennis tun tana 'yar shekara 3, sannan har ta kai ga zama ta zama a jerin 'yan wasan tennin mata na duniya-wanda shi ne matsayi babba da dan Afirka namiji ko mace ko Balarabe ya kai. Jabeur ta lashe gasa uku, sannan ana mata kallon gwarzuwa wajen karfafa gwiwar masu tasowa.

Sneha Jawale, Indiya
Ma'aikaciyar jin kai
A lokacin da iyayen ta suka kasa cika sharudan sadaki a Disamban 2000, sai mijin Sneha Jawale ya cinna mata wuta da kalanzir, sai dai iyayenta ba su kai kara wajen 'yan sanda ba. Bayan mijinta ya tafi da dansu, sai ta fara fafutikar gyara rayuwarta wajen aikin tsara labarai da sauransu da ba a bukatar ganin fuskarta.
Jawale, wadda yanzu ma'aikaciyar jin kan al'umma ce an bukaci ta fito a fim din Nirbhaya, da aka shirya domin tuna wadanda aka yi fyade na Delhi. Fitowa fili duniya ta ganta ya taimaka mata wajen cire tsoron da take yi na bayyana kanta.
"A shekara 10 da suka gabata, yadda ake kallon wadanda suka kone da wuta ko guba ya canja. Ba na ganin wadda ta fi kowa kyau a duniya ta fi ni kyau. Nima kyakkyawa ce."
Sneha Jawale

Reema Juffali, Saudi Arabia
Mai tseren mota
A shekarar 2018, Reema Juffali ta kafa tarihin zama mace 'yar kasar Saudi Arabia ta farko mai gasar tseren mota. A bana ta assasa kungiyarta, Theeba Motorsport domin shiga gasar duniya ta GT Open sannan ta samar da dama ga masu bukatar shiga gasar tseren na mota. Ta hanyar kungiyarta din, kwararriyar matukiyar tana samar da damarmaki da dama na ilimi domin habaka harkar wasanni.
Ta zama abar koyi ga sauran mata masu tseren tuki a duniya, wanda hakan ya sa Juffali take da burin kasancewa mace ta farko da za ta shiga babbar Gasar Le Mans 24-hour race da kungiyarta ta Theeba Motorsport.
"Har yanzu ana nuna wariya a kan mata. Karfafa gwiwa daga gida ya kamata ya faro, sannan daga al'umma domin a samar sauyin da ake bukata."
Reema Juffali

Kadri Keung, Hong Kong
Tela
Dinka kaya ta hanyar zayyana yanayin duniya mai kyau domin tsofaffin mutane yana cikin ababen sha'awar Kadri Keung. Ta assasa kamfanin dinkin RHYS tare da mahaifiyarta Ophelia Keung a shekarar 2018, wanda suka samo karfin gwiwa daga kakarta bayan ta gano cewa tufafin tsofaffi ba a musu kwalliya sosai.
A matsayinta ta wadda ta karanci dinki, Keung tana amfani da iliminta wajen biyan bukatar kwastomominta. Kamfaninta ya dauki nauyin koyar da mata marasa karfi guda 90 dinki, cikinsu har da nakasassu. A shekarar 2022 ce Keung ta assasa boundless, wanda kamfani ne shi ma na dinki.

Mie Kyung (Miky) Lee, Koriya ta Kudu
Mai shirya fina-finai
A matsayinta na mai matuƙar son wasanni, Miky Lee na jagorantar al'amuran al'adu na Koriya. Tana gaba-gaba wajen nasarar da ke K-pop ke samu a duniya sannan tana taka rawa wajen shirya bikin kalankuwa na KCON. Sannan ita ce mai shirya fim ɗin Parasite da ya ci kyautar Gasar Oscar saboda kyawun hoto.
Lee ce matsaimakiyar shugaba ta katafaren kamfanin da ke shirya fina-finai da dirama a talabijin na CJ ENM ta Koriya ta Kudu.

Ƴar fim Rebel Wilson a natsayin gwarzuwa a 2021.
Ina daukarta a matsayin abar koyi kuma Jajirjacciyar mace ce. Ta wakilci tare da ciyar da al'adarta gaba a duniya.

Laura McAllister, Wales
Farfesa kuma tsohuwar 'yar kwallon kafa
A matsayinta na tsohuwar kyaftin din tawagar 'yan wasan kwallon kafa mata ta kasar Wales, Laura McAllister ta rike wasu manyan mukamai a bangaren wasanni da gwamnati. Yanzu haka ita ce Mataimakiyar Shugabar Kwamitin Kwallon Mata na Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, sannan ta tsaya takarar zama wakiliyar Uefa a Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya a watan Afrilun 2021. Darakta ce kuma a Hukumar Football Asociatio of Wales Trust.
Yanzu haka farfesa ce a Jami'ar Cardiff, kuma mai sharhi a kan harkokin siyasar Wales. A bana an zabe ta a matsayin ambasadar masu madigo da luwadi da suka halarci Gasar Kwallon Kafa ta Duniya a Qatar. Sai dai an bukaci ta cire alamar goyon bayan masu madigo da luwadin a lokacin da take shiga filin wasa a Qatar.

Milli, Thailand
Mawakiyar gambara
Mawakiya, kuma marubuciya Danupha Khanatheerakul, wadda aka fi sani da Milli tana amfani da wasu baitocin waka masu tayar da hazo domin magance wasu matsalolin al'umma kamar wayar da kan mata a kan saduwa da sauransu. tana gambara da harsuna da dama, inda a ciki take hadawa da karyayyen Turancin Ingilishi na yankin mata-maza na kasar Thailand. A wasu lokutan baya ne ta sanar da fitar da kundin wakokinta na farko mai suna BABB BUM BUM.
Ta zama fitacciya ce bayan taron baje kolin Coachella na bana da aka gudanar a kasar Thailand domin yaki da gwamnatin kasar Thailand kan nuna bambanci ta hanyarvcin shinkafar mangoro a gaban al'umma, wanda ba kasafai ake haka a kasar ba. A bara, Gwamnatin Thailand ta tuhumce ta zargin bata suna a lokacin annobar covid-19, wanda hakan ya sa aka rika zanga-zangar yanar gizo na #SaveMilli.

Rita Moreno, Amurka
Jaruma
Jarumai kadan ne suka kai matakin EGOT-Kalmar da ake kiran wadanda suka lashe manyan kyaututtukan Emmy da Grammy da Oscar da Tony Blair-Amma Rita Moreno tana daga cikinsu. Jarumar 'yar asalin Puerto Rico ta kwashe gomman shekaru a harkar fim da waka da rawa.
Ta fito a Singin in the Rain da The King and I, amma fim dinta na Anita ne ya sa ta fara lashe kyautar Oscar. Steven Spielberg sai da ya canja yanayin wata jaruma kacokam saboda ita a fim dinsa karo na biyu. Yanzu Moreno ta haura shekara 90 a duniya.

Salima Rhaidka Mukansanga, Rwanda
Rafare
A wani babban al'amari a harkar kwallon kafar duniya, Salima Rhadia Mukasanga ta shiga cikin mata uku da za su yi alkalancin wasannin a Gasar Cin Kofin Duniya na maza da ake fafata a kasar Qatar a 2022-wanda shi ne karon farko da aka sanya mata a cikin alkalan wasa a kwallon duniya na maza a cikin shekara 92 da fara gasar.
A watan Janairun bana ne ta kasance mace ta farko da ta yi alkalancin wasa a Gasar Cin Kofin Afirka, sannan ta yi alkalancin wasanni a Gasar Olympic ta Tokyo. Yanzu haka ta riga ta yi alkalancin wasannin a babbar gasar kwallon kafa ta maza. Kafin ta koma harkar alkalancin wasanni, ta kasance ma'aikaciyar ungozoma ce.

