Test Embed Page made with 10.4.7 generator and 10.0.8 embed wrapper
Click here for a list of include paths
Click here for a test page with no right hand side
Bayar da Hukumomin Masu Samarwa Cikin Saurin Samun Hanyar Komfuta Ta kowace hanya Indiya tana ba da dama ga Duniya a cikin Muhalli mai Kyawu Ta hanyar Kyautata Harkokin Shekarar Al'umma Ta Forex Don Officeirfafa Ofishi, Sakon Matsayinsa na Sanarwar
Bayanan abokantaka na rayuwa, ra'ayinsu, tattaunawa, tsari, kasuwa, da dai sauransu, manyan manufofin manufa iri ɗaya ne. An sanar da ƙaddamar da jagorar siye. Yanzu haka ba batun labarin narancin Ingilishi. Jaane Dishame Kungiyar Hadin gwiwar Lafiya Dole ne ta Duniya, amma
BBC ta bayyana jerin sunayen Mata fitattu da suka fi shahara su 100 daga sassan duniya na shekara ta 2023.
A cikinsu akwai lauyar kare haƙƙoƙin bil`adama Amal Clooney, da fitacciyar ƴar fim Ba'amurkiya Ferrera, da mai rajin kare mata Gloria Steinem, da matar tsohon shugaban Amurka Michelle Obama, da mamallakiyar wajen kasuwancin kayan ƙawa Huda Kattan, da Aitama Bonmati zakarar wadda ta lashe kyautar kwallo na Ballon d'Or.
A shekarar da ta kasance mai tsananin zafi, da gobarar daji, da ambaliya, da sauran bala'o'i da suka fi ƙarfin a ce mutum ya haddasa su, suke kankane kanun jaridu, jerin sunayen ya kuma taɓo mata da suke ta aiki tuƙuru wajen taimaka wa al'umominsu shawo kan matsala ta sauyin yanayi da ɗaukar matakan rage illarsa.
A cikin Matan 100 na BBC mun zayyana waɗanda su ne suka fara batu a kan yanayi su 28, tun kafin Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kan Sauyin Yanayi, COP28.
An jero sunayen ne ba tare da la'akari da wani tsari ba
Al`adu da Ilimi
Afroze-Numa, Pakistan/Fakistan
Mai kiwo
Ɗaya daga cikin makiyaya na Wakhi, Afroze-Numa tana kula da akuyoyi da shanu da tumaki tsawon shekaru 30.
Ta koyi sana`ar ta kiwo daga mahaifiyarta da kakarta, wani ɓangare ne na tsohuwar al`ada da a yanzun take shuɗewa a kwarin Shimshal valley da ke Pakistan.
A kowacce shekara, wanannan makiyaya suna yawon kiwo da dabbobin nasu a wuraren kiwo da ke mita 4,800 sama da teku inda suke sarrafa kayayyakin madara/nonon shanu domin sayarwa, a lokacin da dabbobinsu suke cin abinci.
Abubuwan da suke samu sun sa kauyen ya bunnasa da ba su damar bai wa `ya`yansu ilimi har yanzun Afroze-Numa tana tuna cewa ita ce mace ta farko a tudun nasu da take da takalmi.
Hosai Ahmadzai, Afganistan
Mai gabatarwa a gidan talabijin
Lokacin da Taliban suka karbe iko da Afganistan a watan Agustan 2021, Hosai Ahmadzai tana daya daga cikin 'yan tsirarun mata da ke ci gaba da yaɗa labarai a kasar.
Ta ci gaba da aikinta a gidan talabijin Shamshad duk da matsalolin tsaro da tsayin daka da ake yi wa mata a kafafen yada labarai.
Tun lokacin da ta yi hira da jami'an Taliban da dama, amma an ƙayade mata irin abubuwan da za ta iya tambayarsu saboda haka ba ta iya yin tambaya game da abubuwan da suke yi.
Ahmadzai ta kware a fannin shari'a da harkar siyasa kuma ta shafe shekaru bakwai tana aikin yaɗa labarai. Ta mayar da hankali ne kan ilimin 'ya'ya mata, wanda 'yan Taliban suka takura musu sosai.
Esi Buobasa, Ghana
Mai sana`ar sayar da kifi
`Yar Fuveme, wani kauye a Ghana da tekun da ba za a yafe mata ta wanke shi, Esi Buobasa ta ganewa idonta ba labari ba, abubuwan da sauyin yanayi yake haifarwa.
Da mijinta da `ya`yanta biyar, an tilasta mata yin hijira a lokacin da teku ta taso, ta sa ba mai iya zama a mazauninsu.
A matsayinta na wadda ke kan gaba a sana'ar sayar da kifi a kauyensu, Buobasa da abokan sana`arta sun kafa wata kungiya da ke da manufar taimaka wa mata masunta da ke yankin, tunda zaizayar kasa ta ga~ar teku tana barazana ga hanyarsu ta samun abinci.
kawancen wanda a yanzu yana da mata kusan 100, suna haduwa a duk mako domin tattauna batutuwan da suka shafi mata da suke yin sana`ar da yin karo-karo na kudi domin tallafa wa iyalai da suke cikin bukata.
Mukan yanke kauna a duk lokacin da igiyar tekun ta yunduro, mutuwa takan zo mana da kuma zuri`a ta gaba
Esi Buobasa
Chila Kumari Burman, Ingila
Mai zane
Yin ayyuka da suka shafi fasaha da suka hada da ɗab'i, zane-zane da fina-finai, Chila Kumari Burman tana amfani da aikinta don tattauna batutuwa kamar wakilci da jinsi da al'adu.
A wannan shekarar an baje kolin aikinta a wajen bikin baje-koli na Blackpool Illuminations, wani biki da aka fara yin sa a Birtaniya tun 1879. Aikinta mai taken Lollies in Love With Light, ta yi shi ne sanadiyyar sana'ar da iyayenta ke yi.
A 2020, Burman ta gudanar da aikinta na 'Remebering a Brave New World' inda ta ƙawata fuskar ginin Tate Britain bisa la'akari da wani tarihihi na mutanen Indiya da kuma batun ƙarfafa mata.
A bara ta samu lambar girma ta MBE.
Paulina Chiziane, Mozambique
Marubuciya
Da littafinta na farko a 1990 wato"Ballad of Love in the Wind", Paulina Chiziane ta zama mace ta farko da ta wallafa littafi a Mozambique.
Girman da ta yi a gefen babban birnin Mozambique,wato Maputo, Chiziane ta koyi harshen potugal a wata makaranta ta katolika, ta nazarci harsunan a jami'ar Eduardo Mondlane,sai dai ba ta kammala karatun ba.
An fassara aikin ta zuwa harsuna daban-daban ciki harda Ingilishi da jamusanci da sifaniyanci. Da wani littafi mai suna "The First Wife: A Tale of Polygamy", ta samu lambar yabo ta gida ta José Craveirinha.
Sannan a baya bayan nan ta samu lambar yabo ta Camões, da ake ɗaukar ta a matsayin lambar yabo a ɓangaren rubutu a ƙasar Portugal.
Susanne Etti, Australia
Ƙwararriya a bangaren ɗorewar yawon buɗe ido
Ɗaya daga cikin masu ilimin kimiyyan yanayi a masana'antar tafiye tafiye da yawon buɗe idanu da ake dasu su kaɗai, Susanne Etti tana da sha'awar jagorantar masana'antar domin cigaba da ɗorewarta nan gaba.
Aikinta a matsayin manajar tasirin muhalli a duniya a Intrepid Travel, wata 'yar karamar ƙungiya mai gudanar da kasuwancin tafiye tafiye ya sa kamfanin ya zama na farkomai gudanar da yawon buɗe idanu da ke da tantantaciyar manufar rage gurɓata muhalli da yanayi da hayaƙI ke yi.
Etti ta rubuta wani jagora na gudanar da kasuwancin tafiye-tafiyen da ke son kawar da illar hayaƙi kuma muhimmin ɓangare na Tourism Declares, wadda ƙungiya ce ta al'umma ta sa kai mai ƙungiyoyin tafiye tafiye guda 400,da kamfanoni da ƙwararru waɗanda suka ayyana ɗaukar matakin gaggawa a kan yanayi.
A yau muna ganin ƙarin 'yan kasuwa da ke yaba wa da muhimmancin ɗaukar mataki a kan yanayi ta hanyar tsara manufofi domin rage matsala ta muhalli da zuba jari na sa ke sabunta makamashi da kuma duƙufa da rage yadda a ke fitar da hayaƙI da ke gurɓata muhalli.
Susanne Etti
Jannatul Ferdous, Bangladesh
Wadda ta rayu bayan ƙuna
Bayan ta tsira da ranta a wani haɗari da kusan fiye da rabin jikinta ya ƙone, Jannatul Ferdous ta ci gaba har ta zama ai shirya fina-finai, da rubutu da kuma gwagwarmayar kare masu lalurar nakasa.
Ita ce ta kafa Voice & Views wato murya da ra'ayoyi, ƙungiya ta kare haƙƙin ɗan'adam da take fafutukar kare haƙƙin mata da suka tsira da ransu sakamakon ƙuna.
Kamar yadda ƙawaye da iyalai ke kiran ta kainuwa, ta shirya ƙananan fina-finai guda biyar da wallafa litattafai guda 3, inda ta yi amfani da labarinta wajen faɗakar da jama'a da suke da lalurar nakasa.
Ferdous ta yi karatu sosai, kuma nasarorin da ta samu a karatu sun haɗa da digiri na biyu a adabin Ingilishi da kuma wani digiri a nazarin ayyukan ci gaba.
Licia Fertz, Italiya
Mai tallar kayan ƙawa da jan hankali
Ba duka ƴan shekaru 93 a duniya za su ce suna da mabiya 235,000 a Instagram, amma tsohuwar ƙasar italy ta ja hankali, wannan kaɗan ke nan.
Licia Fertz ta shaida yaƙin duniya na biyu, ta jure wa mutuwar ƴarta ƴar shekara 28, kuma mijinta ya rasu a gabanta.
Sai dai a lokacin da jikanta ya buɗe mata shafain Instagram don ya ɗebe mata kewa, irin fitar da take yi da murmushin da take yi na ɗaukar hankali ya sa ta zama gwarzuwa a soshiyal midiya.
Ta yi rubutu a kan tarihi, kuma an wallafa hotonta ba tare da sutura ba a bangon mujallar "Rolling Stone magazine" lokacin tana da shekara 89 da haihuwa.
Mace ce mai rajin yaƙi da tsufa, mai rajin kare hakkin mata da kare haƙƙin masu luwadi da maɗigo da dangoginsu, inda take yeƙuwa wajen ganin mutane sun yi alfahari da jikinsu da kuma sauya tunanin al'umma kan tsufa da tsofaffi.
Natalia Idrisova, Tajikistan
Ƙwararriya ɓangaren makamashi da ake samu daga shuke-shuke
Mata da suke zaune a yankunan karkara na Tajikistan sukan sha wahala kafin su samu makamashi kamarsu lantarki da itace. Jami'ar ƙungiyar muhalli ta Environmental charity project Natalia Idrisova ta fara neman ƙwararan hanyoyi na mgancce wannan matsala ta makamashi da kuma ilmantar da mata a kan albarkakun da Allah ya huwace da kuma fasaha daban-daban na samun wadataccen makamashi da kayayyaki.
Banda horarwa ƙungiyarta na bayar da na'ura na adana makamashi, da ɗakin girki mai aiki da hasken rana, da na'urar girki mai amfani da iska da sadaukar da lokuta na tallafa wa mata da kuma tallafawa daidaiton jinsi a gida ta hanyar yanayin da ya dace.
A yanzu Idrisova ta na koyar da al'umomi a kan yadda yanayi ke sauyawa musamman yadda yake shafar jama'a da su ke da lalurar nakasa, da lalubo hanoyin tabbatar da anji muryoyin waɗannan mutane a hanyoyi na siyasa.
Yadda lamura ke tsananta a duniya shi yake mana gargaɗI na karshe cewa b aka iya raba mutane daga abubuwan da suke tattare da su. Ba za mu yi sakacin ƙin cin gajiyar waɗannan abubuwa ba tare da manyan sakamako ba.
Natalia Idrisova
Vee Kativhu, Zimbabuwe/Ingila
Mai yin bidiyo a intanet da Youtube
Kama daga gaɗa karatunta da take yi da aiki na loto-loto a McDonald zuwa samun digirori a jami'o'in Oxford da Harvard, ƙoƙarin da Vee (Varaidzo) Kativhu ta yi wajen neman ilimi ya zama ƙarfafa gwiwa ga dubban mutane da suke faɗin duniya.
A lokacin da ta ke jami'a, ta buɗe wata tasha ta yutub domin yaɗa abubuwan da ta yi fama da su a matsayinta ta ɗaliba daga daga ƙaramin matsayi na zamatakewa da tattalin arziƙi, da kuma samar da bayani a kan karatu, da kuma zama jagora ga saura kamarta.
Tun daga lokacin Kativhu ta ƙaddamar da wani dandali na soshiyal midiya mai suna "Empowered by Vee", wanda ta nemi a samar da ilimi na manyan makarantu ga ɗalibai da ba su da galihu da ke faɗin duniya.
Ta rubuta littafi na taimaka wa kai domin matasa kuma a yanzu haka tana nan ta na karatun digirin-digirgir a ɓangaren shugabanci a ilimi.
Huda Kattan, Amurka
Wadda ta kafa wajen kasuwanci na kayan kwalliya
Iyayen Huda Kattan ƴan ci-rani ne da suka je Amurka daga Iraqi, ta girma a Oklahoma kuma ta yi watsi da sana`arsu ta gado/gida ta mayar da hankali ga abin da take sha`awa tsawon rayuwarta a fannin ado da kwalliya.
Ta shiga wata fitacciyar makarantar horarwa a ɓangaren ado da kwalliya a Los Angeles, ta samu tarin kwastamomi fitattu da kowa yake son ganin su ciki har da iyalan sarakuna da gidajen sarauta daga sassan Gabas ta Tsakiya.
Tuni ta zama wadda ta fi mabiya a fannin ado da kwalliya a Instagram inda take da mabiyan da suka haura miliyan 50.
Kattan ta ƙirƙiro nata kayan shafe-shafen na kwalliya, Huda Beauty, a 2013 ta hanyar ƙaddamar da kayan gyaran gira da gashin idanu. A yau kasuwancin nata na Biliyoyin-Dala ya ƙunshi kayayyaki na kwalliya na mata guda fiye da 140 da ake sayar da su a manyan kantuna fiye da 1, 500 a faɗin duniya.
Sophia Kianni, Amurka
Ɗaliba kuma 'yar kasuwa
Bayan ta yi Magana da dangi a iran ƴar kasuwa Sophia Kianni ta gane cewa babu wasu wadatattun labaru masu inganci a game da sauyin muhalli a harshensu, saboda haka ta soma fassara wa]annan abubuwa zuwa harshen Farsi.
Gaba kaɗan ta faɗaɗa zuwa aiki mai faɗI lokacin da ta samar da ginshiƙi na muhalli, ƙungiya da matasan duniya ke yiwa jagora da ba ta samun riba ba da ta ke da manufar fassara bayanai na yanayi zuwa kowane harshe guda da kuma samar dashi cikin sauƙI ga wadanda basu iya turanci ba.
A yanzu tana da ɗalibai yan sa kai su dubu goma daga ƙasashe 80 sun fassara kalmomi guda miliyan ɗaya a kan yanayi zuwa fiye da harsuna ɗari.
Burin Kianni shi ne taimaka wa kawar da duk wani shinge na harshe ga isar da ilimi na kimiyya ga duniya.
Matasa yan gwagwarmaya sun samar tare da rainon ƙungiyoyin faɗa da cikawa a kan yanayi a duniya, su ka janyo hankalin mutane da yawa domin bijirewa da sanya a rubuta dubban ƙorafe-ƙorafe akan bunkasa samar da wasu makamashi, da samar da miliyoyin dala domin taimakawa ɗaukar nauyin ayyuka na yanayi. ƙalubalen duniya na da girman gaske a garemu mu zauna mu haɗe ƙafa ko dan saboda shekaru ko dan kwarewarmu.
Sophia Kianni
Arati Kumar-Rao, India/Indiya
Mai daukar hoto
Da take aiki a sassan kudancin asiya, mai daukar hoton mai zaman kanta, marubuciya, kuma mai bincike ta kasa kangaren duwatsu da yanayi Arati Kumar-Rao ta tattara bayanai a kan sauyin da a ke samu na yanayi da sauyin yanayi ke haddasawa.
Ta yi bincike sosai a kan matsalolin ruwa na gargashin kasa da lalata halittu da sayen filaye domin msana'antu suke kara haddasa yarancin kasa da shafan kananan halittu da raba miliyoyin nau'in halittu da muhallinsu zuwa ga kacewa gaba daya.
Kumar-Rao ta karaɗe indiya fiye da shekara goma kuma labarunta masu daukar hankali yadda lalata muhalli ke shafar rayuwar jama'a da kuma kananan halittu.
Littafin ta, Marginlands: India's Landscapes on the Brink, ya nuna irin abubuwan da suke zaune a muhalli mafi tsanani na indiya suke cikin wani mawuyacin hali.
A tushen matsalar ta yanayi asara ce da ta shafi kasa da ruwa da iska. Ya zama wajibi mu magance wannan matsala.
Arati Kumar-Rao
Marijeta Mojasevic, Montenegro
Mai fafutukar kare haƙƙin naƙasassu
Bayan ta tsira daga bugun jini biyu lokacin da take makarantar sakandare, rayuwar Marijeta Mojasevic ta canza sosai.
Kasancewar ta sami sakamako na jiki da na hankali, wanda yawancinsu har yanzu tana rayuwa tare da su a yau, Mojasevic yanzu tana aiki a matsayin mai ba da shawara ga matasa da mai fafutukar kare haƙƙin naƙasa.
Ta yi amfani da muryarta don ƙalubalantar halaye da ɗabi'a ga mutanen da ke fama da ciwon jijiya ko naƙasa.
Ta tsara bita mai suna Life With Disability, inda ta bayyana abubuwan da ta fuskanta da su ƙalubale da kuma yadda ta shawo kansu don taimakawa ƙalubalantar son zuciya.
Ita jakadiya ce ta OneNeurology, wani yunƙuri wanda ke da nufin sanya yanayin jijiyoyin jiki fifikon lafiyar jama'a a duniya.
Sarah Ott, Amurka
Malamar Makaranta
Bayan shekarunta a jihar Jiyojiya ta Amurka sakamakon abubuwan da suka biyo bayan harin ranar 9 ga watan Satumba da aka fi sani da 9/11, malamar makaranta Sarah Ott ta ce tana fama da bayanan da ba daidai ba.
Duk da ta ilimantu a ɓangaren kimiyya ne, tsawon wasu lokuta takan yi tababar ko tabbas sauyin yanayi yana aukuwa.
Amincewar cewa tunaninta ba daidai ba ne shi ne mataki na farko a nemar da take yi wa gaskiyar lamari. Wannan tafiya tata ta yi sanadiyyar zamanta Jakadiyar Sauyin Yanayi a wata Cibiya ta Ilimin Kimiyya ta ƙasa.
A yanzun tana amfani da sauyin yanayi wajen koyar da abubuwa da suka shafi kimiyya da muke iya gani a zahiri ga ɗalibanta da kuma faɗakarwa a kan batutuwa na muhalli a al`umarta.
Duk da sauyin yanayi yanayi ne da kowa da kowa ya kamata ya tallafa, na za mu iya yin komai da komai mu kaɗai ba, Gwagwarmaya kamar lambu ce. Abu ne na lokaci. Sai hutu. Mututa kakar da kake ciki.
Sarah Ott
Jetsunma Tenzin Palmo, Indiya
Malamar Addini Budha
An haife ta a ingila a shekarar 1940, ta rungumi addinin Budha lokacin tana yar yarinya.
Ta na ƴar shekara 20 ta tafi indiya ta zama ɗaya daga cikin ƴan ƙasashen yammacin turai na farko da a ka naɗa ta a matsayin ɗaya daga cikin ƴan addinin na Bhuda.
Domin ɗaukaka matsayin mata da ke wannan aiki, Tenzin Palmo ta kafa Dongyu Gatsal Ling Nunnery a Himachal Pradesh, Indiya, wanda ya zamo gida ga mabiya addinin su fiye da 120.
An fi sanin ta da kwashe shekara 12 tana zaune a wani kogo a wani karkara da ke Himalayas, uku daga cikin waɗanda suka keɓance kansu don bauta. A 2008, aka ba ta muƙamin da ba a cika bai kowa ba na Jetsunma, da ke nufin jigo.
Lala Pasquinelli, Arjentina
Yar wasa
Lala Pasquinelli ce ta ƙirƙiri batun "Women who were not on a (magazine) cover'" wato mata da ba su samu an bayyana labaransu a jaridu ba, a 2015 domin ƙalubalantar yadda ake yi wa mata kuɗin-goro musamman kan abin da ya shafi kyau da kuma yadda ake ɗaukar su a kafafen yaɗa labaru da kuma al'adu.
Wannan ƙoƙari na ta shiyasa gangami ya yaɗu ko ina da ke gayyatar mata su sake tunani a game da jikinsu ciki har da batutuwa kamar na shekaru/tsufa da kuma irin abincin da suke ci. Kiran da aka yi a ƴan kwanakin nan na ɗaukar mataki #HermanaSoltaLaPanza "Sister, stop sucking in your tummy" ya haskaka ainihin labarai na mutane da ke da dukkan suffofi.
Lauya, mai rubutun waƙe, da gwagwarmayar kare mata, Pasquinelli ta yi aiki tuƙuru wajen rushe wani nau'i na nuna kyawawan mata da ta ce ba su kamata ba tare da ƙarfafa nuna daidaito ga mata.
Jess Pepper, Birtaniya
Wadda ta kafa Kanti a kan Yanayi
Kanti a kan Yanayi wani waje ne da al`uma key i wa jagora inda mutane suke taruwa domin shan irin su gahawa , da tattaunawa da ɗaukar mataki a kan sauyin yanayi. Jess Pepper ne ya soma kafa irinsa na farko a 2015, a wani ɗan ƙaramin gari da ke Scotland.
A yanzun tana tallafa wa al`umomi su soma nasu wuraren, su haɗa su a matsayin ƙawance na duniya.
Masu halarta sun ce waɗannan wurare ne da ba sa tattare da wata matsala ta tsaro, inda sukan yi musayar tsoronsu da damuwarsu a kan matsaloli na yanayi.
Pepper ta yi jagoranci daban-daban a sararin na yanayi, kuma babbar mai alfarma ce a a ƙungiyar Royal Scottish Geographical Society kuma wakiliya a Royal Society of Arts.
Matakai a kan Yanayi da sauye-sauye masu alfanu, suna aukuwa a al`umomi, da a wasu lokuta mata da yara suke yi wa jagora. Ganin yadda ƙawance ke ƙarfafa gwiwa da sanar da sauyi, ƙarfafa dagewa a lokacin da ake samar da damarmaki da sarari na siyasa domin ci gaba da kawo sauyi, su suke ƙarfafa mun gwiwa.
Jess Pepper
Matcha Phorn-in, Thailand
Mai gangamin kare haƙƙokin ƴan ƙasa da LGBTQ+
Zama a Tailan a kan iyaka da Myanmar, yankin da yayi fama da matsaloli na sauyin yanayi da kuma taƙaddama, Matcha Phorn-in ta maida hankali a kan aikinta na haƙƙokin 'yan tsiraru.
Ta kafa ƙungiyar ci gaba ta Sangsan Anakot Yawachon Development Project, wadda ƙungiya ce da ke da manufar ilmantarwa da ƙarfafa dubban mata da basu da jiha, da mata da basu da filayeda yan matasa yan al'ummar LGBTQ+.
Mai gwagwarmayar kare 'yan tsirarun ƙabila da kare mata masu auren jinsi na gida, Matcha Phorn-in ta jagoranci gwagwarmayar dakatar da cin zarafin da akeyi wa mata a yankin tare kuma da gwagwarmayar kare haƙƙin samun fili da kuma rashin adalci na yanayi ga mutanen da suka rasa muhallinsu ko a ka danne musu hakkokinsu.
Babu yadda za a samu mafita a kan matsalolin muhalli ba tare da an samu shiga mai ma'ana ba da kuma muryoyi daga al'umomi na gida, da LGBTQIA+, da mata da yara yan mata.
Matcha Phorn-in
Carolina Díaz Pimentel, Peru
Yar Jarida
Lokacin da aka gano tana da lalura irin ta galahanga a lokacin da take ƴar shekara 20 Carolina Díaz Pimentel da haihuwa, ta haɗa wa kanta kyak don bikin sanin cewa ta gane tana da lalura ta ƙwaƙwalwa.
A yanzu da take da shekara 30 tana tunƙaho da lalurarta tana aiki a matsayin ƴar jarida da ta ƙware ɓangaren masu lalura ƙwaƙwalwa da ɗauko labaru da suka shafi masu lalurar ƙwaƙwalwa.
Har ila yau Díaz ta yi aiki domin kawo ƙarshen ƙyamar da masu irin lalurar ke fuskanta. Ita ce ta kafa ƙungiyoyi daban-daban domin faɗakarwa a kan masu lalura irin ta ƙwaƙwalwa: "Mas Que Bipolar", da ƙawancen "Peruvian Neurodivergent Coalition", da kuma "Proyecto Atípico".
Wadda ta samu tallafi daga cibiyar Pulitzer Center da tallafin karatu daga Rosalynn Carter.
Shairbu Sagynbaeva, Kyrgyzstan
Ɗaya daga cikin wanɗanda suka kafa shagon ɗinki mai suna For Life Sewing Shop
Bayan ta kwashe shekara 3 ana mata maganin sankara da ta kai mataki na 4 kuma take ta ƙoƙarin biyan kudin maganinta, Shairbu Sagynbaeva a yanzu haka ta na samun sauƙi.
Tare da wasu mutum 4 masu lalura ta sankara da suke samun sauƙi ta kafa shagon ɗinki mai suna for life sewing shop, inda suke yin jakuna da saida su ta hanyar amfani da kayayyakin ado na kasar, inda suke ba da gudunmawar ribar da suke samu wajen tallafawa warkar da lalurar ta sankara.
Zuwa yanzu sun tara fiye da $33,000 (£26,500) ga mata 34 da ke buƙatar tallafin kuɗI domin jinya.
Sagynbaeva har ila yau ta ga no cewa akwai buƙatar tallafawa majinyata da suke nesa da cibiyar magann, saboda haka ta taimaka wajen kafa wajen kwana a kusa da ban a neman riba ba, da majiyyata za su iya zuwa su zauna.
Daria Serenko, Rasha
Mai waƙe
Marubuciya kuma ƴar gwagwarmayar siyasa Daria Serenko ta na ɗaya daga cikin jami'ai da dama da suke gudanar da Feminist Anti-War resistance – wadda ƙungiya ce da ke yaƙi da mamayar da Rasha ta yi wa Yukren.
Tsawon shekara tara ke nan take ta rubutu a kan cin zarafin mata a Rasha kuma ta rubuta litattafai guda biyu a kan mata da kuma zube na adawa da yaƙi.
Serenko har ila yau ita ce ta ƙirƙiri Quiet Pickett art initiative, inda ta ke sanye da kwalaye da a ka rubuta saƙonni domin janyo hankalin mutane a kan wasu batutuwa.
Makonni biyu kafin Rasha ta fara cikakkar mamayarta a Ukraine, hukumomi sun tsare Serenko suna zarginta da yaɗa saƙonni na tsatstsauran ra'ayi. Bayan kwanaki ka]an ta tsallaka zuwa Georgia kuma a yanzu haka hukomin Rasha sun ɗauke ta a matsayin wakiliya ta ƙasashen ƙetare.
Kera Sherwood-O'Regan, Niyuzilan
Mai gwagwarmayar haƙƙoƙin 'yan ƙasa da naƙasassu
Ƴar asalin Kāi Tahu kuma ƙwararra ɓangaren yanayi mai lalurar naƙasa, Kera Sherwood-O'Regan ta fito ne daga Te Waipounamu, tsibirin kudancin New Zealand.
Ta na cikin wanda suka kafa wata ƙungiya mai suna Activate, wacce ƙungiya ce da ta ƙware wurin tabbatar da adalci ɓangaren yanayi da kuma sauyi na zamantakewa.
A ayyukanta tana koyi ne da dabarun Māori ga ƙasa da kaka da kakanni wanda sai a 'yan kwanakinnan akayi watsi da su ɓangaren tattaunawa akan yanayi.
Sherwood-O'Regan na da cikakkiyar dangantaka da ministoci da jami'ai da kuma ƙungiyar al'umma ta farar hula domin nuna matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa a al'ummanta, a daidai lokacin da ta ke gwagwarmayar a ƙara kulawa da haƙƙoƙin mutane yan ƙasa da kuma mutane masu naƙasa a tattaunawa a kan yanayi.
Muna yin watsi da tsohon tsarin gwagwarmaya, muna samun waje, muna jagoranta tare da al-umma – kuma yana aiki. Ina jin mutane da dama a yanzu sun gane cewa baiwa 'yan ƙasa 'yanci it ace mafita daga matsalolin yanayi.
Kera Sherwood-O'Regan
Sagarika Sriram, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
Mai ilmantarwa da ba da shawara kan muhalli
Matashiya Sagarika Sriram na gwagwarmayar mayar da ilimin yanayi ya zama dole a makarantu.
Ta hanyar amfani da kwarewarta, ta kafa dandali a intanet mai suna Kids4abetterworld, domin ilimantar da yara a faɗin duniya da talla musu wajen gudanar da ayyukan cigaban al'ummominsu.
Ta ci gaba da wannan gwagwarmaya ta hanyar shirya taruka a fili da kuma ta intanet don koya wa yara yadda za su iya kawo sauyi a yaƙi da sauyin yanayi.
A lokacin da take karatun zurfafa iliminta a Dubai, Sriram na cikin tawagar yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ba wa yara shawarwari kan haƙƙoƙinsu, inda ta rungumi gwagwarmayar kare muhalli.
Lokaci ne na aiki ba na kwarmato ba, saboda a ilimantar da kowane yaro yadda zai rayu da kuma kawo sauyi mai ma'ana da muke nema a duniyar nan tamu.
Sagarika Sriram
Clara Elizabeth Fragoso Ugarte, Meziko
Direbar Babbar Motar ɗaukar Kaya
Direbar babbar mota Clara Elizabeth Fragoso Ugarte ta sadaukar da rayuwarta ta shekara 17 ga wata masana`anta da maza suka yi kaka-gida a cikinta, tafiye-tafiye zuwa falin Meziko a wasu daga cikin tituna mafi hadari na kasar.
Ainihinta daga Durango, an mata aure tana `yar shekara 17, Fragoso Ugarte ta haifi `ya`ya hudu, tana kuma da jikokinta bakwai.
A matsayinta ta mace mai tuƙa babbar mota, ta kwashe rayuwarta a kan hanya tana kai kayayyaki sassa daban-daban na Meziko da Amurka.
Har ila yau ta taimaka wajen horar da direbobi masu tasowa da kuma burin garfafa wa sauran mata gwiwar shiga masana`antar domin cimma daidaito na jinsi a sana`ar tuna manyan motocin daukar kaya.
Louise Mabulo, Filifins
Mai noma kuma ƴar kasuwa
A shekarar 2016, mahaukaciyar guguwar Typhoon Nock-Ten ta ratsa ta sassan Camarines Sur, da ke ƙasar Philippines, ta lalata kashi 80 cikin 100 na gonaki.
Louise Mabulota kafa The Cacao Project bayan afkuwar lamarin. Wadda ƙungiya ce da ke manufar kawo sauyi a tsarin samar da abinci na ƙasa ta hanyar noman gandun daji mai ɗorewa.
Mabulo ta ƙarfafa manoma su ciccire tsarin samar da abinci da iskar ta ruguza, ta kuma kasance kan gaba wajen bunƙasa tattalin arziƙi na yankunan karkara, ta maida ikon mallaka a hannun waɗanda suka nome gona.
Ta bada shawara ɓangaren tsare-tsare na yanayi na duniya, inda ta kwarmata labaru na yankunan karkara da kuma ilimi. Tsarin kare muhalli na majalisar Ɗinkin Duniya ya yaba mata a matsayin gwarzuwar matashiya ta ƙasa/Young Champion of the Earth.