Alla Pugacheva, Rasha
Mawakiya
Mwakiya Alla Pugacheva ta sayar da sama kaset miliyan 2500, inda a ciki akwai sama da wakoki 500 a cikin kundi sama da 100. Wakokin 'tsarina of Russian pop' ya yi fice matuka wajen nuna al'ada.Ta yi fice ne wajen murya mai zaki, duk da cewa yanzu ta yi ritaya daga waka.
Gwamnatin Rasha ta sha karrama ta saboda wakokinta, amma duk da haka bai hana Pugacheva sukar gwamnatin ba a wasu lokutan. Kwanakin baya ta wallafa wani sako a shafinta na Instagram mai mabiya miliyan 3.6 inda ta nuna rashin jin dadinta kan yakin Ukraine, wanda ya jawo mata yabo a wani bangaren, sannan ya jawo mata zargin cin amanar kasa a wani bangaren.
"An samu cigaba da dama a duniya musamman a wajen fafutikar ilimin mata da dogaro da kansu. Sai dai har yanzu cin zarafin mata na cigaba a wasu kasashe."
Alla Pugacheva

Elnaz Rekabi, Iran
Mai hawa dutse
A Gasar Asian Championship da aka yi a Koriya ta Kudu, Elnaz ta fafata gasar hawa dutse ba tare da kallabi ba domin nuna rashin amimcewarta da mayar da sanya hijabi dole a kasarta. Ita ta zo ta hudu a gasar, amma ta fi samun daukaka ce a tsakanin masu zanga-zanga, Mutane da dama ne suka tarbe ta a Filin Jirgin Saman Tehran lokacin da ta dawo daga gasar, kuma ta sha yabo a kafofin sadarwa.
A wani sakon da ta wallafa a shafinta na Instagram, ta bayyana cewa hijabin ta fadi ya yi, sannan ta bayar da hakuri ga mutanen Iran a tashar talabijin na Gwamnatin Iran bisa nuna damuwarsu. Sai dai wata majiya ta bayyana wa BBC cewa tursasa ta aka yi ta yi jawabin.

Yulimar Rojas, Venezuela
Yar wasan tsalle
Yulimar Rojas 'yar wasan tsalle ce da ta lashe kambun zinari da azurfa a Gasar Olympic sannan ta lashe gasannin duniya sau uku. Yuilmar ta zamo wadda ta kafa tarihin tsalle mafi tsayi bayan ta yi nisan mita 15.7 a Gasar Duniya ta World Athletics Indoor Championship a watan Maris. Yanzu tana shirin kafa wani tarihin ne-wato tsallen mita 16.
An haife ta be a Caracas na kasar Venezuela inda ta taso a yankin talakawa na tsibirin Carribean. Ta bayyana gwagwarmayar da ta sha da take tasowa a matsayin sirrin nasararta. Yanzu tana cikin 'yan wasan Kungiyar FG Barcelona, sannan ana mata kallon gwarzuwa a kasarta. 'Yar madigo ce a bayyane, sannan tana fafutikar kwato hakkin 'yan madigo da luwadi.
"Bai kamata a rika tsoratar da mata ba. Babu wani abin da ba za mu iya ba, a fili yake cewa za a iya raina mu, amma mun riga mun nuna cewa za mu iya abubuwan da za mu iya yi."
Yulimar Rojas

Sally Scales, Austreliya
Mai fasahar kirkira
A shekarar 2022 ce aka saka Sally Scales a cikin kungiyar da za ta yi aiki da Gwamnatin Austreliya a shirin kasar na zaben raba gardama da aka fi sani da 'Voice to Parliament'- wanda wani gangami ne da idan aka samu nasara, asalin mutanen kasar za su samu wakilci a harkokin majalisa.
Mace ce mai daraja kuma mai fasahar kirkira, Scales 'yar kabilar Pitjantjatra ce daga yankin Pipalytjara a kuryar Yammacin Anangu Pitjantjatjara Yankunytjatjara (APY) a kauyen Kudancin Austreliya. Ita ce mace ta biyu da ta shugabanci APY, kuma ita ce Kakakin Art Centre Collective, wadda kungiya ce ta 'yan kasar masu fasahar kirkira.

Tsohuwar 'yar siyasa, Julia Gillard da ta kasance cikin Mata 100 na BBC na 2018 ce ta bayar da sunanta.
"Sally tana da fasahar kirkira da ke amfanar da mutane ta hanyar ilimantarwa, ta jagoranci kawo sauye-sauye da dama da suka taimaka wajen kawo karshen nuna bambancin launin fata da bambancin jinsi."

Nana Darkoa Sekyiamah, Ghana
Marubiciya
Littafinta the Sex Lives of Africab Women an bayyana shi a matsayin "wani babban aiki domin sauya tunanin harkokin saduwa", a wani nazarin littafin da aka yi. The Economist ta sanya littafin a cikin fitattun littafan shekara.
Marubuciya ce, kuma mai fafutikar kare hakkin mata sannan tana cikin wadanda suka kirkiri Adventures from the Bedrooms of African Women- wadda manhaja ce, da tashar rediyon intanet da take watsa labarai na halin da matan Afirka suka shiga na saduwa da sauransu.
"Masu fafutikar kare hakkin mata sun samu nasarar assasa wani dandamali ga mata domin cigaban kansu. Sai dai muna fuskantar kalubale, wanda baya rasa nasaba da nasarorin da muke samu-Sai dai wannan kalubalen yana da alaka da bambancin jinsi."
Nana Darkoa Sekyiamah

Geetanjali Shree, Indiya
Marubuciya
Marubuciya, Geetanjali Shree ta kafa tarihi a bana bayan ta zama 'yar Indiya ta farko da ta lashe gasar marubuta ta duniya da littafinta mai suna Tomb and Sand, wanda fassarar littafinta ne mai suna Ret Samadhi. Haka kuma fassarar littafin da harshen Farasanci ya samu shiga cikin labarai masu kyau na Gasar Emile Guimet.
Shree tana rubuta kagaggun labarai da na gaskiya a harshen Indiya da na Turancin Ingilishi. Ta yi fice ne wajen amfani da harshe da tsari mai kyau. An fassara littafanta zuwa harsunan cikin kasar Indiyan da dama da wasu harsunan na duniya. Tana kuma aiki wajen tsara labarai tare da kungiyar Vivadi, wadda ta kasance cikin wadanda suka assasa.
"Mata sun dade suna fafutikar kwato wa kansu martaba, amma a lokacinmu an samu cigaba a wannan bangarenn, duk da cewa akwai bambanci tsakanin al'adu da matsayi."
Geetanjali Shree

Alexandra Skochilenko, Rasha
Artist
An taba tsare Alexandra Skochilenko saboda sauya littafin farashin babban kantuna da sakonni game da yakin Ukraine, ciki har da bayanai game da wadanda ake tunanin an rasa a harin bam din Mariupol da kasar Rasha ta kai. Bayan wani mai shago ya kai ta kara, sai aka tuhume ta da zargin tauye bayanai game da sojojin Rasha.
A yanzu haka tana tsare ne, inda take jiran a yanke mata hukunci. Tana kallon kanta a matsayin fursunan da ra'ayinta ya kai ta ga haka, kuma tana iya fuskantar har zuwa shekara 10 a gidan yari.
A yanzu haka tana tsare ne, inda take jiran a yanke mata hukunci. Tana kallon kanta a matsayin fursunan da ra'ayinta ya kai ta ga haka, kuma tana iya fuskantar har zuwa shekara 10 a gidan yari.

Velia Vidal, Colombia
Marubuciya
Marubuciya ce sannan mai kokarin adana tarihin yankin El Choco na Colombia. Velia Vidal tana son bayar da labari. Ita ce ta assasa Kungiyar Motete domin habaka karatu da rubutu da yaki da jahilci da kuma adana tarihin Choco. Tana kuma shirya taron karatu da rbutu a yankin domin ganin da take yi wa karatu da rubutu a matsayin makamin yaki da nuna bambancin launin fata da rashin adalci ga yankinsu.
Littafin da ta fitar kwanan nan, Aguas de Estuario shi ne na farko da ya samu tallafin marubuta bakake na Colombia wato Afro-Colombia daga Ma'aikatar Al'adu ta Colombia. Haka kuma mai bincike ce a shirin nan na Afluentes, wanda hadaka ce da Gidan Adana Tarihin Birtaniya.
"Yanzu mun fi sanin tarihin yadda aka rika danne mata, kuma mun fi sanin akwai bukatar a magance hakan, amma ba mu fahimci yadda nuna bambancin launin fata yake kara munana danniyar ba a tsakanin bakake da 'yan asalin kasa."
Velia Vidal

Esraa Warda, Algeria/Amurka
Yar rawa
Esraa Warda 'yar asalin kasar Algeria mazauniyar kasar waje ce, wadda ta fitar da al'adun kasar zuwa idon duniya. Tana fafutikar adana tarihin rawar matan Arewacin Afirka, musamman rawar rai, wadda rawa ce ta al'ada da ke nuni da nuna rashin amincewa da rashin adalci.
Tana cikin daliban Chiekha Rabia, wadda take cikin mata kadan masu rawar rai a kasashen waje. Warda tana sha'awar tafiye-tafiya, sannan malama ce sannan ta baje kolin fasahohinta a gurare daban-daban a duniya ciki har da birnin Washington DC da Landan.
Fafutuka da Wayar da kai

Lina Abu Akleh, Palestian
Mai yakin kare hakkin dan Adam
Lina Abu Akleh 'yar gwagwarmaya ce 'yar asalin kasar Palestian da aka haifa a Armenia, kuma 'yar uwa ce ga 'yar jaridar nan 'yar asalin kasar Palestin da aka haifa a Amurka, Shireen Abu Akleh, wadda mai daukan rahoton Al Jazeera ce da aka kashe a lokacin da take dauko rahoton lokacin da jami'an tsaron Israel suka farmaki West Bank. Sojojin Israel sun bayyana cewa akwai alama mai karfi cewa daya daga ckin sojojinsu ne ya kashe ta da kuskure.
Lina sai ta kasance mai fafutikar tabbatar da adalci ga 'yar uwarta da aka kashe. Tana digiri na biyu a kan harkokin kasashen waje, inda ta fi mayar da hankali kan hakkin dan Adam. Tana cikin shugabannin gobe 100 na Jaridar Times na shekarar 2022.
"Dole mu daura daga inda 'yar uwata Shireen Abu Akleh ta tsaya domin cigaba da bayyana halin da mata suke ciki domin tabbatar da cewa labaran da muke bayarwa da wadanda muke samu na gaskiya ne-kuma hakan ba zai yiwu ba ba tare da mata ba."
Lina Abu Akleh

Tarana Burke, Amurka
Yar gwagwarmaya
Gangamin #MeToo ya shahara a kafofin sadarwa shekara biyar baya, inda miliyoyin mutane a duniya suka rika bayyana halin da suka shiga na cin zarafi. Amma an fara tafiyar ce daga wadanda suka tsira da kuma masu fafutikar Tarana Burke tun a shekarar 2006. Daga baya sai ta sauya kalmar domin wayar da kan mutane kan cin zarafin mata.
Lokacin da sakon twitter na jaruma Alyssa Milano ta karfafa #MeToo, sai ya dauki hankalin duniya, inda aka rika tattauna yadda ake cin zarafin mata, sannan ya ba wadanda suka taba fuskantar hakan damar bayyana halin da suka shiga. Burke ta kasance mai fafutikar kwato hakkin matan da suka fuskanci irin wannan cin zarafi, kuma tana cigaba da kokarin domin kawo sauyi.

Sanjida Islam Choya, Bangladesh
Daliba
Bangladesh na cikin kasashen da aka fi auren wuri a duniya, amma Sanjida Islam Choya tana ta kokarin kawo sauyi. Mahaifiyarta ta yi aure tana karama, amma bayan Choya ta samu karfin gwiwa bayan jin wani bayani da aka gabatar a kan illar auren wuri, sai ta yanke shawarar yin wani abu a kan hakan.
Ita da abokanta da malamai da sauransu sai suka fara kiran kansu da suna Ghashforing (Grasshoppers) inda suke kai rahoton auren wuri da aka yi wa kananan yara wajen 'yan sanda. Yanzu tana jami'a, amma aikin Choya tare da sauran abokan aikinta a Grashforing bai tsaya ba, sannan ta horar da wasu mambobin kungiyar. Zuwa yanzu sun dakatar da auren kananan yara 50.

Heidi Crowter, Birtaniya
Mai fafutikar kare hakkin nakasassu
Heidi Crowter ta kasance mai fafutikar sauya tunanin mutane kan mutane masu fama da cutar rashin iya tafiya wato Down Syndrome. Ta taba kai karar Gwamnatin Birtaniyya kara kotu domin yaki da dokar cewa za a iya zubar da cikin da aka gano yana dauke da wannan cutar, inda ta ce akwai nuna bambanci a cikin lamarin. sai dai Babbar kotu ta ki amincewa da bukatarta, inda kotun ta ce an yi dokar ce domin samar da daidato tsakanin jariran da iyayensu mata. A watan Nuwamba, Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da karar Crowter, sai dai ta ce ita da mutanenta za su cigaba da fafutikar, sannan za su tafi Kotun Koli.
Ita ce uwar kungiyar Positive About Down, kuma tana cikin wadanda suka assasa National Down Syndrome Policy Group. An wallafa littafinta mai suna I'm Just Heidi a watan Agustann bana.
"Burina shi ne mata masu ciki su samu gamsasshen bayani game da cutar Down Syndrome. Ina so mutane su fahimci yanayinmu, sannan su iyi rayuwa da mu a yadda muke."
Heidi Crowter

Sandya Eknaligoda, Sri Lanka
Mai fafutukar kare hakkin ɗan adam
Mai kare hakkin ɗan adam kuma mai fafutuka, Sandya Eknaligoa na taimaka wa uwaye da mata da dama a lokacin yaƙin basasar Sri Lanka. Mijinta Prageeth Eknaligoda, wanda shahararren ɗan jarida ne mai binciken ƙwaf kuma mai zanen barkwanci, ya ɓata a watan Janairun 2010. Babban mai sukar gwamnati ne ya kuma yi binciken ƙwaf da dama kan zarge-zargen cin zarafin yan awaren Tamil Tiger.
Tun bayan ɓatansa, matar tasa Sandya mai ƴaƴa biyu take neman a yi mata adalci. Ta zargi magpoya bayan Mahinda Rajapaksa, tsohon shugaban Sri Lanka, da hannu kan sace mijinta. An gano waɗanda suka aikata laifin an kuma wanke su tare da sakin su.
Ni mace ce da ke fafutuka a madadin sauran mutane a yayin kowace dama,ina shiga kowace fafutuka, tare da shawo kan duk wani ƙalubale ko da ana zagi da cin mutuncina da ɓata min suna, ta hanyar sadaukarwa da jajircewa.
Sandya Eknaligoda

Gohar Eshghi, Iran
Mai fafutikar kare hakkin fararen hula
Gohar Eshghi ta zama wata abar misali wajen kokari a Iran. Danta, Sattar Beheshti, dan jarida ne da ya mutu a tsare kusan sama da shekara 10 da suka wuce, kuma tun lokacin ne Eshghi take fafutikar kwato hakkinsa, inda take zargin Gwamnatin Iran da kashe shi.
Tana cikin kungiyar Iranian Complainants Mothers, inda suke kokarin neman an yi wa yaransu da aka kashe adalci. Tana zargin Shugaban Addinin Iran, Ayatollah Ali Khameni ne kai tsaye da mutuwar danta, kuma tana cikin wadanda suka sa hannu a wasikar da aka aika ana bukatarsa ya yi murabus a shekarar 2019. A zanga-zangar bana, bayan mutuwar Mahsa Amini, Eshghi ta cire kallabinta domin goyon bayan masu zanga-zangar.

Ceci Flores, Mexico
Yar gwagwarmaya
A shekarar 2015 ce 'yan bindiga suka dauke dan Ceci Flores mai suna Alejandro yana mai shekara 21. Bayan shekara hudu kuma sai aka sake sace mata wani dan mai suna Marco Antonio mai shekara 31. Flores ta ce tana fafutika ce domin kada ta mutu ba tare da ta gano abin da ya faru da yaranta ba.
Wadanda suka bace a kasar sun kai akalla mutum 100,000 a wani lamari da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana da "Bala'i babba" A karkashin jagorancin Flores, kungiyar Madres Busacadoras de Sonora collectiv (Sonora's Searching Mothers) sun samu nasarar gano sama yara 1,000 da suka bace a wasu kaburbura.