Na samu ƙarfin gwiwa da nasan cewa mutane ne suke kafa ƙungiyoyi da ke fadin duniya kamar yadda nayi da jagora zuwa ga aikin gona da zai haɗa al'umomi a inda abincinmu zai ɗore da kuma samun sa, inda tsari na gaskiya da tabbatar da daidaito ke gudana da tattalin arziƙinmu.
Louise Mabulo
Oksana Zabuzhko, Ukraine
Marubuciya
Ta rubuta litattafai fiye da 20 ciki har da tatsuniya da rubutattun waƙoƙi, da waɗanda ba tatsuniyoyi ba, sannan, Oksana Zabuzhko ana kallon ta a matsayin ɗaya daga cikin manyan marubuta na ƙasar Ukraine kuma ma'abuciyar ilimi.
A duniya ba ki ɗaya an san ta saboda rubuce-rubucenta kamar su "Field Work in Ukrainian Sex," da kuma "Museum of Abandoned Secrets."
Ta kammala karatu a sashen Falsafar na jami'ar Shevchenko da ke Ukraine kuma tana da digiri na uku a falsafar fasaha.
An fassra litattafanta zuwa harsuna 20, kuma ta samu lambobin yabo masu yawa na kasa da na duniya baki ɗaya ciki har da lambar yabo ta rubutu ta "Angelus Central European Literary", da lambar yabo ta ƙasa ta "Ukraine Shevchenko", da kuma lambar yabo ta "French National Order of the Legion of Honour".
Nishaɗantarwa da Wasannin motsa jiki
Aitana Bonmatí, Sifaniya
Ƴar wasan ƙwallon ƙafa
Da a ka haife ta a Catalonia, ƴar wasan tsakiya Aitana Bonmatí ta samu nasarar lashe gasar sifaniya da kuma gasar zakarun turai da akayi da kulob dinta na Barcelona a wannan shekarar.
Sai dai a lokacin gasar cin kofin duniya ne ta zama wata gwarzuwar ƴar wasa ta duniya: ta zama jigo a samun nasarar Sifaniya inda ta jefa ƙwallo guda uku a cikin raga, kuma aka ba ta fitacciyar ƴar wasa ta gasar. Ƴar shekara 25, ta lashe lambar yabo Ballon d'Or kuma a ka nada ta a matsayin gwarzuwar yar wasan Uefa ta shekara.
A matsayinta ta mara tsoro wajen amfani da muryarta a filin wasa da kuma a bayan fage, Bonmatí ta yi Magana a kan daidaito a wasannin kwallo ga mata.
A lokacin da nasarar da kasarta ta samu a wasan cin kofin duniya ta dishe saboda sumbatar wata ƴar wasa Jenni Hermoso, da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Sifaniya Luis Rubiales yayi a laɓɓa, Bonmatí ta yi amfani da na amincewa da kyautar Uefa ta bata domin nuna goyon bayanta ga ƴan uwanta ƴan wasa da kuma sauran mata da ke fuskantar irin wannan ƙalubale.
Antinisca Cenci, Italy/Italiya
`Yar wasan doki
A lokacin da Antinisca Cenci ta soma wasan da doki a shekarunta na 30, ba ta dauka cewa bayan shekara 10 za ta dinga zagaye duniya tana rangadi tare da `yan wasa da suke wasanni a kan dawakai.
Daga La Fenice, da ke arewacin Italiya, ba ta samu saurin rayuwa ba. An sanar da mahaifiyarta cewa ba za ta tsira ta yi rai a sanyin farko ba bayan ta yi fama da wasu matsaloli a lokacin haihuwa.
Cenci ta soma wasan a bangare na wani shiri da karamar cibiyar ANFFAS ta kullo da shi (kungiyar Iyalai da Mutane da suke da Lalurar Nakasa ta kasa ta Italiya/Italy's National Association for Families and People with Disabilities) da kungiyar `yan wasa ta La Fenice.
A yanzun haka tana horarwa tare da zakaran duniya na wasan na doki Anna Cavallaro da mai horarwa Nelson Vidoni.
Andreza Delgado, Brazil
Shugabantar harkokin al'ada
Da ta ke ƙoƙarin kawo abubuwan da ta koya, a lokacin da ta halarci wani taro a kan littafi ga mutanenta da suke zaune a unguwannin ya-ku-bayi maƙwabta da ke wajen Sao Paulo, Andreza Delgado ta taimaka wajen ƙaddamar da PerifaCon.
Taron wanda kyauta ne ya mayar da hankali a kan marubuta littafan zane da ƴan wasa da sauran masu bayar da gudunmawa daga yan Brazil da a kan musu kallon banza a matsayin ci-ma-zaune ɓangaren al'adu ko ƙirƙire-ƙirƙire.
Ta amfani da litattafai na zane-zane, da wasanni na bidiyo, da taro na wasanni, da sauran abubuwa na al'adu, PerifaCon karo na uku ya gudana a 2023 inda ya sama mutane fiye da 15,000 da suka halarta.
Ta amfani da dandalinta daban-daban, a matsayinta ta ƴan youtube, Delgado ta zama mai Magana sosai a kan samar da damar kai wa ga al'adu a Brazil, ta mayar da hankali musamman a kan ayyukan ƴan wasa baƙar fata.
Desak Made Rita Kusuma Dewi, Indoneshiya
Mai haye-haye
Lokacin da take makarantar firamare a Bali, an gayyace Desak Made Rita Kusuma Dewi zuwa wasan hawan bango, kuma nan da nan ta kamu da son haye-haye.
Ta samu nasarori a farko-farko a gasannin na matasa, amma "Sarauniyar hawan dutsen ta Indoneshiya" ta kai matsayi mafi girma a bana, inda ta lashe gasar gudun mata a gasar hawa bango ta kofin duniya ta 2023 IFSC inda ta kafa tarihi cikin minti 6 da daƙiƙa 49.
Wannan rawar da ta taka ta samu tikitin shiga gasar Olympics ta Paris 2024, inda hawan bango zai kasance a matsayin wani taro a karon farko.
Mai hawar za ta iya kafa tarihi a Indonesiya, wacce zuwa yanzu ta sami lambar yabo wasan badmiton, da na ɗaga nauyi da kuma harba mashi.
America Ferrera, Amurka
Ƴar wasan fim
Fuskar da a ke saurin ganewa a duniyar nishaɗantarwa ƴar wasa da ta samu lambobin yabo, darakta kuma mai shirya fina-finai America Ferrera ta yi suna a fita daban-daban da take yi ciki harda fitaccen fim ɗin da a ka ɗauka kwanan nan, wato Real Women Have Curves da kuma wani wasan Ugly Betty.
Ta zama mafi ƙarancin shekaru da ta samu lambar yabo ta Emmy a matakin jagoran an wasa saboda rawar da ta taka a – ita ce ta farko ar al'umman Latina. Daɗaɗɗiyar ƴar gwagwarmaya, Ferrera ta yi fice a wajen yin batu a kan haƙƙoƙin mata da kuma buƙatar ƙara samun wakilci a fina-finai.
Ɗiyar ƴan cirani na Honduras ta yi gangamin neman kyautata rayuwar waɗanda ba farare ba a amurka ta hanyoyi daban-daban da ba na samun riba ba.
Anne Grall, Faransa
Yar wasan Barkwanci
Kulob ɗin Greenwashing Comedy kulob ne da ya miƙe tsaye ko da ya haɗa ƙarfi wajen magance batutuwa na muhalli da kuma kare haƙƙoƙin mata da kauda fatara, da hakkokin masu lalurar nakasa, da kuma haƙƙoƙin masu auren Jinsi.
Ƴar wasan barkwanci Anne Grall ce ta ƙirƙiro kulob din, wadda ta yi imanin cewa ta barkwanci, za a iya dasa batun sauyi a zukatan jama'a har da ma shafar halayyarsu.
A al'ummar da ke son nishaɗi da kananan kalamai da saƙonni ke yin tasiri, Grall ta yi imani da cewa barkwanci zai iya zama kyakyawar hanyar musayar ra'ayi idan aka yi batun sauyin yanayi.
Nasarar da kulob ɗin ya zamo abun farin ciki ne saboda ya nuna cewa a yau mutane da dama sun damu da batun sauyin yanayi, kuma suna so su hadu waje guda, su yi dariya sannan su bar wajen barkwancin da karsashin cewa sun shirya domin ci gaba da yaƙar nasarar!
Anne Grall
Georgia Harrison, Ingila
Mai shirye-shiryen talabijin
Bayan Georgia Harrison ta zama wadda a ka ci zarafinta ɓangaren lalata saboda saboda matsayinta, ta yanke shawarar amfani da labarinta wajen taimakawa magance cin zarafin mata da a ke yi da sauya irin kallon da ƴan kallo da ke Ingila ke yi wa ire-irenta.
Mai fitowa a talabijin ɗin da ta yi suna saboda fitowwar da ta ke yi a shirye-shirye daban-daban, kamar su Love Island da The Only Way is Essex, ya haddasa gangamin a yi gyara ga dokar Ingila ta intanet ya zama cewa cin zarafin masu fitowa a talabijin laifi ne, da har ila yau ake kira da "revenge porn" ya zama mai sauƙin hukuntawa.
Harrison a yanzu haka tana kiran dandali daban-daban na intanet su fuskanci ƙwararan hukunci saboda sa hotuna da a ka ɗauka ko a ka watsa ba tare da izini ba.
Harmanpreet Kaur, Indiya
Ƴar Wasan kuriket
A wannan shekarar, Harmanpreet Kaur ta zama mace ta farko ƴar Indiya da ta zama ɗaya daga cikin gwarazan ƴan wasan kuriket guda biyar na wannan shekara.
Kyaftin din ƴan wasan kuritet ta mata ta ƙasa, mai cin ƙwallo ce a cikin gida da waje. A shekarar bara ta sa ƴan wasanta sun ciwo azurfa a gasar wasannin ƙasashe rainon Ingila.
Sannan a wasan kurket na gida ta jagoranci Indiyawan Mumbai zuwa buɗe gasar wasanni na mata da ta gudana a wata Maris.
Ɗaya daga ciki nasarorin da ta samu shine a 2017 lokacin da ta ciyo wa Indiya kwallaye 171 ta doke masu kwallo 115 a gasar kusa da ƙarshe ta cin kofin duniya da suka fafata da Australia da ya taimaka wa ƴan wasanta kaiwa fafatawa ta ƙarshe.
Dayeon Lee, Koriya ta Kudu
Mai hanƙoro a Kpop4Planet
Ta Kpop4Planet, Dayeon Lee tana tara masu so da sha`awar K-pop da ke ko`ina cikin faɗin duniya domin tunkarar matsalar yanayi.
Tun ƙaddamar da gangamin a 2021, ƙungiyar fafutukar ta nemi mutane da suke da hali a babbar masana`antar mishaɗantarwa Koriya ta Kudu su ɗauki mataki a kan yanayi, da komawa ga makamashin da ake iya sabuntawa.
Ƙungiyar ta nuna matsaloli na yanayi da suka sa taurarin na K-pop su jingina da waƙoƙi ma zamanance.
Dayeon Lee a yanzun ta zarce batun kaɗe-kaɗe, domin ƙalubalantar alƙawuran yanayi na abubuwa na ƙawa, da a wasu lokutan sukan bayyana a tattare da fitattu na K-pop da kowa yake son gani a bayyanarsu cikin jama`a.
A lokacin da muka yi tsayin daka wajen neman a yi adalci, ba ma taɓa haƙura har sai mun kawo sauyi. Mun tabbatar da hakan ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, kuma za mu ci gaba da yin hakan, yaƙi da matsaloli na muhalli.
Dayeon Lee
Justina Miles, Amurka
Ɗan wasan kurumta
A wasannin Super Bowl LVII na watan Fabrairu , ɗaya daga cikin wasannin da motsa jiki da aka fi kallo a duniya, Justina Miles ta kafa tarihi.
Bidiyon `yar wasan kuma kurma yana ta karaɗe soshiyal midiya a lokacin da take kwaikwayon wasu daga cikin waƙoƙin fitacciyar mawaƙiya pop Rihanna tana kakkarya jiki da takawa cikin kwarjini da karama.
Wannan ya sa ta zama mace kurma ta farko da ta yi wasa cikin tsarin maganar kurame na Amurka a wajen nishaɗantarwa na rabin lokaci, a wajen fitaccen wasannin Super Bowl. Har ila yau maganar kurame da ta yi amfani da ita wajen rera Lift Every Voice and Sing – da aka fi sani da Taken ƙasa na Baƙaƙen Fata wato Black National Anthem da ta yi tunda farko, shi ne na farko a bikin.
Miles tana so ta nuna wa duniya ƙarin sahihin wakilci na mutane masu nakasa, tana kuma fatan buɗe tata horarwar domin horar da ƙarin jami`an jinya kurame.
Dia Mirza, Indiya
Ƴar Wasan fim
Dia Mirza ba ta tsaya ga samun lambobin yabo saboda yadda take taka rawar gani a fina-finan Indiya kawai ba, har ila yau ta kasance cikin ayyukan kare muhalli da na jin-ƙai.
A matsayinta ta Jakada ta Shirin Majalisar Ɗinkin Duniya a kan muhalli, Mirza ta yaɗa saƙwanni a kan batutuwa kamar su sauyin yanayi, da iska mai lafiya da kare dabbobi na daji.
Ita ce ta ƙirƙiro da 'One India Stories', shiri da yake da manufar sanar da labaru masu tasiri, da kamar yadda ta faɗa a kalamanta, 'make you pause and think'.(za su sa ka dakata ka yi tunani).
Har ila yau ita jakadiya ce ta shirin 'Save the Children' wato Ceton Yara, da Asusu na Duniya na Kula da Jin Daɗin Dabbobi kuma mamba ce a hukumar Gidauniyar Kare Halittu mai suna Sanctuary Nature. Foundation.
Zandile Ndhlovu, Afirka ta Kudu
Mai koyar da ninƙaya cikin ruwa
A matsayinta ta baƙar fata mace mai koyar da ninƙaya ta farko, Zandile Ndhlovu tana son ƙara yawan masu shiga teku daga mutane daban-daban.
Ta kafa gidauniyar The Black Mermaid Foundation, wadda ke bai wa matasa da al`umomi na kusa shiga damar shiga teku, tare da fatan taimaka wa sabbin ƙungiyoyi yin amfani da waɗannan sarari na wasanni cikin ƙwarewa da kuma motsa jiki.
Ndhlovu mai bincike ce a teku, mai ba da labari kuma mai shirya fim. Tana amfani da ƙwarewarta wajen taimaka wa sabbin masu kula da teku – mutanen da suka koyi abubuwa game da gurɓata teku da hanƙoron teku da kuma gwagwarmayar kare muhalli.
Tunanin yawan muryoyin masu tasowa, da miƙewa domin kawo sauyi a cikin al`umma, su ne ke ba ni ƙwarin gwiwa wajen nazari kan matsalolin yanayi.
Zandile Ndhlovu
Alice Oseman, Ingila
Marubuciyar fina-finai
Marubuciya da ta samu lambobin yabo, malama kuma marubuciyar fina-finai, Alice Oseman ita ce ta ƙirƙiri littafin da ya yi kasuwa tsakanin matasa wato "Heartstopper." Har ila yau ta canza wasan labarin "LGBTQ+ coming-of-age" ya koma wasan talabijin da ya samu lambar yabo.
Oseman ce ta rubuta ɗaukacin labarin, kuma ta kasance a kowane mataki na shirya wasan, tun daga zaɓen ƴan wasa zuwa kaɗe-kaɗe.
Ita ce marubuciyar wasu litattafai na matasa da daman, ciki harda "Radio Silence, Loveless da Solitaire," da aka wallafa tun tana ƴar shekara 19.
Litattafanta sun samu shiga sahun litattafan da suke samun lambobin yabo ciki har da lambar yabo ta "YA Book Prize," da lambar yabo ta "Inky Awards, da lambar yabo ta "Carnegie Medal," da kuma lambar yabo ta Goodreads Choice Awards.
Paramida, Jamus
Mai tsarawa da shirya kade-kade da gabatar da su
Da dagewa kafin barkewar bore/zanga-zanga a Iran a shekarar da ta gabata, Paramida tana ta watsi ko bijire wa takaita wa matan `yan asalin Iran wasu abubuwa na al`adu da ake yi.
A yanzun mazauniyar Berlin, Paramida ta gano sha`awarta da basirarta a kade-kade da al`adar raye-raye a lokacin da take zaune a tsaksnin Frankfurt da Tehran a lokacin da take da karancin shekaru.