Geraldina Guerra Garces, Ecuador
Mai fafutukar yaƙi da kashe mata
Geraldina Guerra Garces wacce ta shafe fiye da shekara 17 tana kare batun ƴancin mata, tana aiki don kare matan da suka samu kansu a yanayi na cin zarafi a Ecuador. Ta ƙware wajen tattara bayanai don fito da yadda ake samun ƙaruwar kashe mata saboda jinsinsu.
Ita ce ta ƙirƙiri tsarin nan na Catographies of Memory Initiative, wanda yake samar da jerin lokutan da aka kashe mata saboda ƙyamar jinsinsu don dinga tunawa da su. Guerra tana bin diddigi da tsara bayanai ga ƙungiyoyin hana cin zarafin mata na Feminist Alliance da Latin American Network Against Gender Violence. Tana kuma wakiltar Cibiyar Aldea da ƙungiyar ƙasar da ke samarwa mata mafaka.
Idan ba a ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki kan kisan mata saboda ƙyamar jinsinsu ba, babu wanda zai samu ci gaba. Duk da sabbin dokokin da ake samarwa, har yanzu kashe mu ake yi, don haka dole a sauya hakan.
Geraldina Guerra Garces

Mouda Goba, Birtaniya
Mai fafutikar kare hakkin 'yan madido da luwadi
A matsayinta na 'yar gudun hijira, Mouda Goba ta yi aiki na sama da shekara 20 da kananan kungiyoyi domin samar wa 'yan gudun hijira mazauni. Yanzu haka ita ce Manajar kungiyar Micro Rainbow, wadda ke aiki domin samar da mazauni ga masu madigo da luwadi da masu neman mafakar siyasa da 'yan gudun hijira. Ita ce take jagorantar shirinsu na samar da gidaje, inda yanzu haka sun zaunar da marasa gida 25,000, kuma suna nema musu aikin yi.
A kwana-kwanan nan, Goba ta samu damar saukar bakin masu madigo da luwadi da suka shiga Birtaniya daga Afghanistan. Tana cikin wadanda suka assasa kungiyar UK Black Pride, inda take rike da matsayin darakta a kwamitin amintattun kungiyar.

Gehad Hamdy, Masar
Likitar hakuri kuma mai taimakon al'umma
Likitar hakuri, Gehad Hamdy ce ta assasa kungiyar Speak Up, wadda kungiya ce a Masar mai kare hakkin mata da ke amfani da kafofin sadarwa domin fallasa masu cin zarafin mata. An samu matsalolin cin zarafin mata a kasar Masar da dama a shekarar 2022, wanda hakan ya kara fito da lamarin fili.
Kungiyar tana karfafa gwiwar mata da su fito fili su bayyana cin zarafinsu da aka yi, tare da daukar dawainiyar shara'ar matan da kuma tursasa gwamnati ta dauki mataki. Gangamin Hamdy ya siga bangarorin kasar da dama, inda ya lashe kyautar neman daidaito da daina nuna bambanci a World Justice Forum 2022.
"Har yanzu akwai sauran aiki a gaba; ba mu ko kusa da karshen ba. Kai yanzu ma muka fara."
Gehad Hamdy

Judith Heumann, Amurka
Mai kare hakkin nakasassu
Judith Heumann ta sadaukar da rayuwarta ne wajen kwato wa nakasassu hakki. Bayan ta kamu da cutar Polio tana karama, sai ta zama malamar makaranta ta farko mai koyarwa a zaune a keken guragu a birnin New York.
Fitacciyar jagorar kwato wa nakassasu hakki ce a duniya. Fafutikarta, ciki har da shiga cikin zama dirshen mafi tsawo da aka wa Gwamnatin Amurka ya sa ta shiga wadanda suka kawo sauyi mai muhimmanci. Heumann ta yi aiki a gwamnatin Clinton da Obama, sannan ta yi aikin kungiyoyi na sama da shekara 20.

Mai fafutikar kare hakkin nakasassu da ta shiga cikin Mata 100 na BBC na shekarar 2020, Shani Dhanda ce ta bayar da sunanta.
"Gaskiya ina samun karin karfin gwiwa matuka daga Judith, wadda a sama da shekara 30 take aiki domin kwato hakkin nakasassu a duniya. Ta kasance wadda ba ta gajiyawa wajen kwato hakkin nakasassu."

Jebina Yasmin Islam, Birtaniya
Yar zanga-zanga
Yar uwa ce ga malamar firamare Sabina Nessa da aka kashe a wani dandalin Landan a Satumban 2021, inda Jebina Yasmin ta zama mai yawan magana a kan hakkin mata a Birtaniya. Tana magana a kan sauya dokoki, inda take bukatar wanda ake zargi su rika bayyana a gaban kotu domin amsa laifinsu.
Bayan an kashe 'yar uwarta, Islam ta soki Gwamnatin Birtaniya da rashin nuna goyon baya gare su, inda ta ce hakan ya nuna yadda ba a cika damuwa da rikicin da maza suka jawo ba. Sannan ta yi magana a kan nuna bambancin launin fata-inda ta ce da a ce 'yan asalin Birtaniya ne kuma fararen fata, da sun samu ingantacciyar kula a asibiti". Islam ta ce 'yar uwarta "abar koyi wadda ba ta da tsoro."
"Ka so kanka sama da yadda kake son kowa a duniyar nan."
Sabina Nessa
Wani sako daga rubutun Sabina Nessa da 'yar uwarta Jebina ta aiko,

Layli, Iran
Yar zanga-zanga
Daya daga cikin hotunan da ake yadawa na znga-zanga a Iran shi ne na wata matashiya da ta tattara gashinta ta fito da shi fili domin cigaba da zanga-zangarta a tituna. Hotonta sai ya zama alamar jajircewa ga 'yan zanga-zanga. Sai dai da farko ganin hotonta din, an yi tsammanin hoton Hadis Najafi ne, wadda wata 'yar shekara 22 da aka kashe a lokacin zanga-zangar.
Da take magana da BBC Pashiya, Layli (Ba asalin sunanta ba ne) ta ce, "Dole mu kwato wa mutane irinsu Hadis Najafi da Mahsa Amini hakkinsu." A game da Gwamnatin Iran kuwa cewa ta yi "Ku daina mana barazanar kisa. Muna da yakinin 'yantar da mutanen Iran."

Hadizatou Mani, Jamhuriyar Nijar
Mai yaki da bauta
An sayar da ita ne domin zama mata ta biyar tana da shekara 12 a karkashin al'adar Wahaya, inda attajiri ke daukar mace domin ta rika bauta ga matansa hudu. Bayan an sako ta a shekarar 2005, sai ta sake aure, amma sai tsohon ubangidanta ya kai kararta cewa ta yi aure a kan aure, wanda hakan ya sa aka daure ta na wata shida a gidan yari.
Sai Mani ta daukaka kara zuwa Kotun Kolin Jamhuriyar Nijar, inda aka wanke ta daga aikata laifi a shekarar 2019, sannan kotu ta hana al'adar wahaya. Yanzu tana cikin masu fafutikar hana bauta, sannan take amfani da kungiyarta wajen ceto matan da suke cikin irin wannan halin.

Oleksandra Matviichuk, Ukraine
Lauyar kare hakkin dan Adam
A shekara 15 da suka gabata, Oleksandra Matviichuk ce ke jagorantar Cibiyar Center for Vivil Liberties (CCL), wadda ta yi lambar yabon zaman lafiya ta Nobel ta 2022 tare da wata kungiyar bisa aikinsu na tattara bayanan yakin Rasha a Ukraine.
Cibiyar CCL tana aiki ne irin na Ukraininan dissidents na 1960s, inda take mayar da hankali kan hakkin dan Adam. Cibiyar ce kungiyar kare hakkin dan Adam ta farko da ta je Crimea da Luhansk da Donetsk domin tattara bayanan yaki. Yanzu tana kira ga kotun musamman a kan ta bincika kasar Rasha a kan zargin tauye hakkin dan Adam a Checheniya da Moldova da Georgia d Syria da Mali da Ukraine.
"Karfin zuciya ba shi da jinsi."
Oleksandra Matviichuk

Narges Mohammadi, Iran
Mai fafutikar kare hakkin dan Adam
Narges Mohammadi 'yar jarida ce kuma ta kasance wadda aka sa sunanta cikin jerin wadanda aka zaba domin karramawar Nobel ta zaman lafiya, kuma ita ce Mataimakiyar Shugabar Cibiyar kare hakkin dan Adam ta Defenders of Human Rights Center, sannan tana aiki ba dare ba rana domin fafutikar ganin an daina yanke hukuncin kisa kan masu zanga-zanga. A zanga-zangar da aka gudakar kwanan nan a Iran, ta aiko da sako daga gidan yarin Evin, inda a ciki ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da Gwamnatin Iran daga yanke hukuncin kisa ga masu zanga-zanga.
A shekarar 2010 ce aka yanke wa Mohammadi hukuncin shekara 11 a gidan yari-daga baya aka mayar da shi shekara 16 bayan ta halarci wani taro a lokacin da aka bayar da belinta, inda a taron ta soki yadda 'yan fursunan suke cikin kunci a gidan yarin Evin. Wani shiri na musamman da ta yi mai suna White Tortures ya yi bayani ne a kan yadda 'yan fursunan suke cikin kunci bayan tattaunawa da ta yi da tsofaffin 'yan gidan yari 16. Yanzu haka yaranta biyu da mijinta wanda shi ma dan gwagwarmaya ne suna zaune a wata kasar ce domin samun mafaka.

Tamana Zaryab Paryani, Afghanistan
Yar gwagwarmaya
Kwanaki kadan bayan shiga cikin gangamin samar da 'yancin karatu da aiki ga mata a watan Janairu, sai aka ga 'yan bindiga sun zo sun kama Tamana Zaryab Paryani da 'yan uwanta a gidansu. A daidai lokacin da duniya ta fara Allah wadai da kama su, sai Gwamnatin Afghanistan ta karyata zargin hannu a kamen.
Sai dai ta samu damar nadar bidiyon lokacin da ake kama su din, ta saka a yanar gizo, bidiyon da ya jawo hankalin mata masu fafutika. Ta kwashe mako uku a tsare kafin aka sake ta. Yanzu tana zaune a Jamus, sannan domin nuna goyon baya ga matan Iran, ita ma ta kona kallabinta, lamarin da matan Afghanistan da dama suke wa kallon rashin kyautatawa.
"A lokacin da matan duniya suke cigaba, matan Afghanistan sai ake mayar da su baya da kimanin shekara 20. Sun bata cigaban da aka samu na shekara kusan 20."
Tamana Zaryab Paryani

Alice Pataxo, Brazil
Yar gwagwarmaya
Mai fafutikar samar da yanayi mai kyau ce, kuma 'yar jarida. Alice Pataxo tana da burin wayar da kan mutane a kan wasu dokokin Gwamnatin Brazil na baya-bayan nan a kan noma da muhalli suka barazana ga hakkin filayen mutane. A matsayinta na muryar mutanen yankinta, tana da burin kalubalantar tsarin da game da asalin mutanen yanki da kuma bayyana yadda aka kashe masu fafutikar samar da muhalli mai kyau.
Yar jarida ce a Colabora da take amfani da manhajar YouTube a tasharta ta Nuhe, kalmar da ke nufin hakuri da juriyar mutanen Brazil wajen yada labaranta.

Mai fafutikar ilimin yara da mata Malala Yousafzai, wadda ta kasance cikin mata 100 na BBC na 2021 ce ta bayar da sunanta.
"Ina matukar alfahari da bayar da sunan Alice Pataxo domin shiga cikin Mata 100 na BBC na 2022, Kokarin Alice wajen yaki da gurbacewar muhalli da samar da daidaito da 'yan asalin mutanen gari na ba ni kwarin gwiwar cewa an kusa kai wa lokacin da da za a samu daidaito a duniya."

Roya Piraei, Iran
Yar gwagwarmaya
A watan Satumba ne hoton Roya Piraei ya karade kafofin sadarwa. Mahaifiyarta Minoo Majidi mai shekara 62 ta dade tana zanga-zanga a Kermanshah, wanda shi ne birni mafi girma da ake amfani da harshen Kurdish, kuma a wajen zanga-zangar aka kashe ta. Piraei ta dauki hoto ne a gaban kabarin mahaifiyar da kashin kanta a aske tana rike da gashin a hannunta tana nuna wa kyamara.
Ta zama daya daga cikin wadanda duniya ta haska a bangaren masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Iran bayan mutuwar Mahsa Amini. Piraei ta samu ganawa da Shugaban Kasar Faransa, Emmanuel Macron domin samun tallafin kasashen waje domin cigaba da zanga-zangar.

Yuliia Sachuk, Ukraine
Jagorar nakasassu
Yuliia Sachuk jagorar kare hakkin dan Adam ce a kasar Ukraine, ind take shugabantar kungiyar Fight for Right, wadda kungiya ce ta mata masu bukata ta musamman. Ta assasa aikin ceton gaggawa tun bayan fara yakin Ukraine, inda suke aiki ba dare ba rana tare da kungiyoyin duniya domin kai dauki ga dubban nakasassun kasar Ukraine.
Sachuk tana da sha'awar taimakon mata masu nakasa domin su shiga a dama da su a siyasa. Ta halarci horon Leader Europe na Gidaunar Obama, sannan ta lashe kyautar National Huma Rights Award na 2020, sannan tana cikin kwamitin Ukraine na hakkin nakasassu a Majalisar Dinkin Duniya.

Suvada Selimovic, Bosnia and Herzegovina
Mai fafutikar samar da zaman lafiiya
Yanzu shekara 30 ke nan yakin ya daidaita kasar Bosnia and Herzengovina, wanda hakan ya sa Suvada Selimovis take zaune tare da mutane a kauyen da suka sake ginawa tare da sauran 'yan gudun hijira, wadanda suka dawo gida ba tare da maza ba, sannan an barsu da yara kanana. Hakan ya sa Selimovic ta assasa kungiyar Anima domin samar da zaman lafiya da karfafa gwiwar mata.
Bayan an gano gawar mijinta a wani babban kabari a shekarar 2008, sai ta bayyana a gaban kotun laifukan yaki inda ta yi bayani, sannan ta bukaci sauran matan su yi hakan. Yanzu Anima na shirya tarukan kara wa juna sani ga mata da suka shiga damuwa saboda yaki sannan kungiyar na ba mata damar sayar da kayayyakin da suka hada.

Efrat Tilma, Isra'il
Mai aikin sa kai
Kasancewarta ta farko da ta sauya jinsi cikin 'yan sandan sa kai a Israel, Efrat Tilman tana amsa wayoyin neman daukin gaggawa sannan tana kokarin inganta alaka tsakanin 'yan sanda da masu madigo da luwadi. Tilma ta gudu daga Israel tana karama ta koma Turai-bayan iyayenta sun guje ta da kuma cin zarafin 'yan sanda. Sai ta yi tiyatar sauya jinsi a shekarar 1969 a Casablanca, lokacin da aka hana tiyatar a kasashen Turai da dama.
Sai ta zama ma'aikaciyar jirgi a Berlin, har ta yi aure. A shekarar 2005 ce ta dawo Israel bayan mijinta ya sake ta, inda ta samu kasar ta sauya wajen nuna bambancin jinsi, wanda hakan ya sa ta shiga aikin dan sandan sa kai.

Zhou Xiaouan, China
Mai kare hakkin mata
A matsayinta ta fuskar MeToo a China, Zhou Xiaoxuan ta kasance abar koyi ga mata masu kare hakkin mata a China da duniya. A shekarar 2018 ce ta kai karar Zhu Jun, wadda babban mai gabatar da shirye-shirye ne a tashar talabijin na gwamnati na CCTV, inda ta zarge shi sumbatarta a lokacin da yake ba su horo a shekarar 2014, zargin da ya karyata, shi kuma ya kai kararta ta bata suna.
An kori kararta ne bisa rashin isasshen shaida, sannan a bana aka sake korar daukaka karar, a wani lamari da gidajen jaridun kasashen waje suka bayyana da wani kalubale ga shirin MeToo a China. Zhou Xiaoxuan yanzu ta fi tallafawa mata da aka ci zarafinsu sannan tana wayar da kan mata kan kare hakkinsu a China.

Mace mai aske gashinta, Iran
Mai zanga-zanga
A bana ne aka yi wata zanga-zanga mai zafi a Iran bayan an kashe Mahsa Amini, wadda 'yar Tehran ce mai shekara 22 da 'yan sanda suka kama a 13 ga Satumba bisa zargin karya dokar Iran ta tislasta sanya mayafi ko dankwali.
A bana muna so mu karrama matan da suka taka muhimmiyar rawa a zanga-zanga, inda suke kokarin kwato 'yancinsu bisa dokar tilasta su sanya hijabi.
Aske gashin da ta yi sai ya zama wata alama da ta bazu zuwa fitattun mutane da 'yan siyasa a duniya. Ana kallon hakan a matsayin nuna alhini a Iran.
Lafiya da Kimiyya

Aye Nyein Thu, Myanmar
Likitar zuciya
Aye Nyein Thu likita ce da ke gaba-gaba wajen jinyar marasa lafiya a yankunan kasar Myanmar da ke fama da rikce-rikice, musamman kauyukan Jihar Chin. Ta gina karamin asibiti da karamin wajen tiyata a Nuwamban shekarar 2021, inda take jinyar marasa lafiya.
A lokacin da ba ta da aiki, takan tafi wasu yankunan da suma suke fama da karancin likitoci domin taimakon marasa lafiya ciki har da masu gudun hijira. A aikin da take yi, ta taba shiga zargin Rundunar Sojin Myanmar cewa tana ingiza mutane su yi bore, da kuma zarhin taimakon kungiyoyin adawa da gwamnati da ake kira People Defence Forces.