Sakamakon karfafa gwiwar da ta samu daga rawa da kida mai tarihi, kade-kadenta mai suna Love On The Rocks ya daukaka jin dadi da al`adar rawa ta wani daga can waje a yau.
A matsayinta ta mazauniyar kulob na dabdalewa da daddare na Berghain a Berlin, ta zama DJ da ake ribibin nemanta ta zo ta yi wasa a duniya bakidaya kuma fitacciyar mai yin kaɗe-kaɗe a duniya. Ta yi amfani da wannan sarari ko dama wajen dalubalantar dabi`u na jinsi a ɓangaren kaɗe-kaɗe da maza suka fi yin kaka-gida da masana`antar dabdalewa ta dare.
Camila Pirelli, Paraguay
Yar wasan Olympic
Duk da ƙwarewarta a wasan heptathlon, gasar gudu na tsallake shinge ne na mita 100 ya sa Camila Pirelli ta kai ga wasannin Olimpik na Tokyo.
Kamar yadda aka santa da laƙabin Guarani Panther, 'yar wasan ta sama nasarori daban-daban ɓangaren motsa jiki kuma mai horas da 'yan wasa cee kuma malamar turancin Ingilishi.
Pirelli ta girma a cikin iyali da suka san muhimmanci muhalli a wani ƙaramin gari da ke Paraguay inda ta ga matsalolin da sauyin yanayi ya haifar.
A yanzu zakara ce ta EcoAthlete da ke nufin ta duƙufa ga amfani da dandalinta na wasannin motsa jiki domin ƙarfafawa mutane tattaunawa a kan sauyin yanayi da kuma ɗaukar mataki domin rage gurɓata muhalli da hayaƙi ke yi.
Na girma a wani gari da ganin namun daji a kullum ba ba}on abu bane sanin cewa waɗancan dabbobi suna wahala a yanzu saboda sauyin yanayi shi yake matuƙar damuna da kuma sa ni son in taimaka.
Camila Pirelli
Aziza Sbaity, Lebanon
Yar wasan guje-guje
Wadda ake girmamawa a matsayin mace ƴar ƙasar lebanon mafi sauri a tarihi bayan ta zama ta farko a gudun mita 100 a ƙasar, Aziza Sbaity a ƴan kwanakin nan ta sake zama kanun labaru a matsayinta ta mace ta farko baƙar fata ƴar wasa daga ƙasar ta da ta ciwo zinari a gasar zakarun yammacin Asiya da kuma Larabawa a wannan shekara.
Wadda mahaifiyarta ƴar Laberiya mahaifinta ɗan Labanan suka haife ta, tana yar shekara 11 ta matsa zuwa labanan inda ta yi fama da matsaloli na wariyar launin fata.
Wasannin motsa jiki ne ya zama wata gare ta ta gano baiwar da Allah ya yi mata da ƙarfafawa da kuma ƙara duƙufa ga gwagwarmaya.
Ta yi amfani da matsayinta wajen tattaunawa a kan wariya da ake nuna wa ta launin fata da ake nuna wa a ƙasar ta kuma kasance kan gaba wajen tabbatar da dadaito da yin komai tare, sannan ta haɗa ƙarfi wuri guda da makarantu da jami'o'i domin ƙarfafa gwiwar matasan labanan.
Khine Hnin Wai, Myanmar
Ƴar fim
Farawarta a matsayin jaruma a Myanmar kusan shekaru 25 da suka gabata, Khine Hnin Wai ta shahara saboda rawar da ta taka a matsayin jagora a fim din San Ye. Ta ci gaba da zama ɗaya daga cikin ƴan fim da suka yi nasara a sinimar Burma.
Duk da haka, a yanzu an fi saninta da ayyukan agaji. A shekarar 2014, ta kafa gidauniyar Khine Hnin Wai, wata ƙungiyar agaji da ke tallafawa abubuwa daban-daban, ciki har da kula da marayu da yaran da aka yi watsi da su.
Ta hanyar aikinta, a halin yanzu tana kula da yara kusan 100 waɗanda iyayensu ba sa iya tallafa musu saboda wasu dalilai.
Har ila yau Hnin Wai tana aiki a matsayin jakadiyar hana safarar yara.
Bianca Williams, Ingila
Ƴar wasan Motsa jiki
Wadda ta yi nasara a wasannin turai da na ƙasashen rainon ingila ɓangaren gudun mita 4x100 da zinari, Bianca Williams fitacciyar ƴar birtaniya da arewacin Ireland, kyaftn ce ta zakarun ƴan wasan Turai ta shekara ta.
A watan Juli ta kammala a matsayin ta biyu a gudun mita 200 a guje-gujen zakarun Ingila domin kare matsayinta a ƴan wasan birtaniya a gasar zakarun guje-guje na duniya a Budapest.
Ita da abokiyar gudun ta Ricardo Dos Santos, jami'an 'yan sanda sun dakatar da su suka bincike su a landan a watan yuli na shekara ta 2020.
Williams da Dos Santos sun gabatar da korafi a hukumance inda suka zargi yan sanda da nuna musu wariyar jinsi aka samu jami'an ƴan sandan biyu da laifi kuma aka sallame su daga aiki.
Siyasa da Gwagwarmaya
Maryam Al-Khawaja, Bahrain/Denmark
Ƴar gangamin kare Haƙƙoƙin ɗan'dam
Ƴar gangamin kare haƙƙoƙin ɗan'adam yar Denmar-Bahraini Maryam Al-Khawaja murya ce da take kan gaba wajen neman a kawo sauyin siyasa a Bahraini da kuma yankin gulf.
Aikinta na da manufar ƙarin haske a kan danne haƙƙin ɗan'dam musamman neman a sako mahaifinta, Abdulhadi Al-Khawaja, ta gangamin #FreeAlKhawaja. Fitaccen ɗan gwagwarmaya ne da aka kai shi gidan yari a hukuncin ɗaurin rai da rai saboda ya shiga boren da akayi na goyon bayan dimokraɗiyya da akayi a shekarar 2011.
Al-Khawaja ta yi aiki a hukummomi daban-daban ciki harda kamfanin Civicus da kuma hukumar kare haƙƙin ɗanAdam na duniya, kuma ta na cikin ƙungiyar mata matasa ta FRIDA kuma likita ce ta kare haƙƙin ɗan'adam.
Shamsa Araweelo, Somalia/Birtaniya
Yar gangamin hana yi wa mata Kaciya
A burinta na ganin an daina yi wa mata kaciya, Shamsa Araweelo ta ilmantar tare da wayar da kai ta amfani da bidiyo da take haɗawa da kuma waɗanda take watsawa kai tsaye.
Araweelo, wadda aka haife ta a Somilya kuma tana zaune a Ingila, an yi mata kaciya lokacin ta na ƴar shekara 6 ba tare da wasu ƙwararan dalilai daga likitoci ba.
Saboda ta na da mabiya fiye da 70 a TikTok, ta na so ta tabbatar da cewa babu wanda ya yi saura da bai san wannan batu ba.
A yanzu haka tana taimakawa ‘yan ƙasar birtaniya da suka maƙale a ƙasashen waje a ke kuma cin zarafin su. Har ila yau ta samar da shawarwari a kan yi wa mata kaciya ga ‘yan sandan Landan, kuma ta na shirin ƙaddamar da wata ƙungiya ta agaji mai suna The Healing Garden.
Yasmina Benslimane, Morocco
Wadda ta ƙirƙiro ƙungiyar "Politics for Her"
Ta sadaukar da kai don inganta daidaiton jinsi, Yasmina Benslimane ta kafa Politics4Her, wadda ke haɓɓaka shigar matasa mata da ƴan mata cikin harkokin siyasa da yanke shawara.
A lokacin da wata mummunar girgizar kasa ta afku a kasarta ta Moroko a cikin watan Satumba, Benslimane da kungiyarta sun yi kira da a ɗauki matakin ba da taimako ga mutane.
Ta fitar da wani bayani da ke nuna kalubale musamman ga mata da 'yan mata wadanda bala'in zai shafa, kamar talaucin lokaci da auren dole.
A matsayinta na mai ba da shawara da kuma memba na ƙungiyoyi masu zaman kansu da yawa, tana taimaka wa mata matasa su haɓaka ƙwarewar jagoranci. Aikinta ya samar mata lambar yabo ta Majalisar Dinkin Duniya mai wanzar da zaman lafiya.
Yael Braudo-Bahat, Isra'ila
Mai haƙoron samar da zaman lafiya
A matsayinta ta shugabar kungiyar Women Wage Peace (WWP), Yael Braudo-Bahat ta kawo asalinta a fannin shari'a ga kungiyar zaman lafiya ta Isra'ila wacce ke da mambobi sama da 50,000.
An kafa WWP a cikin 2014, WWP na neman sasantawa ta siyasa game da rikicin Isra'ila da Falasdinu, yana mai da hankali kan rawar da mata ke takawa a cikin tsarin zaman lafiya.
"A cikin shekaru biyu da suka gabata, WWP ta haɗu da ƙungiyar mata ta Falasdinawa, Women and Sun "
Braudo-Bahat ta ce mai ba ta shawara, fitacciyar mai fafutukar neman zaman lafiya kuma wacce ta kafa WWP, Vivian Silver, wacce ta sadaukar da shekarunta na rayuwarta wajen bunkasa fahimta da daidaito tsakanin Isra'ilawa da Falasdinawa na da alhakin ƙwarewarta. An kashe Silver a harin da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoba 2023.
Alicia Cahuiya, Ekwado
Mai gwagwarmayar kare haƙƙoƙin ƴan ƙasa.
A matsayinta ta ginshiƙi a gwagwarmayar kare gandun daji na Amazoniya ta Ekwado, Alicia Cahuiya tana da gagarumar nasara a wannan shekarar.
A zaɓen jin ra`ayoyin `yan ƙasa mai tarihi da ya gudana a watan Agusta, `yan ƙasar Ekwado sun zaɓi a dakatar da dukkan sabbin rijiyoyin mai a Yasuní National Park – matakin da ke nufin kamfanin mai na ƙasa ya kawo ƙarshen ayyukansa a ɗaya daga cikin yankunan da suka fi arzikin albarkatu a duniya, wanda gida ne ga al`umma `yan asalin ƙasa da ba a tintiɓe su ba.
Cahuiya, wacce aka haife ta a Yasuní kuma shugaba ce ta Waorani (NAWE), ta kwashe fiye da shekara goma tana gangamin a gudanar da zaɓen jin ra`ayoyin jama`a
A yanzun haka ita ce shugabar ɓangaren mata, a tarayyar Mutane `Yan Asalin Ekwado.
Matsaloli na sauyin yanayi sun sa abubuwa sun zama daban a gare mu, da haddasa ambaliya da ta lalata mana amfanin gona. A lokacin da rana take tsananin zafi kuma akwai fari, muna asarar abincinmu mai tarin yawa da ke haddasa mana babban baƙin ciki, domin kuwa ƙoƙarin da aka yi a kan amfanin gona, ya tafi a banza ke nan.
Alicia Cahuiya
Amal Clooney, Birtaniya/Lebanon
Lauya Mai Kare Haƙƙin Bil`Adama
Amal Clooney lauya ce mai kare haƙƙin bil`adama da take ta samun lambobi da kyaututtukan yabo da ta kwashe shekaru tana kare waɗanda aka tabka musu rashin adalci.
Shari`u da ta yi nasara a kan su sun haɗa da na kisan kiyashi da aka yi a Armenia da Myanmar, da cin zarafin mata a Malawi da Kenya, da laifukan da aka aikata wa bil`adama a Ukraine.
Nasarorin da ta samu a ƴan kwanakin nan sun hada da wakilta/tsaya wa waɗanda harin mayaƙin ƙungiyar IS da na Darfur ya shafa. Ta taimaka wajenn sako ƴan jarida da aka garƙame da sauran fursunonin siyasa da gwamnatocin kama-karya suka azazzala.
Farfesa ce ta loto-loto a Makarantar Koyon Aikin Lauya ta Kolombiya, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa Gidauniyar Tabbatar da Adalci ta Clooney da take yin aikin lauya kyauta ga waɗanda aka take musu haƙƙoƙin a fiye da ƙasashe 40.
Dehenna Davison, Birtaniya
Ƴar majalisar Dokoki
A shekarar 2019, Dehenna Davison ta zama ƴar majalisar dokoki ta farko mai tsatsaurar ra'ayi ga Bishop Auckland tun bayan ƙirƙiro da mazaɓar a 1885. Ta zama minista a shekarar 2022, inda ta mayar da hankali a kan zamantakewa da kuma ci gaba.
Ta ajiye aiki a watan satumba na 2023, inda ta fito fili tana batu a kan lalurar tsananin ciwon kai.
Lokacin da Davison take 13, naushi ɗaya ya kashe mahaifinta, da ya sanya ta auka lamuran siyasa. Ta kafa wata ƙungiya ta ƴan majalisa da ke yaƙi da cin zarafi na naushi guda da kuma neman gangamin a kan a yi adalci a kan "One Punch UK" da kuma gyara a kan hukuncin wanda ya aikata irin wannan laifi.
Har ila yau ta mayar da hankali a kan samun ƙarin hanyoyin magance tsananin ciwon kai da kuma gangamin samar da ƙarin kudaden gudanar da bincike ɓangaren sankara.
Christiana Figueres, Costa Rica
Jami'ar Diflomasiyya da Kuma Kare Yanayi
Da tattauna wa ta cije a wajen taron majalisar ]inkin duniya a kan yanayi a shekarar 2009 a Copenhagen, sai a ka janyo Christiana Figueres don magance wata matsala.
Bayan an naɗa ta amatsayin babbar sakatariya ta taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kan sauyin yanayi, Figueres ta kwashe shekara 6 ta na tsara wani shiri domin tabbatar da ƙasashe sun amince a kan dabarun ɓullowa matsaloli na yanayi.
Bayan an naɗa ta amatsayin babbar sakatariya ta taron Majalisar Ɗinkin Duniya a kan sauyin yanayi, Figueres ta kwashe shekara 6 ta na tsara wani shiri domin tabbatar da ƙasashe sun amince a kan dabarun ɓullowa matsaloli na yanayi.
Figueres ta na ɗaya daga cikin wanda suka kafa Global Optimism, wacce ƙungiya ce da ta ke aiki da ƴan kasuwa domin magance matsaloli da suka shafi yanayi a aikace.
A wani lokaci baƙin ciki kan lulluɓe ni in ji na nakasa saboda tunani na, in ji na kasa taɓuka komai. A wasu lokutan kuma nakanji haushi inji tunanina ya mamaye ni, in ji ina so in yunƙura in yi wani abu amma a wasu ranakun ina amfani da wannan damuwa tawa wajen danne baƙin cikina in mayar da su wani karsashi na yunƙurawa, da ƙauna, da farin ciki da tunanin samar da kyakyawar duniya ga ƴaƴanmu da jikokinsu.
Christiana Figueres
Bella Galhos, Leste
Yar Gwagwarmayar Siyasa
Ƴar hanƙoro maras tsoro, Bella Galhos ta zama jigo wajen kawo ci gaban Timor-Leste da kafin da kuma bayan ƙasar ta samu ƴancin kai daga Indonesiya a 2002.
A shekarun da ta yi ta na gudun hijira, ta zaga duniya ta na gwagwarmayar neman ƴancin cin cin gashin kan mutanenta. Da ta dawo Timor-Leste bayan samun ƴancin kai, Galhos ta shiga ayyukan sake gina ƙasar bayan shekaru da aka yi a na taƙaddama da ta jefa rabin al'ummar ƙasar cikin tsananin talauci.
A 2015 ta buɗe makarantar Leublora Green School, da ta ke ɗaukaka ɗorewar ci gaba da ƙarfafa wa yara gwiwar su zama masu kawo canji.
A yanzu haka Galhos ta na aiki a matsayin mai bai wa shugaban ƙasar Timor-Leste shawara, inda ta maida hankali a kan ƙarfafa mata kuma fitacciyar murya ce ga al'ummar LGBTQ+.
Rina Gonoi, Japan
Tsohuwar Soja.
Mata sojoji sun taimaka wa Rina Gonoi ƴar shekara 11 a lokacin kwashe jama`a sakamakon muguwar girgizar ƙasar da ta auku a 2011 da tsunami kuma tun daga lokacin ta yi mafarkin tana aiki Rundunar Kare Kai ta Japan .