Sirisha Bandla, Indiya
Injiniyar jirgin sama
Sirisha Bandla ta je karshen duniyar wata a tafiyar mai mai dimbin tarihi ta Unitty 22 mission ta 2021, wanda shi ne zuwa duniyar wata na farko na Kamfanin Virgin Galactic, inda ta zama 'yar Indiya ta biyu da suka je duniyar wata.
Bandla ta fara sha'awar zuwa duniyar wata ne tun tana karama, wanda hakan ya sa ta karanci Injiniyancin jirgin sama a Amurka, inda yanzu haka ita ce Mataimakiyar Shugabar Harkokin Gwamnati da Bincike na Kamfanin Virgin Galactic, matsayin da ya kunshi aiki da abokan hulda na kimiyya da fasaha masu sha'awar zuwa duniyar watan.

Jaruma Sunny Leone da take cikin Mata 100 na BBC na 2016 ce ta bayar da sunanta.
"A wani bangare da maza suka fi yawa, yadda Sirisha ta shiga har ta kai matsayin da take, ya nuna kwazonta, sannan kokarinta yake ban sha'awa, sannan na san zai kayatar da 'yan mata masu irin tunaninta."

Victoria Baptiste, Amurka
Nas
Victoria Baptiste nas ce a Jihar Maryland ta Amurka, inda take ilimantar da mutane game da rigakafi. Ta fahimci dalilin da ya sa bakaken fata ke kin yin allurar rigakafi, kasancewar ta fito ne daga dangin Henrieatta Lacks, wadda bakar mata ce da kansar mahaifa ta kashe a shekarar 1951, wadda tantanin halittarta da aka dauka ba tare da saninta yana cikin na farko da aka dauko domin bincike.
An fi sanin tantanin halittarsu da aka dauko din da HeLa cells, kuma ana amfani da su domin bincike a banaren kiwon lafiya tun wancan lokacin, amma iyalansu ba su sani ba. Yanzu Baptiste tana cikin Gidauniyar Henrietta Lacks kuma Ambasada ce ta WHO wajen yaki da cutar kansar mahaifa.

Niloufar Bayani, Iran
Mai binciken dangatakar halittu da muhalli
Mai fafutukar kare muhalli Niloufar Bayani na ɗaya daga cikin masu kare muhallin da aka tsare a Iran a 2018, bayan da suka yi amfani da kyamarori wajen gano halittun da ke barazanar ɓacewa. An zarge su da tattara bayanan sirrin gwamnati a kan wurare masu matuƙar muhimmanci da gwamnati ke taka tsan-tsan da su, inda aka yanke wa Bayani hukuncin ɗaurin shekara 10 a gidan yari.
Bayani ce manajar tsare-tsare a cibiyar kula da namun daji ta Persian Wildlife Heritage, wacce aka kafa don ceto damusa irin wacce ake samu a yankin Asiya. A wani bayani da sashen Persia na BBC ya samu, ta ce Dakarun Juyin Juya Hali na Jamhuriyar Musulunci ta Iran ne suka jawo ta shiga yanayi na tsananin damuwa da ya taɓa lafiyar hankalinta saboda azabtar da ita da suka yi da barazanar cin zarafinta na a ƙalla awa 1,200. Sai dai hukumomin Iran sun ƙaryata zarge-zargen.

Sandy Cabrera Arteaga, Honduras
Mai fafutuka kan kare ƴancin lafiyar mata
Ɗalibar falsafa, marubuciya kuma mai rajin kare hakkin mata, Sandy Cabrera Arteaga mai kare hakkokin mata ce kan abin da ya shafi ƴancinsu na haihuwa da zubar da ciki da matantakarsu. Tana koyar da mutane batutuwan da suka shafi maganin da ake sha don wanke mara bayan saduwa don gudun ɗaukar ciki, kuma ita ce mai magana da yawun wata ƙungiya ta 'Hablemos lo que es' - mai wayar da kan mutane kan magungunan wanke mara.
Tana kuma aiki da ƙungiyar Accion Joven wato ta fafutukar matasa, wacce ke mayar da hankali kan rayuwar matasa da hakkokin abin da ya shafi haihuwa da zubar da jiki. Ta iya yaren Honduran na maganar kurame sosai, a matsayinta na ƴa ɗaya tilo ga mahaifiyarta wacce kurma ce, tana alfahari da yadda aka ene ta.

Samrawit Fikru, Habasha
Masaniyar kwamfuta
Duk da cewa ba ta fara amfani da kwamfuta ba sai da ta kai shekara 17, Samrawit Fikru ce ta assasa Kamfanin Hybrid Design, wanda ya kasance daya daga cikin kamfanonin da suka kirkira mahajar karbar haraji a kasar Habasha ta RIDE.
Yadda take shiga yanayin rashin natsuwa lokacin hawa tasi da kuma yadda direbobi ke kara mata kudin mota ne ya sa ta kirkiri manhajar, wadda ta fara da kudi kasa da Dala 2,000 (kimanin Fam 1,700). Kamfaninta yanzu haka ya fi daukar mata aiki. Babu mata da yawa a bangaren harkokin kwamfuta a Habasha, wanda hakan ya sa Fikru ke kokarin karfafa gwiwar mata masu tasowa da su shiga harkar.
"Kasuwancin da mata ke jagoranta suna kara yawa; yanzu muna bukatar karin 'yan mata su rika samun tallafin kudade domin kai wa ga bantensu wajen bayyana fasaharsu."
Samrawit Fikru

Wegahta Gebreyohannes Abera, Tigray, Habasha
Ma'aikaciyar jin kai
Wegahta Gebreyohannes Abera ma'aikaciyar jinya ce da ta kirkiri kungiyar Hdrina domin yaki da rashin abincin masu gina jiki a yankin Tiagray da aka yi yaki. Hdrina na da wasu shirye-shirye da suka gudanar domin taimakon mata da kananan yara, ciki har da ciyarwar gaggawa a sansanonin gudun hijira da kauyuka,
Kungiyar tana kuma gudanar da shirin tallafawa mata ga matan da aka ci zarafinsu a yaki, da kuma matan da talauci sanadiyar yaki ya tursasa su shiga karuwanci.

Dilek Gursoy, Jamus
Likitar zuciya
Dokta Dilek Gursoy 'yar asalin kasar Turkiyya ce da aka haifa a kasar Jamus, wadda yanzu haka tana cikin manyan likitocin zuciya. Jaridar Forbes ta taba yin babban labarintaa game da ita a Jamus, inda labarin ya mayar da hankali a kan kasancewarta likita ta farko da ta yi dashen zuciyar roba a Turai.
Ta kasance gaba-gaba wajen dashen zuciyar roba na sama da shekara 10 da suka gabata, inda suka aiki domin samar da wata hanyar dashen zuciya ba tare da dasa ainihin zuciyar ba duba da yadda ake wahalar samon masu bayar da zuciyar. Ta rubuta littafin tarihin rayuwarta, kuma yanzu haka kana shirin bude asibitinta.

Sofia Henonen, Ajantina
Mai fafutikar kula da muhalli
Tana aiki ne domin kiyaye lalacewar yanayi. Sofia Henonen ce ta jagoranci yunkurin farko na yaki da bacewar wasu dabbobi da tsirrai a yankin Kudancin Amurka ta hanyar sake hada tafkin Esteros del Ibera, wanda shi ne babban tafkin Ajantina kuma daya daga cikin manya a duniya. Ta kwashe akalla shekara 30 tana bayar da gudunmuwa wajen dawo da gurare masu muhimmanci.
A karkashin jagorancinta. an sake hada wasu muhimman tafki a yankunan Ajantina guda hudu wanda ya hada Patagonian steppe, inda suka mayara da yankin ya zama wajen shakatawa, sannan suka shuka wasu tsirrai na da domin gyara wajen da jawo masu shakatawa.