Ta zama hafsa, sai dai wannan mafarki nata na tun tana yarinya, ya sukurkuce saboda kusan a kullum sai an neme ta da lalata.
Gonoi ta bar aikin soja a 2022 kuma ta ƙaddamar da gangamin bainar jama'a da ke yin kiran a dinga kiyayewa da gaskiya, wanda aiki ne ba ɗan ƙarami ba, a al`umar da maza suka kankane komai, inda waɗanda aka ci zarafinsu aka yi lalata da su, suke shiga matsanancin hali idan suka fito fili suka yi magana.
Batun ta, ya sa sojoji gudanar da bincike na cikin gida, da ya sa aka gano ƙorafe-ƙorafe irin wannan har fiye da 100. Daga bisani ma`aikatar tsaro ta fitar da takardar ban-haƙuri ga Gonoi.
Sonia Guajajara, Brazil
Ƙaramin Minista
Fitacciyar Babbar mutum a Ƙungiyar fafutukar kare haƙƙin 'yan ƙasa a brazil a shekarar 2023 Sonia Guajajara ta zama mace ta farko minister ta 'yan ƙasar akayi ta jinjinawa a matsayin na]I mai tarihi da sabon shugaban ƙasa da aka zaɓa Lula da Silva ya yi.
Ta lashi takobin mayar da yaƙi da laifuka na muhalli daya daga cikin manyan abubuwa da za ta maida hankali a kansu.
Iyayen da suka haifi Guajajara a Araribóia basuyi karatu ba, a yankin ne ta samu wajen zama a kujeru da ke gaba a batun yaƙi da abubuwan da taɓarɓarewar yanayi ke haifarwa a an tsire-tsire da shuke-shuke.
Ta bari domin zuwa ta karanci adabi, tana aiki a matsayin malamar jinya ko malamar makaranta, ta kuma shiga lamuran gwagwarmaya a shekarar 2022 ta zama mace ta farko 'yar ƙasa da aka taɓa samu 'yar siyasa ta jihar São Paulo.
Ya kamata muyi tunani a kan yadda za mu ɗaukaka batun yanayi da yaƙi da wariyar muhalli domin kuwa mutanen da suka fi dacewa su kare muhalli sune mutane na farko da ɓarnar tafi shafa. Mu mutane 'yan ƙasa mune ainihin masu kare dukkan tsire-tsire da shuke-shuke da kuma rayuwa.
Sonia Guajajara
Renita Holmes, AMURKA
Mai gangamin samar da gidaje.
Mazauniyar Miami da ke makwabtaka da Haiti, Madame Renita Holmes ita ce daraktar da ta samar da O.U.R. Homes (Gidajenmu), kwararru kangaren kasuwanci na kaddarori a jihar Florida taAmurka.
Tana gangami a kan hakkin samun gidaje ga al`umomin da aka ware su, ciki har da wadanda matsalar yanayi ta shafa a lokacin da teku take sa kara tsadar kaddarori a yankunan da ke nesa da tekun.
Ta girma a hannun mahaifiya mai `ya`ya 11, Holmes babba ce da ke rayuwa da nakasa.
Tana cikin wata Cibiya ta Cleo Institute's Empowering Resilient Women programme, ta garfafa mata masu kwazo da ke neman fadakarwa domin daukar mataki a kan yanayi ta amfani da ilimi na kimiyya. Tana taimaka wa kananan dillalai na gidaje a kan batutuwa da suka jihanci `yan Afirka da suke Amurka da kuma lamura na mata.
Akwai fata a gane muhimmancin hadin kanmu a matsayinmu na mata ginshidan duniya. A tsaye muke, da karfinmu, Allah Yay i mu, mu yi reno; mu dauki mataki da kuma kula.
Renita Holmes
Nataša Kandić, Serbia/Sabiya
Lauya kuma `yar gwagwarmayar kare haƙƙoƙin bil`Adama.
Tun lokacin da yaji ya karke a tsohuwar Yugoslabiya a farko-farkon shekarun 1990, Nataša Kandić ta tattara bayanai a kan aika-aikar da aka aikata a lokacin yaji ciki har da fyade, da azabtarwa da kisan gilla da dacewar mutane da karfi da yaji.
Ta wakilci iyalan na wadanda abin ya shafa daga al`umomi daban-daban a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka a Belgrade kuma tana cikin wata kungiya da ta yi nazarin tsarin gwamnatin mai wandon karfe na Sabiya Slobodan Milosevic ga Kosovo da idon basira.
Kandić ce ta kafa cibiyar shari`a ta Bil`Adama, da akan yabe ta, saboda bincike ba n a son kai ba da ta gudanar a kan laifuka na yaji.
Ta taimaka wajen tsara hawancen sasantawa na RECOM, da ya budaci nuna gaskiya a zahiri a game da yade-yaden Balkan da aka kiyasta mutane 130,000 suka mutu.
Rukshana Kapali, Nepal
Yar gwagwarmayar samar da muhalli
Wakiliya a ƙungiyar Newa ta ƴan asalin Nepal, mai gwagwarmayar kare haƙƙoƙin jinsin ɗan'adam Rukshana Kapali ta yi fama da ƙarancin bayanai a game da ko ita wace ce a lokacin da ta ke girma.
Ta miƙe tsaye wajen ilmantar da kanta a jinsina daban-daban da kuma batun jima'i.Ta fito a matsayin yarinya kuma take ta kwarmato a soshiyal midiya a kan haƙƙokin abubuwan da ba'a saba gani ko ji ba.
A yanzu haka tana aji uku a karatun lauya kuma tana cikin masu ɗaukaka batun haƙƙoƙi ɓangaren doka da kuma kundin tsarin mulki ga ƙungiyar LGBTQ+ da suke Nepal.
Kapali ta fito daga ƙabilar Newa da a ka daɗe a na nuna wa wariya, mutanen Jugi, da faɗa da korar mutanen Jugi daga gidajensu na gargajiya.
Sofia Kosacheva, Rasha
Mai aikin Kashe Gobara
Mai koyar da waƙoƙi, Sofia Kosacheva ta sake amsa wani kiran lokacin da ta haɗu da wata ƙungiya ta ƴan kwana-kwana a shekarar 2010.
Ita kanta ta zama ma'aikaciyar kashe gobara, kuma ta ƙirƙiro da wata al'umma domin horar da ƴan sa kai domin taimakawa wajen kasha gobarar daji a Rasha. Wannan ya yi sanadiyyar kafa ƙungiyoyin ƴan-sa-kai fiye da 25 a sassan ƙasar.
Ta taimaka wajen kashe ɗaruruwan gobara a sassan Rasha, ta kuma haɗa gwiwa da Greenpeace, har zuwa lokacin da a ka sa sunan ƙungiyar da ba a so, reshen ta kuma na Rasha aka rufe shi.
Har ila yau Kosacheva ta ƙirƙiro da wani dandali na intanet na ƴan kwana kwana masu sa kai na daji wanda aka ɗauke ta a matsayin cikakken rumbun bayani na intanet a Rasha da ke ɗauke da bayanai a kan rigakafin wutar daji da kuma yadda za a iya kashe ta.
Duk wata gagarumar nasara ta na farawa ne daga ƴar ƙarama, za a iya kallon mu a raina mu a matsayin masu kawo sauyi a duniya, amma dole mu fara da sauyin da za mu iya yi a tsakanin junanmu.
Sofia Kosacheva
Monica McWilliams, Birtaniya
Tsohuwar ƴar siyasa da wanzar da zaman lafiya
A wanna shekarar a ke cika shekara 25 tun lokacin da a ka sa hannu a yarjejeniyar Northern Ireland's Good Friday Agreement. Monica McWilliams ta taka muhimmiyar rawa a matsayin jagorar tattaunawa lokacin tattaunawar zaman lafiya tsakanin jam'iyyu da ta kai ga yarjejeniyar.
Tare da ita a ka kafa ƙawancen ƙungiyoyin matan arewacin Ireland wacce jam'iyyar siyasa ce da ta tabo kowane ɓangare da ta ɓullo da manyan tanade-tanade na yarjejeniyar zaman lafiya.
A ka zaɓe ta a majalisar dokoki ta farko ta Northern Ireland kuma a matsayin babbar kwamishiniya ta hukumar kare haƙƙoƙin ]anAdam ta arewacin Ireland, ita ta tsara shawarwarin da ke cikin ƙudurin dokar kare haƙƙoƙin Arewacin Ireland.
Yanzu haka McWilliams ta na aiki a matsayin kwamishina ta ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da a ka haramta kuma ta yi wallafe-wallafe masu yawan gaske a kan cin zarafin mata.
Najla Mohamed-Lamin, Yammacin Sahara
Mai kare haƙƙoƙin mata da gwagwarmayar kare yanayi
Wacce ta kafa Cibiyar ɗakin Karatu ta Almasar Najla Mohamed-Lamin tana so ta ilimantar da mata da yara a kan lafiya da muhalli a sansanoni na `yan gudun hijira da ke Saharawi a kudu – maso yammacin Aljeriya.
Asalinsu daga Yammacin Sahara, tsohon waje da ke ƙarƙashin mulkin Sifaniya ƙarƙashin mamayar Marokko tun 1975, an tilasta wa iyalanta barin ƙasar bayan tsere wa tashin hankali.
Wacce aka Haifa kuma aka rene ta a sansanonin, Mohamed-Lamin ta koyi Imgilishi a lokacin da take yarinya, da aka fassara domin wakilai na ƙasashen waje, kuma ta iya zuwa karatu ƙasashen waje bayan ta biya ku]inta na makaranta.
Bayan ta kammala karatun a fannin nazarin ɗorewar ci gaba da mata, sai ta dawo sansanonin domin taimaka wa `yan gudun hijira na Saharawi su fiye da 200,000 a ɓangaren ruwa da abinci da sauyin yanayi ya sa lamarin ya taɓarɓare.
Dole ne mu ɓullo wa matsalolin da sauyin yanayi yake haddasawa a yankin sahara ta bayan gida, da muke fama da ganin ambaliya da goguwa suna tusa mana gidaje a kai-a kai, sannan mutanenmu suna shan wahala saboda tsananin zafi. Dukkan wa]annan suna aukuwa a lokacin da mutanenmu ba su ba da wata gudunmawa ko ]aya ga matsalolin na yanayi ba.
Najla Mohamed-Lamin
Ulanda Mtamba, Malawi
Mai yaki da yi wa yara auren wuri.
Ulanda Mtamba ta girma ne a wata al`uma da ke Lilongwe, Malawi, da ke ba da tallafin da bai wuce cikin cokali ba, ga ilimin mata, da yara masu yawan gaske ake matsa musu fita daga makaranta domin yi musu aure kafin su kai shekara 18 da haihuwa.
Mtamba ta ƙalubalanci matsayin al`umar kuma ba ta tsaya ga kammala karatun jami`a kawai ba, ta kai ga samun digiri na biyu.
Ta mai tsaye wajen tilasta aiki da dokokin da ake da su, da suke kare yara mata daga daga yi musu auren wuri, da kuma zuba jarin jari domin magance matsaloli na lafiya da suke da nasaba da samun juna biyu da wuri.
A yanzun haka tana aiki a matsayin darakta ta AGE Africa ta Malawi wacce kungiya ce da take nemar damabiri guda ta samun shiga makarantar sakandare ga dukkan `yan mata da suke nahiyar.
Tamar Museridze, Georgia/Jiyojiya
Yar Jarida
Tamar Museridze wacce fitacciyar fuska ce da ke karanto labaru daga talabijin na Georgia tun tana `yar shekara 17– har ila yau an santa a matsayin Tamuna – komai yana tafiya mata dai-dai. Sai dai da ta kai shekara 31, sai rayuwa ta yi matuwar sauya mata. Lokacin da ta gano ashe ba a hannun ainihin iyayenta da suka haife ta take ba.
Ta hakura da komai ta dudufa ga neman ainhin iyyenta da suka haife ta. Kuma a lokacin da take neman su ta samu shaifar da ke nuna akwai babbar kasuwar bayan fage ta daukar yara marayu da ire-irensu domin renonsu da ke gudana a Georgia tun shekarun 1950.
Ta bude dandalin fesbuk a kan wannan matsala da ya haifar da tattaunawa ta kasa a game da yadda wasu iyalai ke daukar yara tun suna jarirai su mayar da su nasu ba bias ka`ida ba. Yawanci jarirai da aka dauko daga asibitocin masu haihuwa
kungiyar Museridze ta taimaka wajen sada iyalai 800, sai dai har yanzun tana neman ci gaba da neman nata iyayen.
Neema Namadamu, Jumhuriyar Dimukraɗiyyar Kongo
Mai fafutukar kare haƙƙoƙin masu lalurar nakasa.
Ƙungiyar Hero Women Rising, ko Mama Shuja, tana da manufar kyautata jin da]in mata da yara `yan mata a DRC.
Mai gwagwarmayar kare haƙƙoƙin masu lalurar nakasa Neema Namadamu ta kafa ƙungiyar ta ta karkara da take amfani da ilimi da fasaha wajen ɗaukaka muryoyin mata da koya musu yadda ake gwagwarmayar neman haƙƙoƙinsu.
Wadda aka haifa a yankin karkara na gabashin Kongo, Namadamu ta kamu da ciwon Inna a lokacin da take ƴar shekara biyu. Ita ce mace ta farko da ke da lalurar nakasa daga ƙabilarsu da ta kamala karatun jami`a.
Ta zama ƴar majalisar dokoki kuma ita ce mai ba da shawara ga ministan jinsi da iyali ta ƙasar.
Michelle Obama, Amurka
Babbar lauya, marubuciya kuma ƴar gwagwarmaya
Uwargidar Tsohon Shugaban Amurka, Michelle Obama ita ce ta samar da ƙungiyar Bai wa Ƴaƴa Mata Dama wato Girls Opportunity Alliance, wadda take tallafawa tare da ba da goyon baya ga ƙungiyoyi da ke yankunan karkara a faɗin duniya da ke aiki tuƙuru wajen tabbatar da ƴaƴa mata sun samu ilimin da suka cancanci su samu.
Wannan ya ɗora a kan wani shiri mai suna Let Girls Learn, wato a bar ƴaƴa mata su yi ilimi da Obama ya ƙaddamar inda a matsayyinta na Uwar Gidar Shugaban ƙasa ta yi amfani da ɗinbin dabaru na gwamnati wajen taimaka wa ƴan mata da ke faɗin duniya samun ingantaccen ilimi.
A matsayinta ta Uwar Gidar Shugaban ƙasa ta jagoranta tare da samun nasara a wasu manya-manyan tsare-tsare guda uku: Mu tashi tsaye domin taimaka wa iyaye renon ƴaƴansu su tashi cikin ƙoshin lafiya; Haɗa ƙarfi domin tallafa wa jami`n Amurka, da gwaraza, da iyalansu; da Kaiwa Ga Babban Matsayi - da har yanzun take aiki a kai - ƙarfafa wa mutane matasa gwiwar ci gaba da neman ilimi mai zurfi.
Sepideh Rashnu, Iran
Marubuciya kuma mai zane
Sepideh Rashnu ta shahara a Iran saboda nuna adawa da dokar tilasta saka hijabi.
Biyo bayan wata hatsaniya a cikin wata motar bas da wata mata da ke tilasta mata rufe kai, an kama ta.
Yayin da ake tsare da ita, ta fito a gidan talabijin na kasar tare da rauni a fuska, "inda ta nemi gafara kan abin da ya faru". Hakan ya faru ne a watan Yulin 2022, makonni kadan kafin Mahsa Amini mai shekaru 22 ta mutu a hannun jami'an 'yan sandan Iran.
A farkon wannan shekarar ne aka gurfanar da Rashnu a gaban kuliya bayan ta wallafa hotunan ta ba lullubi. Ta ce an dakatar da ita daga jami'a saboda fafutukar da take yi.
A halin yanzu ta fita daga gidan yari kuma tana ci gaba da bijirewa dokokin tilasta saka hijabi.
Bernadette Smith, Turtle Island/ Canada
Ƴar gwagwarmayar kare iyalan waɗanda suka ɓata
Sakamakon ɓacewar ƴar'uwarta a shekarar 2008, Bernadette Smith ta yi neman amsa har ta gaji.
Ta zama jagorar gwagwarmayar kare iyalan mata da ƴan mata ƴan asalin yankin da ko dai suka ɓace ko aka kashe su a faɗin Canada tare da kafa wata ƙungiyar ƙawance domin tafiyar da ɗaukar mataki tare da kuma neman amsa.
Har ila yau tana cikin waɗanda suka kafa "Drag the Red", ƙungiya da ke laluben gawarwaki ko wata shaida na mutanen da suka ɓace.
A kwanan nan aka zaɓi smith a matsayin ƴar majalisar dokoki ta Manitoba karo na uku kuma ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko cikin matan ƙasar na farko da aka naɗa a matsayin minista a lardin. Yanzu haka tana matsayin ministar gidaje da kula da marasa muhalli.
Iryna Stavchuk, Ukraine
Mai bada shawara a ɓangaren tsare-tsare na yanayi
Babbar kwararriya a ɓangaren tsare-tsare na yanayi, Iryna Stavchuk a 'yan kwanakinnan ta shiga gidauniyar European Climate Foundation a matsayin manajar Ukrain, wacce ke da babbar manufar tsara hanyoyin samun mafita ta amfani da yanayi daga matsalar da yaƙi ya haifar a ƙasarsu.
Kafin kasancewa a wannan matsayi ta yi aiki a gwamnatin Ukrain a matsayin mataimakiyar minister muhalli daga 2019 zuwa 2022 kuma itace ke da haƙƙin sauya tsare-tsare a kan muhalli, da ci gaban turai, da dangantaka da ƙasashen duniya, da bunƙasa aikin gona.
Stavchuk har ila yau tana ɗaya daga cikin wanda suka ƙirƙiro fitattun ƙungiyoyi wanda ba na gwamnati ba guda biyu akan muhalli - Ecoaction da ƙungiyar Kyiv Cyclists' Association (U-Cycle) – kuma ta gudanar da ƙungiyoyi daban-daban na al'umma da suke aiki akan batutuwa na sauyin yanayi.
Akinmu shi ne yin iya ƙoƙarinmu a waje da yanayin da muke ciki. Ina kiyayewa da kalaman Saint Francis na Assisi: "Fara da abun da yake wajibi, sannan ka yi mai yiwuwa, sai ka ga nan da nan kana yin abunda ba zai yiwu ba."
Iryna Stavchuk
Gloria Steinem, AMURKA
Jagorar Kare Mata
A matsayinta ta jagorar gwagwarmayar kare mata tun shekarun 1970, an san Gloria Steinem tare da yaba wa gudunmawarta ga gwagwarmayar mata a fa]im duniya tsawon shekaru.
Steinem ta yi gwagwarmaya a kan batutuwa na daidaito a matsayinta ta ƴar gwagwarmaya, ƴar jarida, marubuciya, lakcara kuma mai Magana da yawun mata a kafofin watsa labaru.
Har ila yau tana cikin waɗanda suka kirkiro da Mujallar Ms. Magazine, wacce aka soma ya]ata a 1971 kuma har zuwa yau ana ci gaba da wallafata, kuma ake ɗaukarta a matsayin mujalla ta farko da take fitowa a Amurka da ke kawo batutuwa a kan gwagwarmayar kare haƙƙoƙin mata a muhimman batutuwa.
Tana da shekara 89, Steinem ta ci gaba da aikinta ga duniya ta tallafawa da kuma goyon bayan da take ba da wa ga kungiyoyi kamar su cibiyar kafofin watsa labaru na mata wato Women's Media Center, kawance ko gamayyar neman adalci na ERA Coalition and Equality Now.
Summia Tora, Afghanistan
Ƴar gwagwarmayar kare haƙƙoƙin ƴan gudun hijira
Dosti Network wata ƙungiya ce da a ka sadaukar da ita ga samar da muhimman kayayyakin aiki da kuɗaɗe da bayanai ga ƴan ƙasar Afganistan- a cikin Afganistan da kuma waɗanda suke zaune a matsayin ƴar gudun hijira – aka ƙaddamar saboda mayar da martani ga karɓe abubuwa da Taliban ta yi a 2021.
A matsayinta ta ƴar gudun hijira ita kanta, Summia Tora ta fahimci ƙalubalen da ɗai-ɗaikun ƴan gudun hijira ke fama da su.
Ayyukanta sun mayar da hankali a kan sake tsugunar da ƴan gudun hijira da kuma samar da ilimi ga ɗaliban da rikici ya shafa.
Sanin muhimmancin da ilimi yake da shi wajen kawo ci gaba, Tora ta yi aiki da ƙungiyoyi kamar su Majalisar Ɗinkin Duniya, da Bankin Duniya da Giduniyar Malala, da sauran su, ta wadannan ƙawance ta sama nasarar taimakawa samun ilimi musamman ga ƴan gudun hijira da mata da yara ƴan mata a yanayi na gaggawa.
Xu Zaozao, Sin
Mai gangamin adana ƙwayayen haihuwa na mace
A 2018, ta nemi a kwashe mata ƙwayayenta na haihuwa don adana su a wani asibitin gwamnati da ke Beijing. Sai dai Xu Zaozao, wadda mace ce maras aure, an sanar da ita cewa mata masu aure ne kawai ake musu haka a ƙasar Sin wato Caina.
Saboda haka ta maka asibitin a kotu mataki irinsa na farko da aka taɓa ɗauka don kare haƙƙin mata da ba su da aure a ƙasar ɓangaren kwashe musu ƙwayayen haihuwa.
Wannan shari`a irin ta ta farko da aka soma ta a watan Disamba na 2019, labarinta ya mamaye kanun jaridu da sauran kafofin watsa labaru, a daidai lokacin da ake ta damuwa da batun ana samun ƙarancin haihuwa a ƙasar.
Har yanzun ana zaman jiran yanke hukunci , sai dai ma`abuta ilimi suna ta nazartar wannan shari`a ta Xu a fagen shari`a, da na likitanci, da sauran fagage. Har zuwa yau, ita ke ci gaba da zama fitacciyar mai fafutukar kare haƙƙin mata da ba su da aure ɓangaren batun haihuwa da ƴancin jikinsu.
Kimiyya, da Lafiya da Fasaha
Basima Abdulrahman, Iraƙi
Ƴar kasuwar tsarin gine-gine da ba shi da illa ga muhalli da yanayi
A 2014, da kungiyar da'awar kafa ƙasar Muslunci ta Islamic State ta ƙwace yawancin sassan garinsu, IraƙI ta na karatu a jami'a a amurka.
An lalata garuruwa da dama sakamakon fadan, amma da Abdurrahman ta dawo gida bayan ta kamala digirinta na biyu a ɓangaren injiniyanci na tsare tsare, sai ta ga hanyar taimakawa.
Ta kafa KESK, yunƙuri na farko a kasar Iraƙi, da a ka sadaukar dashi ga yin tsarin ginin da ba shi da illa ga muhalli da yanayi. Ta gano cewa samar da irin waɗannan gine-gine na nufin haɗa sabbin dabaru na wadataccen makamashi da kayayyaki na gine-gine na gargajiya na iraƙi.
Ta duƙufa wajen tabbatar da gine-gine da ake yi yau ba su da wata illa ga kyautata jin daɗin al'umomi na nan gaba.
Nakan damu kwarai a game da matsalolin yanayi , nakan kasance cikin tunanin yadda mutum zai kasance cikin kwanciyar hankali, ba tare da ya kasance wani bangare na laluben hanyoyin rage matsalar ba.
Basima Abdulrahman
Amina Al-Bish, Syria
Mai aikin ceto
A lokacin da yaƙin basasa na ƙasar Syria ya ƙazance a 2017, Amina Al-Bish ta yanke shawarar zama ɗaya daga cikin mata ta farko ƴan sa kai na masu tsaron farar hula, wata ƙungiya ce ta ƴan sa kai wanda aka fi sanin ta da "White Helmets", da ke da fatan ceto rayuka da kuma samar da agajin farko ga farar hula da suka ji rauni.
Daga bisani Amina ta ta sa kanta aikin ceto waɗanda girgizar ƙasar da ta shafi Syria ta turkiya a watan Fabarairu na shekarar 2023 ta shafa, da ta ɗaiɗaita ƙasashe maƙwabta sannan da iyalanta suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai.
A yanzu haka Al-Bish tana ayyuka domin kyautata rayuwar sauran mata da ke al'ummarta a arewacin siriya inda yaƙi ke ci gaba. Ta na karatun digiri a ɓangaren sha'anin kasuwanci, ta kuma bayyana cewa burinta shi ne ta shiga aikin gina zaman lafiya a Syria.
Sara Al-Saqqa, Yankunan Falasɗinawa
Babbar likitar tiyata
Likitar tiyata ta farko a Gaza, Dr Sara Al-Saqqa tana aiki a babban asibitinta, Al-Shifa.
Ta kasance tana amfani da shafinta na Instagram wajen rubuta yadda za a bai wa mutane agajin gaggawa a tsakiyar yaki. Asibitin Al-Shifa ya samu mummunar barna yayin da Isra'ila ke ayyukan aiki kan Hamas.
Al-Saqqa dai ta dade tana yaɗa labaran rashin wutar lantarki, man fetur, ruwa da abinci, wanda ya hana asibitin kula da majinyata. Sai da ta bar Al-Shifa jim kadan kafin sojojin Isra'ila su kai farmaki asibitin, a wani harin da rundunar tsaron Isra'ila ta bayyana a matsayin harin da aka kai wa Hamas.
Al-Saqqa ta karanta likitanci a jami'ar Islamic University of Gaza da kuma karatun fiɗa a Queen Mary University London. Yanzu akwai sauran waɗanda suka yi karatun fiɗa a yankin Gaza, waɗanda ke koyi da ita.
Bayang, China
Yar gwagwarmayar rubuta bayanai a takardar diyari da kuma ɗorewa
Tun shekarar 2018, Bayang ke ta adana bayanai a kan tsire-tsire da halittu a cikin diyari, da sa ido a kan ire-iren halittu da tsire-tsire na gida, da sauye sauye ga kafofin samun ruwa, da rubuta yanayi, da kuma sa ido saosai a kan shuke-shuke.
Tun shekarar 2018, Bayang ke ta adana bayanai a kan tsire-tsire da halittu a cikin diyari, da sa ido a kan ire-iren halittu da tsire-tsire na gida, da sauye sauye ga kafofin samun ruwa, da rubuta yanayi, da kuma sa ido saosai a kan shuke-shuke.
Bayang tana cikin ƙungiyar mata ta muhalli mai suna Sanjiangyuan, kuma mai gwagwarmayar kare lafiya da ɗorewa a cikin al'ummanta.
Ta koyi ƙwarewa daban-daban ɓangaren kusantar ƙananan halittu da shuke-shuke a muhalli ciki harda ma shafawa a leɓe, da sabulu, da jakunkuna – domin kare kafofin samun ruwa na gida da ƙarfafawa jama'a gwiwar shiga lamuran na kare muhalli.
Susan Chomba, Kenya
Ƙwararriya a ɓangaren kimiya
Yanzu haka darekta a Cibiyar Albarkatun Duniya (WRI), Susan Chomba ta ce abin da ta fuskanta na talauci a lokacin kuruciya a gundumar Kirinyaga da ke tsakiyar Kenya ya sa ta taimaka wajen inganta rayuwar wasu.
Ta fi damuwa da kanta game da kare gandun daji, maido da shimfidar wurare da sauya tsarin abinci na Afirka.
Tun daga dazuzzukan Kwango zuwa busasshiyar Sahel ta yammacin Afirka, da kuma gabashin Afirka, Chomba na yin aiki tare da ƙananan manoma, musamman mata da matasa, domin taimaka musu wajen cin gajiyar filayensu.
Tana haɗa kai wajen yaɗa ƙwarewar ta ga gwamnatoci da masu bincike don gina al'ummomin da suka fi dacewa ta fuskar haɓaka canjin yanayi.
Rashin aikin shugabannin duniya ya fi shafa ta, musamman daga manyan masu ƙasashen da suka fi fitar da sinadarai masu gurɓata muhalli, wadanda kuma suke da karfin tattalin arziki na canza hanya amma kudi da mulki da siyasa sun hana su. Don sarrafa waɗannan abubuwan, na binne kaina cikin ayyuka a ƙasa, ina aiki tare da mata da matasa a duk faɗin Afirka kan kariyar yanayi da maidowa, canza tsarin abinci da canza manufofinmu.
Susan Chomba
Leanne Cullen-Unsworth, Birtaniya
Mai Ilimin Kimiyyar Teku
An san ciyayi/ciyawa da iya adana sinadarin carbon da samar da ƙananan shuke-shuke domin kifaye, sai dai wasu halittu da suke ƙarƙashin teku an jefa su cikin wani mawuyacin hali.
Leanne Cullen-Unsworth tana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa a yanzun kuma Babbar Jami`ar Aikace-Aikacen Seagrass, wani tsari na farko na Ingila na maido da ciyayin teku a cikin tsari mai ma`ana.
Tsarin ya sauƙaƙa matakan ta amfani da mutum-mutumi da ake sarrafa shi daga can nesa, domin shuka iri na shuke-shuke da kuma samar wa sauran ƙasashen duniya, hanyoyin kare shuke-shuke na ƙarƙashin tekunansu.
A matsayinta ta ƙwararriya a fage daban-daban na kimiyya da take da ƙwarewa ta fiye da shekara 20 a binciken ruwayen teku, Cullen-Unsworth ta duƙufa ga adani da kariya ɓangaren kimiyya.
Akwai gagarumin aiki a gaban dukkan wani da ke son cimma abubuwa shi kaɗai. Sai dai mutane suna aiki tare da kuma musayar ra`ayi. A nawa ɗan ƙaramin ɓangaren, Na san za mu iya farfaɗo da muhimman halittu da kare su domin dukkan alfanun da suke bayarwa ga duniyarmu da al`umarmu.
Leanne Cullen-Unsworth
Canan Dagdeviren, Turkiyya
Mai ilmin Kimiyya
Ɗan galadimar farfesa a cibiyar fasaha ta Massachusetts Institute of Technology (MIT) a Amurka, Canan Dagdeviren a ƴan kwanakin nan ta ƙirƙiro da wata na'ura ta ɗaukan hoto da ke saurin gano cutar sankarar mama tun ta na ƴar ƙarama.
Ta sama wannan ƙarfin gwiwa ne daga wata ƴar uwarta da a ka gano ta na da sankarar mama a lokacin da take da shekaru 40 a duniya duk daa na kula da ita a kai- a kai ta rasu bayan wata shida.
A lokacin da take gefen gadon jinya na 'yar uwan ta ta, Dagdeviren ta zana wata na'ura da za a iya sa ta a cikin rigar mama a dinga barinta na wani lokaci domin taimakawa ɗaiɗaikun jama'a kauc ewa kasadar kamuwa da ciwon sankarar mama. Fasahar za ta iya taimakawa wajen ceto miliyoyin rayuka.
Izabela Dłużyk, Poland
Mai ɗaukar Sauti
Ɗauke da na'urar ɗaukar sauti a hannu, Izabela Dłużyk ta bazama neman sautuka na daban na Białoweiza, ɗaya daga cikin dazuna na Turai da a ka ware mafi tsufa a Poland.
Wannan aiki da take yin a ɗaukar sauti abu ne da ba'a saba gani ba bawai don saboda ta na matashiya a sana'ar da maza ne suka fi yin kakagida a cikin ta, sai dai saboda tun da aka haife ta makauniya ce.
Dłużyk tun lokacin da iyayenta suka ba ta na'urar naɗar sauti tun tana shekara 12 ta zama mai mayar da hankali na musamman ga kukan tsuntsaye kuma ta ke iya gano nau'in tsuntsaye daban-daban ta irin kukansu tun da ba gani take yi ba.
Ta yi imanin cewa dama ce ta yaɗa dukkan abubuwa masu kyau da za a iya ji daga sautuka ba tare da wani banbanci da muke iya gani a tsakinmu ba.
Marcela Fernández, Colombia
Jagoran zuwa gudanar da bincike
Daskararren ruwan kogi yakan zama muhimmin kafar samun ruwa mai kyau ga al`umomi, sai dai a Colombia sai ɓacewa suke yi.
Wadda ta ƙirƙiro da Marcela Fernández da abokan aikinta da ke NGO Cumbres Blancas (White Peaks) suka ɗora gangamin faɗakarwa a kan batun, da bayyanin daskararrun ruwaye 14 da ada ake da su, guda shida kaɗai suka yi saura, su ma suna cikin ha]ari.