Kimiko Hirata, Japan
Mai fafutuka kan sauyin yanayi
Wata babbar mai adawa da amfani da makamashin gawayi, Kimiko Hirata ta shafe kusan rabin rayuwarta tana yaƙi da ganin Japan ta daina dogaro da makamashi masu ɓata muhalli - waɗanda su suka fi taka rawa sosai wajen gurɓata muhalli. Fafutukar da take yi a yankunan da take sun ta jawo an soke wasu shirin samar da cibiyoyin makamashi na gawayi 17 da aka yi niyyar kafawa. Ita ce ƴar Japan ta farko da ta samu kyautar karramawa a fagen kyautata muhalli ta Goldman.
Hirata ta bar aikinta a wani kamfanin ɗab'i don zama mai faftukar sauyin yanaui a shekarun 1990 bayan da ta karanta wani littafi na Al Gore mai suna Earth in the Balance. A yanzu ita ce babbar darakta ta wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna Climate Integrate, da aka ƙirƙira a watan janairun 2022, wacce take magance matsalar rage hayaƙin carbon.

Judy Kihumba, Kenya
Tafintar kurame
A matsayinta ta mai fafutikar kula da lafiyar kwakwalwa da kula da kurame, Judy Kihumba tana shiga tsakani domin tabbatar da ilimin kiwon lafiya yana kai wa ga dukkan mata lokacin da ta gane cewa asibitoci da dama a Kenya ba sa da tafintar kurame.
Ita ce ta kirkiri Talking Hands, Listening Eyes on Postpartum Depression (THLEP), inda take taimakon mata masu fama da matsalar ji. Kihumba ta assasa kungiyar ce bayan ta lura da yadda mata suke shiga damuwa bayan haihuwa, wanda ita ma yi fama da shi a shekarar 2019. A bana, sun shirya taron baje kolin jarirai, inda aka tara iyaye mata kurame 78 suka tattauna da masana kiwon lafiya.

Marie Christina Kolo, Madagascar
Mai bincike kan sauyin yanayi
Marie Christina Kolo mai fafutikar magance matsalolin al'umma da yaki da gurbacewar muhalli ce da ta kasance cikin tawagar kasar Madagascar da suka halarci taron COP27. Ta kasance mai kare hakkin dan Adam da sauyin yanayi kasancewar kasarta ta sha fama da fari ta jawo karancin abinci. Ita kanta Majalisar Dinkin Duniya ta ce wannan yunwar ita ce ra farko da sauyin yanayi ya jawo.
Kolo darakta yanki ce a Gidauniyar People Power Inclusion, wadda ke kokarin yaki da talauci ta hanyar inganta tattalin arziki ta bangaren samar da yanayi mai kyau. Kungiyarta ta Green'N'Kool na cikin kungiyoyin duniya masu fafutikar yaki da sauyin yanayi da ake ji da su. Haka kuma kasancewarta wadda ta fuskanci cin zarafin bambancin jinsi, sai ta assasa kungiyar Women Break the Silence, wadda ke yaki da fyade.
"Ba ma so ana mana kallon wadanda suka rasa yadda za su yi saboda gurbacewar muhalli, ina da yakini sannan ina cike da alfahari a duk lokacin da na ga mata suna nuna kwazo duk rintsi duk wahala"
Marie Christina Kolo

Iryna Kondratova, Ukraine
Likitar yara
Duk da cewa sun fuskanci harin bama-bamai, Dokta Iryna Kondratova da ma'aikatanta sun cigaba da aikin taimakon mata masu juna biyu da jarirai da iyayensu mata a asibitin mata na yankin Kharkiv. Sun assasa dakin karbar haihuwa a karkashin asibitin, sannan suka sadaukar rayuwarsu wajen rainon jariran da aka haifa da ba za su iya fitar da su ba, duk da jefa bama-bamai da ake yi a garin.
A matsayinta na shugabar cibiyar, Dokta Kondratova ta karbi shafin Instagram na David Beckham a watan Maris, inda ta bayyana kalubalen da suka fuskanta. Ma'aikatanta sun taimaka wajen bayar da tallafin maganin damuwa ga sama da mata 3,000 daga yankin Luhansk da Donetsk tun daga shekarar 2014.
"Gidajanmu aka tarwatsa da hanyoyinmu da asibitocinmu- da kuma rayuwarmu. Amma da manufarmu da burukanmu suna nan da karfinsu,"
Iryna Kondratova

Asonele Kotu, Afirka ta Kudu
Masaniyar kwamfuta
Asonele Kotu ta fara tunanin kasuwancinta ne bayan ta so a cire mata kariyar daukar ciki, amma ta rasa wanda zai cire mata. Hakan ya sa ta kirkiri FemConnect domin samar da fasahar rage rashin ingantacciyar hanyar kula da ala'ada da rage daukar cikin kananan yara.
Manhajar tana bayar da dama ga mata su samu shawarwari a kan maganin da suka shafi saduwa da haihuwa ba tare da wata tsangwama ba da kuma magungunan hana daukar ciki masu inganci-sannan tana sayar da abinci ta yanar gizo. Kotu tana burin samar da audugar al'ada tare da samar da hanyoyin samar da ingantacciyar lafiya, musamman ga matasa da garuruwan da ba a cika kula da su ba.
"Ina shiga farin cikin ganin matasa masu sha'awar kawo sauyi da magance matsaloli domin tabbatar da cewa masu tasowa ba su fuskanci matsalolin ba."
Asonele Kotu

Erika Liriano, Jamhuriyar Dominican
Yar kasuwar koko
Erika Liriano ta assasa kamfanin sarrafawa da kasuwancin koko a Jamhuriyar Dominican domin inganta kasuwancinsa. Sunan kamfanin INARU, wanda ta bude tare da 'yar uwarta, Janett da burin ganin sarrafawa da kasuwancinsa ya inganta. A bana ne kasuwancinsu na samu tallafin iri.
A tarihi, kasuwancin koko an bar shi ne kawai ga kananan 'yan kasuwa, amma kamfaninsu ya fadada harkar. An haife su a birnin New York ne, amma sun yi gadon noma da kasuwanci ne a Jamhuriyar Dominican. Yanzu haka suna hada hannu da mata masu noma da kungiyoyi a kasar.
"Dagewa wajen aiwatar da abin da mutum ke sha'awa abu ne da ya kamata kowa ya horar da kan shi a kai, wannan ya kunshi a bar mata su zabi duk abin da suke son zama a rayuwa."
Erika Liriano

Naja Lyberth, Greenland
Masaniyar halayyar dan Adam
Likitar damuwa, Naja Lyberth tana 'yar shekara 13 ne aka saka ta a na'urar intrauterine device da ake kira da (IUD) a wani shirin likitocin Denmark na rage yawan haihuwa a shekarun 1960 zuwa 1970. A bana ne Gwamnatin kasar Denmark da ta Greenland suka amince domin bincikar wannan lamarin, wanda ake tunani ya shafi mata da 'yan mata 4,500.
Lyberth ta kuduri aniyar taimakon wadannan matan, musamman wadanda suke zargin sanya su a na'urar da haifar musu da rashin haihuwa. Tuni ta kirkiri dandalin a Facebook domin matan da suka fuskanci hakan su taru suna taimakon juna.
Mata da dama da suka fuskanci wannan matsalar suna zama ababen koyi da mata masu tasowa. Fitowa fili ana magana yana taimaka wa masu tasowa wajen cire tsoro, musamman sanya musu tunanin babu abin da zai faru. Bai kamata tsoro ya hana mu magana ba.
Naja Lyberth

Nigar Marf, Iraq
Nas
Nigar Marf ta kasance babbar nas a bangaren kuna a Kurdistan na Iraq, inda take aiki wajen jinyar mata da suka kona kansu. Wannan al'ada ta kona kai fitacciya ce a yankin a matsayin wata hanya ta nuna rashin amincewa da wani abu.
Marf ta yi kusan shekara 25 tana aikin asibiti a bangaren kula da yara masu kuna da bangaren jinya na musamman. A bangarenta, takan kuma yi jinyar wadanda suka kone ba da gangan ba. Yawancin matan da musu jinya sun yi fama da cin zarafi ne da ya sa suka kona kansu, wasu kanana ne da ba su wuce shekara 16.

Monica Musonda, Zambiya
Yar kasuwa
Monica Musonda lauya ce da ta rikide ta zama 'yar kasuwa, inda ta assasa kamfanin Java Foods da take jagoranta, inda suke sarrafa abinci irinsu indomie a kasar. Burinta shi ne ta samar da abinci ta hanyar amfani da noman alkama da ake yi a Zambia, da kuma kokarinta na sauya yanayin cimakan kasar.
Musonda, wadda mai fafutikar cimaka mai kyau ce, ta horar da mata da dama harkokin kasuwanci, sannan takan yi magana a kan abubuwan da suka shafi mata. Ta samu kyaututtukan karramawa da dama, sannan kuma ayyukanta na inganta harkokin noman Afirka sun samu yabo.