Ta hanyar tafiya ta gudanar da bincike na kimiyya, da kuma tattara ayari na masu hawa duwatsu da masu ɗaukar hoto, da masu ilimin kimiyya, da masu aikin zane-zane, Fernández ta sa ido a kan sauye-sauyen tare da ɓullo da ƙwararan hanyoyi na rigakafin asarar daskararrun ruwayen.
Da aikinta na kusa-kusa, "Pazabordo" (Peace on board), har ila yau ta yi tafiya zuwa yankunan da ƙazamin rikici ya fi shafa a taƙaddamar makamai ta cikin gida da ta shekara 50 ana fama da ita a Colombia.
Daskararrun ruwaye sun koya mun yadda zan ɓullo wa baƙin ciki, da rashin … Da ka ji su, ka san cewa asararsu ɓarna ce da ba za mu iya sauya ta ba, amma za mu iya ba da gudunmawa da barin wata alama..
Marcela Fernández
Timnit Gebru, Amurka
Ƙwararriya kan ƙirƙirarriyar basira
Fitacciyar mai ilimin kwamfuta ɓangaren ƙirƙirarriyar basirar ɗan'dam, Timnit Gebru itace ta ƙirƙiro kuma ta kasance shugabar cibiyar bincike akan ƙirƙirarriyar fasahar ɗan'adam, da aka kafa a matsayin sarari na ƴanci, binciken ƙirƙirarriyar fasaha ta al'umma da babu ruwanta da katsalandan na manyan fasahohi.
Ta soki bambancin da a ke nunawa ga ƙirƙire-ƙirƙire da kuma zama ɗaya daga cikin wanda suka kafa wata ƙungiya da ba ta samun riba ba da ke aiki tuƙuru domin sanya baƙaƙen fata a cikin ƙirƙirarriyar fasahar ɗan'adam.
Mai ilimin fasahar kwamfutar haifaffiyar ƙasar Habasha, tana cikin ƙungiyar AddisCoder, wadda ke koyar da abubuwa na kwamfuta ga ɗalibai ƴan ƙasar Habasha.
A lokacin da take aiki a matsayin ɗaya daga cikin jagororin ayarin ƙirƙirarriyar fasahar ɗan'adam na Google a 2020, ta na ɗaya daga cikin wanda suka rubuta wata muƙala da ta taɓo batutuwa a kan tsarin harshen ƙirƙirarriyar fasaha, ciki har da irin bambancin da ake nuna wa ƴan tsiraru da mutanen da ake yi wa danniya da kuma wurare.
Rahoton ya sanya ta bar kamfanin – a lokacin da kamfanin ya mayar da martanin cewa muƙalar ta yi watsi da muhimmancin bincike ta kuma ce Gebru ta ajiye aiki. Sai dai Gebru ta ce an kore ta ne saboda ta taɓo abubuwa na nuna bambanci a wajen aikin.
Claudia Goldin, Amurka
Masaniyar Tattalin Arziki Kuma wadda ta samu lambar yabo ta Nobel
Ba'amurkiya masaniyar tarihin tattalin arziki kuma masaniyar tattalin arziki ɓangaren ƙwadago, Claudia Goldin ta samu lambar yabo ta Nobel ta wannan shekaran ɓangaren tattalin arziƙi, saboda aikin da take yi na ƙarfafa mata da kuma gwagwarmayar kawar da giɓin albashi tsakanin maza da mata.
Ita ce mace ta 3 da ta samu wannan lamba, kuma ta farko da ba ta raba wannan lamba da abokan aikinta maza ba.
Goldin farfesa ce ta Henry Lee ɓangaren tattalin arziki a jami'ar Harvard, kuma ta gudanar da bincike a ɓangarori daban-daban, kamar rashin dai-daiton kuɗaɗen shiga, da ilimi, da kuma zuwa ci-rani.
Wasu daga cikin fitattun muƙalolin da ta rubuta sun duba tarihin ƙoƙarin da mata suke yin a zama masu sana'a da iyali, da kuma tasirin shan ƙwayoyin ƙayyade iyali a sana'o'in da mata sukeyi da kuma yanke shawara a kan aure.
Trần Gấm, Vietnam
Mai kasuwancin makamashin gas da ake samu daga tsirrai
A shekarar 2012, Trần Gấm ta soma ɓullo da tsarin hanyoyin samun makamashi da bashi da illa ga yanayi a gonaki da ke Vietnam.
Trần Gấm mai 'ya 'ya biyu ta ga giɓi a kasuwar saboda haka ta soma kasuwancin sawa da kuma gudanar da makamashin gas da ake samu daga shuke-shuke a Hanoi, daga bisani ta faɗaɗa kasuwancin nata zuwa larduna guda uku maƙwabta.
Wannan aikin nata ya taimakawa manoma rage maƙudan kuɗin da suke kashewa ta hanyar maida kashin shanu da na alade da ciyawa da sauran kayayyaki na bola zuwa makamashi na gas – da ake dauka hanya mai ɗorewa ta samun makamashi fiye da gas da aka saba dashi – da za a iya amfani dashi a matsayin makamashi na girki da kuma gudanar da gida.
Kasuwanci irin na Trần ya haɗa da al'umomi na gida da kuma samar da goyon baya da ake buƙata na siyasa domin sauƙaƙa matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa.
Dole mu tafi da rayuwa kuma dole mu kasance cikin ƙoshin lafiya, saboda haka nayi kokarin in iya haƙuri da kuma kare waɗanda ake ƙauna ta hanyar inganta lafiyarmu ta hanyar motsa jiki da cin abinci mai gina jiki da kuma samun bacci akai-akai. Har ila yau na ƙarfafa wa jama'a gwiwar su tafiyar da rayuwa ta amfani da kayyaaki na gida, su shuka 'ya'yan itatuwansu da ganyeyyaki da kuma yaƙi da amfani da magungunan kasha }wari a kan ganyayyakinmu.
Trần Gấm
Anna Huttunen, Finland
Ƙwararriya a ɓangaren illar da hayaki da ke fita a ababen hawa ke haifarwa
A matsayinta ta mai neman ƙarin ilimi angaren sufuri Anna Huttunen ta miƙe wajen gwagwarmayar samar da hanyar sufuri tsabtatacciya da bata tattare da hayakin ababen hawa a birnin Lahti na ƙasar Finland, da aka bayar da European Green Capital 2021.
Ita ta jagoranci tsarin kasuwancin hayakin da ke fita a ababen hawa ke haifarwa na birnin- dandalin app na farko a duniya da zai bai wa 'yan ƙasa dmar samun kiredit ta hanyar amfani da sufurin da ba shi da matsala ga muhalli kamar su keke ko sufuri na jama'a.
Ta na aiki a matsayin mai bada shawara ɓangaren yanayi a birane ga NetZeroCities, wata ƙungiya da ke taimakawa birane a turai a ƙoƙarin da sukeyi na cimma burinsu na tabbatar da lafiyayyan yanayi nan da shekara ta 2030.
Huttunen ta na da burin samar da wasu hanyoyin masu ɗorewa na kai komo kuma ta duƙufa ga burinta na a koma ga hawa keke wanda ta ke ganin shi ne hanyar sufuri nan gaba a birane.
Birane da ke faɗin duniya suna cike da mutane masu ban mamaki da suka duƙufa wajen samar da rayuwa mai ɗorewa ga jama'arsu. Ka yi naka ɓangaren ka shiga domin zama cikin wannan cigaba!
Anna Huttunen
Gladys Kalema-Zikusoka, Uganda
Likitan Dabbobi
A matsayinta ta likitar dabbobi da ta samu lambobin yabo a Uganda kuma mai kare yanayi, Gladys Kalema-Zikusoka ta na aiki domin ceto goggon biri da ke tsaunukan ƙasar da suke neman ƙarewa da sauyin yanayi ya shafi inda suke rayuwa.
Ita ce ta kafa kuma babbar shugabar Conservation Through Public Health, wacce ƙungiya ce ba ta gwamnati ba da ke ɗaukaka bunƙasa kare halittu da tsirrai ta hanyar ba da dama ga jama'a da sauran namun daji su iya zama tare a duk lokacin da ake kyautata lafiyarsu da kuma mazauninsu.
Bayan shekara 30 ta taimaka wajen ƙara yawan goggon biri da ke tsaunuka daga guda ɗari uku zuwa wajen ɗari biyar wanda da ba'ayi wani abu ba da sun ƙare.
A shekarar 2021 wani shiri na kare muhalli na Majalisar Dinkin Duniya ya ambaci sunan Kalema-Zikusoka a matsayin gwarzuwar ƙasa (champion of the earth).
Abinda ya ƙarfafa min gwiwa a matsalar ta yanayi shi ne ƙaruwar sanin cewa ya kamata a hanzarta wajen magance matsalar. Akwai sabbin hanyoyi na rage wannan matsala.
Gladys Kalema-Zikusoka
Sonia Kastner, Amurka
Wacce ke samar da fasahar gano wutar daji
A wannan shelarar an yi fama da gobarar daji da suka addabi manyan wasu daga cikin manyan dazukan duniya. Inda `yan kwana-kwana sukan fama wajen kasha gobarar da hana ya\uwarta. Sonia Kastner ta samar da wata ƙungiya domin taimakawa wajen gano gobarar tun lokaci bai kai ga ƙurewa ba.
Pano AI na amfani da ƙirƙirarriyar fasahar bil`Adama wajen tsara kai ɗauki cikin hanzari kafin gobarar ta yaɗu ta hanyar ɗaukar hoton dajin don duba dukkan wata alama ta tashin wutar da ankarar da masu kawo ɗauki maimakon dogara da jama`a su kira masu ayyukan `yan kwana-kwana
Kastner a baya, ta kwashe fiye da shekara 10 tana aiki a ɓangarori na soma fasaha.
Abin da ke ƙarfafa mun gwiwa shi ne ƙoƙarin ƙirƙire-ƙirƙire na ɗan'dam. Na ga fasaha daban-daban da za ta taimaka wajen magance matsala mafi muni ta yanayi.
Sonia Kastner
Astrid Linder, Sweden
Farfesa ta kiyaye haɗuran ababen hawa
Shekaru da dama ana ƙera motoci ne ta amfani da ababen hawa na wasan yara da kuma maza matsayin ma su tuƙa su, duk da ƙididdiga ta nuna cewa mata ne suka fi jin rauni ko mutuwa idan an yi haɗarin mota na taho-mu-gama.
Injiniya Astrid Linder ta yi aiki domin sauya wannan da ta sanya a ka sauya tsari na farko a duniya da ake gwajin motocin da mata maimakon maza da ya yi la'akari da jikin mata a lokacin aukuwar haɗari.
Farfesa ta kiyaye haɗuran ababen hawa a cibiyar bincike ta sufuri ta ƙasa ta ƙasar Sweeden kuma mataimakiyar Farfesa a jami'ar Chalmers University, har ila yau Linder ƙwararriya ce ɓangaren jin rauni a titi da kuma kani-kanci.
Neha Mankani, Ƴar Pakistan
Ungozoma
A lokacin da wata matsananciyar ambaliya ta shafi Pakistan a shekarar da ta gabata, unguwar zomaNeha Mankani ta ziyarci yankunan da ambaliyar ya shafa domin taimakawa.
Ta hannun agajinta, Mama Baby Fund, Mankani da ayarinta sun samar da kayayyaki na taimakawa masu haihuwa da kuma kulawa ta unguwan zoma ga iyalai su fiye da 15,000 da ambaliyar ta shafa.
Ayyukan na ta suna maida hankali ga agaji na gaggawa da al'umomi da yanayi ya shafa da ire-irensu.
A yanzu asusun Mama Baby Fund ya tara isassun kudi domn baddamar da jirgin ruwa mai daukar majiyyata da zai dauki mata masu juna biyu da suke cikin al'umomi da ke gabar teku zuwa asibitoci mafi kusa domin bas u kulawa ta gaugawa.
Aikin ungozoma a al'umomin da ke fuskantar bala'o'I na muhalli na da muhimmanci sosai. Dukkanmu masu ba da agaji ne kuma 'yan gwagwarnayar sauyin yanayi da muke tabbatar da mata za su iya ci gaba da samun kula da suke bukata lokacin ɗauka da rainon ciki da kuma bayan haihuwa, ko da kuwa yanayin da suke ciki ba mai kyau ba ne.
Neha Mankani
Wanjira Mathai, Kenya
Mai ba da shawara ɓangaren Muhalli
Jagora ta ilahirin nahiya, Wanjira Mathai tana da ƙwarewa ta shekara fiye da ashirin tana gwagwarmayar kawo sauyi na zamantakewa da na yanayi.
Ita ta jagoranci gwagwarmayar Green Belt Movement, fitacciyar ƙungiya 'yar ƙasa ta yankunan karkara a kyanya da ke ƙarfafa mata ta hanyar dasa itatuwa, da mahaifiyar Wanjira kuma wacce ta sama lambar yabo ta zama lafiya ta Nobel Peace Prize a shekara 2004, Wangari Maathai.
A yanzu Mathai ita ce manajan darakta ta ƙawancen Africa and Global Partnerships a cibiyar albarkatu ta duniya, kuma shugabar gidauniyar Wangari Maathai.
A yanzu haka tana a matsayin mai ba da shawara ta afirka ga asusun Bezos Earth Fund, har ila yau da kuma ga ƙawancen Clean Cooking Alliance da uma gidauniyar European Climate Foundation dukansu da suka shafi kare muhalli da yanayi.
Ɗaukar mataki abu ne na gida. Muna buƙatar mu ba da goyon baya ga dukkan yunƙuri na gida kamar su kasuwanci da ya shafi dasa itatuwa da kuma ayyukan da al'umma ke yi wa jagora wajen ƙarewa, da sabunta makamashi da kuma bunƙasa tattalin arziƙi. irin wadannan yunƙuri, su suke ƙarfafa min gwiwa domin kuwa su suke nuna mana abinda zai iya yiwuwa.
Wanjira Mathai
Isabel Farías Meyer, Chile
Mai wayar da kai kan batun tsayawar jinin al'ada
Isabel Farías Meyer ba ta taɓa tunanin cewa yadda al'adarta take mata wasa da hankali wata alama ce da take nuna akwai matsala ba, amma lokacin da take gab da cika shekara 18 an gano cewa ta na da matsalar ɗaukewar haihuwa tun lokaci bai yi ba ko matsalar rashin wadatattun ƙwayoyin haihuwa. Wannan matsala ta kan auku ne a lokacin da kwayoyin wuraren haihuwa suka dena aiki kamar yadda ya kamata matsalar da ke shafar kusan kasha ɗaya cikin ɗari na mata 'yan ƙasa da shekara arba'in.
Mata sukan yi fama da irin waɗannan alamomi na waɗanda haihuwarsu ke tsayawa cikin hanzari, amma kuma a lokacin da suke ƙananan shekaru. Farias ta fito ta faɗi gaskiya a kan yadda yanayin ya shafi rayuwarta ciki har da rayuwa da matsala ta ɓargo da ke cikin ƙashi.
Yar shekara talatin ƴar jarida ta ƙaddamar da ƙungiya ta farko ta yanki ta batun ɗaukewar haihuwa tun lokaci bai yi ba a Latin Amurka domin raba bayanai da kuma mafita ga mutanen da suke fama da wannan lalura.
Natalie Psaila, Malta
Likita
Malta ta na da wasu daga cikin tsauraran dokoki akan zubar da ciki a turai, sannan Natalie Psaila ta na taimakawa mata da suke neman bayani da shawarwari.
Ta na ɗaya daga cikin wanda suka kafa Doctors for Choice Malta, kuma ta yi gwagwarmayar hana nuna bambanci da kuma halasta zubar da ciki da kuma inganta hanyoyin hana ɗaukar ciki.
Psaila ta ce hanin da akayi gaba ɗaya a Malta na an yarda a zubar da ciki ne kawai idan rayuwar mace na cikin haɗari, na nufin cewa mata na iya shan ƙwayoyin ba tare da kulawar likita ba ke nan. Ta samar da wata hanya ta taimako da ta ke taimaka wa mata kafin zubar da ciki da a lokacin zubar da ciki da bayan zubar da ciki.
Har ila yau ta wallafa wani littafi a kan ilimin jima'i don yara ƴan shekara 10 zuwa ƴan shekara 13 mai suna "My Body's Fantastic Journey" domin taimakawa ƙarin ilimi a kan lafiyar hayayyafa a ƙasar.