Ifeoma Ozoma, Amurka
Masaniyar kwamfuta
Bayan ta karya dokar rashin fitar da bayani ta non-disclosure agreement (NDA), inda ta zargi tsohon ubangidanta Pinteres da nuna bambancin launin fata da jinsi, sai Ifeoma Ozoma ta kuduri aniyar taimakon ma'aikata wajen yaki da wannan al'adar a wajen aiki. Tana cikin wadanda suka dauki nauyin kudurin Silence No More, wanda zai ba ma'aikata a California damar fitar da bayaninsu game da nuna bambancin launin fata da cin zarafi ko da kuwa sun sa hannu a yarjejeniyar NDA. Pinterest ya sauya wasu abubuwa a ma'aikatansa bayan wannan zargin na Ifeoma, sannan ya bayyan goyon bayansa kan kudirinsu.
Haka Ozoma ce ta kirkiri Tech Worker Handbook, inda ta tattara bayanan da za su taimakawa ma'aikata wajen bayyana halin da suke ciki-sannan ta kirkiri Earthseed, da ke ba ma'aikatu shawarar yadda za su samar da daidaito da adalci.

Yuliia Paievska, Ukraine
Ma'aikaciyar jinya
Yuliia Paievska kwararriyar ma'aikaciyar jinya ce bangaren wadanda suka samu raunuka, inda ta assasa sashen Taira's Angel domin taimakon daruruwan sojoji da fararen hula da suka samu raunuka. Yuliia da aka fi sani da Taira ta shiga hannun sojojin Rasha a watan Maris a lokacin da take aikin kwashe fararen hula a birnin Maiupol.
Ta kasance tana amfani da kyamarar jiki domin dauko rahoton yadda suke aiki, sannan ta ba gidajen jaridu bidiyoyin da ta nada. Bayan wata uku a tsare, sai aka sako ta, inda Paievska ta bayyana halin da ta shiga a lokacin da take tsare, halin da ta bayyana da "jahannama"

Jane Rigby, Amurka
Masaniyar ilimin sararin samaniya
Masaniyar sararin samaniya ce ta Hukumar NASA. Dr Jane Rigby ta yi bincike ne a kan yadda duniyoyi suka sauya bayan tsawon lokaci. Tana cikin masana kimiyya na duniya da suka assasa na'urar James Webb, wadda ita ce na'urar daukar hoton sararin samaniya mafi girma a duniya. A watan Yuli, hoton da na'urar ta Webb ta dauko ya kasance hoto mafi gamsasshen bayani game da duniya.
Rigby tana da wallafe-wallafe sama da 100 a mujallun kimiyya, ta sannan samu kyaututtuka da dama saboda bincike-binciken da ta yi. Kuma tana fafutikar samar da daidaito a bangaren kimiyya da fasaha da injiniyanci da lissafi wato STEM.
"A lokacin da nake daliba, ba ni da masaniya a kan ababen koyi daga 'yan madigo da luwadi. Watakila in kasancecikin mutanen da suka taso ba tare da wasu wadanda suka kallo a matsayin ababen koyi ba.
Jane Rigby

Ainura Sagyn, Krygyzstan
Injiniya
A matsayinta na Injiniyar Kwamfuta, kuma mai gwagwarmayar kwato hakkin mata, sannan shugabar kamfaninta. Ainura Sagyn tana amfani da fasaharta wajen kirkirar hanyoyin magance matsalolin muhalli. Ta kirkiri manhajar Tazar da ke hada masu zubar da shara daga gidaje da wajen cin abinci da kamfanoni da sauransu zuwa masu sarrafa bolan. Manhajar ta taimaka wajen rage bola, sannan ta taimaka wajen kawo cigaba a kasar.
Ta kuma shirya tarukan koyar da kwamfuta da kimiyya da fasaha da injiniyanci da lissafi wato STEM ga sama da mata 2,000 'yan makaranta a yankuna da dama a kasar ta Krygyzstan.
"Rashin shigar da mata cikin jagorancin a bangaren tsabtace muhalli a yanzu alama ce cewa da wahala a kai gasamun nasara a gaba."
Ainura Sagyn

Monica Simpson, Amurka
Mai fafutikar adalci wajen haihuwa
A matsayinta na Babbar Darakta ta SisterSong, wadda hadaka ce ta samar da adalci ga mata masu haihuwa a Kudancin Amurka, Monica Simpson tana mayar da hankali ne wajen samar da cin gashin kai wajen saduwa da haihuwa. Lamarinta ya fi fitowa fili a bana ne bayan Kotun Kolin Amurka ta yi watsi ta hukunci tsakanin Roe da Wade, inda aka soke hukuncin bayar da damar zubar da ciki a kasar.
Simpson mawakiya ce, inda take amfani da fasaharta wajen fafutika. Tana cikin daraktocin kungiyar Black Mamas Matter Allience, inda suke fafutikar kula da lafiyar kwakwalwar bakaken fata.

Maryna Viazovska, Ukraine
Masaniyar lissafi
A farkon shekarar nan ne ta lashe lambar yanon Field Medan ta lissafi, wanda ake kwatantawa da Karramawar Nobel ta lissafi kuma duk bayan shekara hudu ake bayar da kyautar. Maryna Viazovska ta lashe kyautar ce bayan aikinta na wani lissafi na shekara 400 da suka wuce.
Tana zaune ne a Swiss Federal Institute of Technology a Lausanne (EPFL), kuma farfesa ce a lissafi kuma tana cikin shugabannin Institute of Mathematics.

Yana Zinkevych, Ukraine
Yar siyasa kuma mai aikin jinyar sa kai
Kungiyar Hospitalles, kungiya ce ta 'yan sa kai karkashin jagorancin Yana Zinkevych da suke kokarin ceton yara da yakin Ukraine ya shafa. Suna aiki ne wajen cetowa tare da tseratar da mutane daga bakin daga. Zinkevych ta zama ma'aikaciyar sa kai ne bayan ta kammala karatu, sannan ta assasa kungiyar The Battalion a shekara 2014 a daidai lokacin da aka fara nuna wa Ukraine yatsa.
Da kanta da dauko sojoji 200 da suka samu raunuka a fagen daga, sannan ma'aikatanta suna bayar da agajin gaggawa ga sojojin da suka samu rauni da fararen hula, sannan tana gudanar da tarukan kara wa juna sani, tare da gudarar da ceto kusan 6,000. Mai shekara 27 din tana cikin kananan mambobi a Majalilsar Ukraine, kuma ita ce shugabar kwamitin magani na sojoji.

Mene ne mata 100?
Mata 100 na BBC na bayyana muhimman mata ababen koyi 100 ne a fadin duniya a duk shekara. Muna hada labarai na musamman da tattaunawa a kan rayuwarsu-Labaran da ke mayar da hankali a kan mata.
Ku bibbiya Mata 100 na BBC a shafin Instagram da Facebook da Twitter. Za ku iya shiga cikin tattaunawar ta hanyar amfani da #BBC100Women
Ta yaya ake zabo su?
Ana zabo mata 100 din ne daga jerin mutanen da kafar BBC na duniya ta ba alhakin tattarowa. Muna neman mace da ta yi fice a cikin wata 12 da suka gabata da kuma wadanda suke da labarin da za su bayar da zai kawo sauyi, ko kuma sun cimma wata nasara a rayuwa ko kuma suka sauya wata al'umma ko da kuwa ba a samu labarin ba. Sai kuma a zauna a taskace wadanda suka fi dacewa da taken karramawar ta bana-Cigaban da aka samu a bangarori da dama a shekara 10 da suka gabata.
Muna zakulo abubuwa ne da suka jawo ra'ayoyi mabambanta kamar hakkin hayayyafa, inda ci gaban wata kan iya zama ci bayan wata, sai mu zabo mata da suka kawo sauyi mai ma'ana, Haka kuma ana yin la'kari da da kowane yanki kafin fitar da jerin sunayen na karshe.
Wasu daga cikin matan an boye sunansu, wasu kuma an boye sunan iyayensu domin kare su da iyalansu bayan samun izininsu da kuma lura da ka'idojin aikin jarida na BBC.