Olena Rozvadovska, Ukraine
Mai rajin kare haƙƙin yara.
Burin Olena Rozvadovska shi ne taimaka wa yara yaran Yukren ficewa daga cikin damuwar da yaƙin ƙasar ya haddasa musu. Tana cikin waɗanda suka kafa Voices of Children wato muryoyin yara. Wadda ƙungiya ce da take taimakawa wajen rage damuwa ta ƙwaƙwalwa.
Ƙungiyar ta soma ne a matsayin wani yunƙuri na matakin karkara a 2019, Shekara huɗu bayan Rozvadovska ya yi balantiya a kusa da fagen daga a Donbas a lokacin da ƴan aware da ke samun goyon bayan Rasga suka soma faɗa da Yukren.
Gidauniyar a yanzun tana da masu ilimin lamuran ƙwaƙwalwa su fiye da 100 da suke aiki a cibiyoyi 14 da kuma layin waya na gaugawa da za a iya kira kyauta. Ta taimaka wa dubban ɗaruruwan yara da iyaye.
Rozvadovska tana cikin labarin da aka zaɓa na Oscar-nominated documentary A House Made of Splinters, tare da ayarinta sun wallafa littafi mai suna War Through the Voices of Children, wato yaƙi ta muryoyin yara.
Rumaitha Al Busaidi, Oman
Mai Ilimin Kimiyya
Mata da yara 'yan mata kuna cikin hanyoyin magance matsalar yanayi shine taken mai ilmin kimiyya ta Omani scientist Rumaitha Al Busaidi ta tattaunawarta ta 2021, da ya sanya a ka samu ra'ayoyi fiye da miliyan ɗaya ya kuma nuna ta a matsayin gwarzuwar kare haƙƙoƙin mata larabawa.
Ƙwarewar Al Busaidi ya kaita ga matsayin nata a majalisar matasan larabawa a kan sauyin yanayida kuma ƙungiyar muhalli ta Oman.
Har ila yau ta baiwa gwamnatin Biden shawara a kan b da agaji na ƙasashen waje kan yanayi da kuma gwamnatin Greenland akan ɗorewar yawon buɗe idanu.
Ita ce mace mafi ƙarancin shekaru 'yar ƙasar oman da ta kai bangon duniya na South Pole kuma wacce ta ƙirƙiro da WomeX, wanda dandali ne na taimakawa mata larabawa su bunƙasa kasuwancinsu da kuma tallata }warewarsu.
Mataki na farko na shawo kan matsalar sauyin yanayi shi ne a ƙarfafa mata da yara mata. Tasirin da za su samu a al'umominsu daban-daban zai sauya tunanin da a ke dashi da kuma matakin da ake ɗauka da kuma kare wannan waje da muke kira gida.
Rumaitha Al Busaidi
Sumini, Indonesiya
Mai kula da dazuka
A lardin Aceh da ke Indonesiya na masu ra'ayin riƙau yana da wuyan gaske ga mata su zama shuwagabanni.
Da sumini ta gano cewa babbar abunda ke haddasa ambaliyar ruwa a yankin ta shine sassare itatuwa a daji, wanda har ila yau ke taimakawa wajen sauyin yanayi, sai ta yanke shawarar ɗaukar mataki da yin aiki tare da sauran mata da ke cikin al'umma.
Ƙungiyarta ta samu izini daga ma'aikatar muhalli da gandun daji na barin al'ummar Ƙauyen Damaran Baru su tafiyar da yankin, duka hecta 251 da ke dajin tsawon shekara 35.
A yanzu haka ita ce jagorar/shugabar sashen gudanar da dajin na Ƙauyen (LPHK), domin hana sare itatuwa ba bisa ƙa'ida ba, da kuma yadda 'yan farauta ke barazana ga manyan dabbobi da ƙanana da ke dajin.
Yadda a 'yan kwanakin nan sare itatuwa da farautar dabbobin daji da kashe su ya kamata dazuka su samu ƙarin kulawa idan aka yi batun yadda zamu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin magance matsalar yanayi. Kiyaye daji da kiyaye rayuwa.
Sumini
Fabiola Trejo, Mexico
Masaniyar abubuwan da suka shafi tunani da zamantakewa
A lokacin da masaniyar tunanin da zamantakewa, Fabiola Trejo ta soma karatu kusan shekaru 20 da suka gabata babu wani bincike a Mexico da ya mayar da hankali a kan jin dadin jima'i na mata a matsayin batu da ya kamata a yi adalci a kai.
Trejo ta buɗe fagen da aikinta wanda ya duba rashin daidaito na zamantakewa da cin zarafin mata da kuma siyasar iko a kan daɗin jima'i, da kuma neman a yi adalci a ɓangaren jima'i ga mata.
Ta yi bayanin cewa wasu daga cikin wannan rashin daidaito ne ya sa a ke cin zarafin wasu mata. Ta hanyar tattaunawa, da bincike na kimiyya da tarurruka na ƙara wa juna sani, ta taimaka wa jama'a gano jin daɗi ta hanyoyi daban-daban na saduwa, da kuma yadda za a shawo wannan matsalar.
Ayyukan nata sun yi fice a yankin Latin Amurka da kuma al'ummomi da suke magana da harshen Sifaniyanci, inda batutuwa da suka shafi lafiyar mata da kuma jima'i suka zama tamkar saɓo.
Jennifer Uchendu, Najeriya
Yar gwagwarmayar kawar da damuwa
Burin ƙungiyar, wadda matasa ke yi wa jagora SustyVibes, da Jennifer Uchendu ta kafa, shi ne ɗorewar daukar mataki da dangogin hakan.
Aikin Uchendu na 'yan kwanakinnan ya maida hankali a kan lalubo tasirin matsalar yanayi a lafiyar ƙwaƙwalwar 'yar afirka musamman matasa.
A 2022, ta kafa wata ƙungiya mai suna The Eco-Anxiety Africa project (TEAP) a taƙaice domin maida hankali a kan tantancewa da kuma kare damuwa a kan yanayi a 'yan afirka ta hanyar bincike da gwagwarmaya da ayyuka na wayar da kai a kan yanayi.
Burinta shi ne yin aiki da jama'a da ƙungiyoyi da ke da sha'awar sauya tunaninsu da yin aiki tuƙuru, aikin da a wasu lokuta ba shi da daɗI na koyon damuwar da jama'a suke da ita a kan yanayi.
Burinta shi ne yin aiki da jama'a da ƙungiyoyi da ke da sha'awar sauya tunaninsu da yin aiki tuƙuru, aikin da a wasu lokuta ba shi da daɗI na koyon damuwar da jama'a suke da ita a kan yanayi.
Jennifer Uchendu
Anamaría Font Villarroel, Venezuela
Mai ilmin sanin ƙarfin halittun duniya
Mai binciken ƙarfin halittun duniya, Prof Anamaría Font Villaroel ta mayar da hankali a kan fagen da ke ƙoƙarin bayyana dukkan abubuwa da kuma muhimman ƙarfi da ke cikin halittu ta hanyar tsara su a matsayin ƴan ƙananan abubuwa na makamashi.
Binciken Font ya zurfafa fahimtar abubuwan da fagen ya haifar idan aka yi maganar tsari na halittu da kuma nauyi ta har ila yau suke da muhimmanci wajen kwatanta baƙaƙen ramuka(black holes) da kuma yanayi na farko bayan samuwar duniya.
A kwanakin baya ne ta sama lambar yabo ta Fundación Polar a Venezuela sannan a wannan shekara a ka zaɓe ta a matsayin wadda ta sama lambar yabo ta mata da ke cikin kimiyya ta Unesco wato Unesco Women in Science award.
Qiyun Woo, Singapore
Mai rubuta labarai
A matsayinta na mai kare muhalli da gudanar da shirye shirye, Qiyun Woo ta yi amfani da soshiyal midiya wajen yaɗa ra'ayoyi game da sauyin yanayi.
Dandalinta na intanet, mai suna The Weird and the Wild, ta sadaukar da shi wajen ƙara samar da bayanan kimiyyar yanayi ga jama'a, da kuma rage kambama matsalar. Yana mayar da hankali a kan harkokin fafutuka da ilmantarwa da kuma shigar da al'ummomi cikin shirye-shiryen daukar daukar matakai kan sauyin yanayi.
Ta haɗa gwiwa wajen tsara abubuwa na muhalli a intanet a kan kudu maso gabashin Asiya da a ke kira Climate Cheesecake, da ke da manufar sauƙaƙa darussan yanayi ta yadda za'ayi sauƙin gane su.
Har ila yau matashiyar mai bincike ce ta ƙasa a ɓangaren duwatsu da yanayin ƙasa.
Matsalar yanayi aba ce mai wuyar gaske da tsoratarwa. Za mu iya tunkarar matsalar da ƙarfin tuwo da kuma ta dabara-maimakon tsoro- domin sanya zuciyarmu ta zama mai sanyi domin kula da duniya,a lokacin da muke wasa kayan aikinmu domin rusa abinda bay a aiki da gina abinda ke aiki.
Qiyun Woo
Elham Youssefian, Amurka/Iran
Mai bada shawara ɓangaren yanayi da nakasa
Lauya mai kare haƙƙin Bil'Adama wacce makauniya ce, Elham Youssefian 'yar gwagwarmaya ce ta neman a tafi tare da mutanen da suke da lalurar naƙasa a lokacin da ake duba matsalar sauyin yanayi, musamman batun ɗaukar matakin gaggawa a kan matsaloli na yanayi.
An haife ta kuma ta girma a iran, Youssefian ta yi ƙaura ne zuwa amurka a shekarar 2016. A yau ta taka muhimmiyar rawa a ƙungiyar International Disability Alliance, wadda ƙungiya ce ta ƙawance da take da ƙungiyoyi fiye da 1,100 da ke wakiltar utane masu naƙasa.
Burinta shi ne ilimantar da shuwagabanni a kan haƙƙokin da ke wuyansu idan aka yi batun tasirin da sauyin yanayi yake da shi a kan mutanen da suke da naƙasa. Har ila yau ta kasance kan gaba wajen nuna muhimmanci da ɗaiɗaikun jama'a suke da shi wajen yaƙi da matsalolin yanayi.
Mu a matsayinmu na ɗaiɗaikun jama'a masu lalurar nakasa, mun nuna ba sau ɗaya ba abubuwan da za mu iya yi domin fuskantar ƙalubale daban-daban da kuma lalubo hanyoyin magance su ko da kuwa babu wata hanya. Ya kamata mutanen da suke da lalurar nakasa su kasance kan gaba a yaƙin da ake yi da matsalolin da sauyin yanayi yake haifarwa.
Elham Youssefian
Mene ne Mata 100?
BBC 100/ Mata 100 na BBC yakan faɗi sunayen fitattun mata guda 100 da ke faɗin duniya a kowace shekara. Mukan ƙirƙiro bayanai, hotuna da kuma tattaunawa game da rayuwarsu- labaru da kan mayar da hankali a kan mata kuma ake wallafa su da watsa su a dukkan dandali na BBC.
Bibiyi BBC 100 Women a Instagram da Fesbuk. Shiga cikin tattaunawar ta #BBC100Women.
Ta yaya ake zaɓo matan 100?
Ayarin BBC 100 Women yak an tsara sunayen da a ka zaɓa ta aiki da sunayen da suka tara ta hanyar bincike da kuma wa]anda ayarin sashen harsuna na sashen BBC suka ba da shawara da kuma BBC Media Action.
Muna neman mata da suka yi fice a muhimman labarurruka a watanni 12 da suka gabata, da kuma wanda suke da labara mai ɗaukar hankali da za su faɗa, ko suka cimma wata muhimmiyar nasara ko sukayi tasiri a kan al'umominsu a hanyoyin da be zama dole ya zama labari ba.
A wannan shekarar ma an tantance sunaye masu yawan gaske a game da taken bana – Sauyin yanayi da tasirinsa a kan mata da yara ƴan mata da ke faɗin duniya, daga nan ne aka zaɓo ƙungiyoyi 28 da ke kan gaba a batun yanayi, da kuma zaɓo wasu shugabanni ɓangaren muhalli.
Mun wakilci muryoyi daga ɓangarorin siyasa da kuma daga dukkan ɓangarori na al'umma, muka lalubo sunaye da suka jiɓanci batutuwa da suka banbanta ra'ayi, da kuma zaɓo mata da suka ƙirƙiro nasu sauyin.
Har ila yau an ɗora jerin sunayen a sikelin wakiltar yanki da kauce wa son kai kafin a zaɓi sunaye na ƙarshe, duka matan sun ba da amincewarsu ta kasancewa su zama a cikin jerin sunayen.
Godiya
BBC 100 Women Production Team: / Ayarin Samar da "100 Women" na BBC Valeria Perasso, Amelia Butterly, Paula Adamo Idoeta, Rebecca Thorn, Cordelia Hemming, Laura García, Sarah Dias, Lucy Gilder, Mai Kanaaneh, Mark Shea, Vandana Vijay, Kindah Shair, Daria Taradai, Lamees Altalebi, Firouzeh Akbarian, Sana Safi, Kateryna Khinkulova, Tamara Gil da Mouna Ba
Editan Mata 100 na BBC: Golnoosh Golshani.
Masu shirya wa sashen ƙasashen duniya na BBC: Roberto Belo-Rovella da Carla Rosch.
Tsarawa: Prina Shah, Jenny Law, Matt Thomas, Pauline Wilson da Oli Powell.
Hadawa: Scott Jarvis, Arun Bhari, Alexander Ivanov, Preeti Vaghela da Holly Frampton.
Hakkin mallakar hoto: Miller Mobley, Maciek Tomiczek/Oxford Atelier, Arati Kumar-Rao, Hamna Haqqi, Craig Kolesky, Pano AI, L. Reid, Benjamin Jones, Yober Arias, Amanda Triplett, Anny Roberts, Diyor Abdughaforzoda, Doi Inthanon Thailand by UTMB, Qinghai Snowland Greatrivers Environmental Protection Association, Jason Boberg, Chaideer Mahyuddin/AFP, New Balance Paraguay, Jo Anne McArthur, The Cartier Women's Initiative (CWI), Lucy Piper, Louise Mabulo, Christian Tasso, Martin Chang, Konstantin Deryagin, Gabriel Quintão, Abel Canizales, Patrick Wally, Sarah Hale, Jimena Mateot, Lucas Christiansen, Hana Walker-Brown, Woody Morris, Xinyan Yu, Chris Parker Edzordzi Sefogaht, Taseer Beyg, Albert Kamanga Zeeya Creations, Salem Solomon, Luke Nugent, R. David Marks, Lee Tinklim, Satu/VTI, FIFA, Josh Finche, Kibuuka Mukisa, Phoebe Xu, Gregory Vepryk, Darko Tomas CROPIX, Wanjira Mathai, Rufat Ergeshov, Osvaldo Fanton, Dani Pujalte, Giuliano Salvatore, Fondation L'Oreal, Daniel Eduardo, Tatyana Egorova, Dovana Films, Jimmy Day/MIT, Editorial Caminho - Leya, Khine Hnin Wai Foundation, Andrew Sikorsky, Ramón Tolosa Calderón, Mariam Siddiqi, Feral Films, Sebastián Aliaga, Diyor Abdughaforzoda, The White Helmets/Syria Civil Defence, Ellie Varley, DGL Nunnery, Mustafa Abumenes, Emanuele Elo Usai, Fazal Raham Arman, Emilia Trejo, Mattia Zoppellaro, Martin Lupton/Light Collective, Yasmina Benslimane, Pavlo Botanov, Marijeta Mojasevic, LenadraPella/International Federation of Sport Climbing, Gal Mosenson, Getty Images.
Kuma Jagorar Jigilar Magana ta Kimiya ta 450 Jigilar Tsarin Masalar tattalin arziki Tsarin Kayayyakin Harshe Suna Taimaka mana Indianarfin Indiya na Caparfin Indianarfin Indiya. Izini kamar siye ne, ba tare da bincike ba. Ushki da alama yana yin fassarar fassarar jagorar fassara na yanzu Amitkumar Sunat zai iya zaɓar koyarwar ɗan adam
Nullification kusan an gama yin sa, amma ana iya samar da bayanan mai amfani. Amma ingantaccen cikakkiyar tattaunawar ba za a iya rushewa ba, amma ana iya inganta umarnin. Na farko shi ne kiyaye duniya a zaman al'umma. Yaren shine yaren al'umma.